Har suka isa be ce mata komai ba ita ba ce masa ba. Haka yake a duk lokacin da suka hadu sai ya rasa abunda zai ce mata, na daya dai yana ganinta yarinya kuma yana ganin kamar akwai kurciya a cikinta sosai wanda be dace ya fara firan soyayyah da ita ba, na biyu kuma baya jin yana mata son da ya wuce na gida daya wanda kusan sun zama yan'uwan juna. Ya rasa yadda zai yi Hajiya ta fahimce shi ya rasa da wane baki zai mata magana ta fahimci yarensa, idan ma bata son Mansura zai iya hakura da ita ya auri wata amman why Nana? Why? Har yanzu ya rasa dalilin Hajiya na son ya auri Nana.
Yana fakin ya bude inda yake ajiyar kudi a mota ta dauko 5k ya mika mata, sai ta bude motar da sauri ta fita.
“Ka jira ni a nan”
Shi dai kallonta kawai yai, daman can ya dade da ayyanawa a ransa Nana bata da hankali kamar sauran mutane wata kila kuma gata ne yai mata yawa. Jinginar da kansa yai jikin kujerar motar ya ciro wayarsa ya kamo hoton Mansura yana kallo.
Murmushi yai yana yinta sosai musamman idan ya tuna irin yadda suke mu'alama da kuma yadda take son shige masa jiki, yadda take yabon daukakarsa da kyausa, gashi ta iya drees tana son duk wani abu da yake so, tana gudun bacin ransa, idan wani abun ya same shi hankalinta zai tashi sosai, duk inda yake tana nan manne da shi, wannan dalilin yasa mutane da yawa suka san alakarsu, kasancewar fitattacen mawaki kuma mai tashe duk wani motsi nasa yan media da yan jaridu sun saka masa ido.Cikin jindadi Nana ta shiga cikin restaurant din, kai tsaye ta wuce reception sai rabon ido take ko zata ga AA. Tsaye tai tana a gurin ta rasa abun da zata ce.
“Hajiya me kike so?”
“Wannan yaron nake nema, wani yaro fari dogo ba sosai ba be da jiki ana mishi lakani da Sardauna”
“Okay kwana biyu be zo ba, ya samu hadari ne ”
Ta dan yi shiru kamin ta sake kallon mai bata amsar ta ce.
“Dan Allah kana da number shi ka kira shi?”
“Okay”
“Yauwa Thank You”
A take ya ciro wayarsa yai dialing number AA ba da wani dade tana ringing ba yai picking.
“Hello Jafar”
“Sardauna wata yarinya ce ta zo nemanka yanzu”
Saurdauna ya tsaya daga tafiyar da yake yana mamaki gabansa kuma na mugun faduwa.
“Wata yarinya? Wacece?”
Jafar ya mika mata wayar.
“Hello”
Yana jin muryarta ya gane ta.
“Nana”
“Na'am na zo baka nan, kana ina ne?”
“Miyasa kika tambaya? Kama ni za ayi?”
“A a ba abunda za a maka, kawai na zo na ji ya jikinka ne, kuma na kawo maka kudi”
“Kudi....”
Dan murmushi yai sai yaji wani karfi da kuzari suna ratsarsa, sai dai tunawa da wani abu yasa tsoro ya kama shi, what if plan ne?
“Nana bana kusa na je Kano, amman idan da gaske kike ki bawa Jafar kudin ya saka min a account”
“To amman yaushe zaka dawo?”
“Sai next week”
“To zan karbi number ka na kira ka da wayar Hajiya Karama ko wata”
“A a ban yarda ba”
Ji yake kamar zata yi amfanin da number na sa ne a gano shi.
“To ka dawo da wuri ka ji”
“To”
YOU ARE READING
FULANI
FanfictionFULANI -The story of unwanted girl, she always had a strong sense of destiny...! The story of a Prince and his kingdom. witchcraft, distorted relationships, hidden secrets, selfishness.