Part 4

46 3 0
                                    

*TSANTSAR YAUDARA😭💔*

*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏾*

*Sadaukarwa ga habibaties👯🏽‍♂️💃🏼*

*Share it fisabilillahi🙏🏽💥😫*

*Shafi na 4*

*KHAUSAR😫*

Khausar gaba d'aya ta rikice,wani irin zazzab'i ne mai zafi tare da matsanancin ciwon kai ne ya sakata a gaba, hankalin Rahma ya gama tashi duk ta rame, gashi mahaifinsu baya gari kusan wata d'aya kenan da akayi masa transfer zuwa Kaduna ya koma chan da aiki, wata muguwar tsanar Fad'ima da Abdulrahman ne ta mamaye mata zuciyata ko sunansu bata so ta ji an ambata, kullum tsanarsu k'aruwa take a cikin zuciyarta, Zaune suke a kan gadon d'akin Khausar, a hankali Khausar ta d'ago ta k'urawa Rahma ido wacce take yanke farcenta, tana kallonta wani irin so da k'auna had'ida tausayin 'yar uwarta ta ne ya cika mata zuciya "Sister mie" D'agowa Rahma tayi tare da cewa "Na'am" Tayi maganar tana sakar mata wani irin lallausan murmushi "Nagode da kulawa, tabbas ke d'in uwa ce a gurin na ba wai matsayinki a 'yar uwata kad'ai ya tsaya ba, kina da matuk'ar muhimmanci a wajena kina d'aukar damuwata a matsayin taki, na yarda da maganar hausawa da suka ce babbar ya uwa" Murmushi Rahma tayi wanda ya k'ara fito da asalin kyanta "Darling sister ai wannan hakkina ne na kula dake fiye da yadda zan kula da kaina, dan haka ba sai kin yi min godiya ba, ni dai burina ki manta da abin da wad'annan dabbobin sukayi miki" Khausar cikin sanyin murya ta ce "Insha Allahu sister mie zan yi kok'arin mantawa da komai","Yawwah dear na ji dad'i sosai wallahi Love you more" Khausar ta ce "Me too dear" Tayi maganar cikin jin dad'i haka suka cigaba da yin hirarsu ta rayuwa wani abun suyi dariya wani kuma su jimamanta abun.

*ABDULRAHMAN😨😂*

Kwanan Abdulrahman uku gaba d'aya hankalinsa ya gama tashi, zuciyarsa jinta yake kamar zata tarwatse zafi da turirin da takeyi masa kuwa kullum k'ara dad'uwa yake, Abdulfatah ne ya shigo d'akin Abdulrahman hangosa ya yi a kan makeken gadon d'akin yana da juyi yana dafe da k'irjinsa, da sauri ya k'arasa kusa dashi ya zauna tare da rik'eshi cikin rawar murya ya ce "Brother meya sameka, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Brother dan Allah ka tashi zan kira Abba a waya wallahi za'a d'aura auren a week d'in nan" Abdulrahman ya ce "A'a Abdulfatah, Abba ba zai tab'a yarda a d'aura auren nan ba, ba ka ga da Daddyn Fad'ima ya kirashi a waya me ya ce ba?? Cewa fa ya yi babu wanda ya isa ya saka shi ya janyen abun da ya ce ba, idan kuma aka matsa masa zai sa a fasa auren gaba d'aya" Ya k'arasa maganar yana kukan takaici zuciyarsa na cigaba da bugu kamar ganga, Abdulfatah ya dafe kai tare da cewa "Ka kwantar da hankalinka bro, komai zai yi dai-dai zan tabbatar da cewa burinka na auren Fad'ima ya cika" Abdulrahman ya yi murmushin yak'e tare da cewa "Karka ba wa kanka wahala bro, Abba baya son auren nan dan haka kawai ka bari nagode da kulawa d'an uwana" Abdulfatah ya ce "Abba yana da sauk'in kai sosai kaima kasan da hakan, amman wannan karan ban san meyasa ba yake kafiya kuma yak'i fad'awa kowa dalilin da yasa ya ce ya d'aga d'aurin auren" Abdurrahman ya ce "Na fad'a muku bashi da wani dalili kawai son ransa ne, saboda baya son ya ganni ina farin ciki" Ya yi maganar cikin sark'ewar murya, Abdulfatah ne ya matsa sosai kusa dashi tare da cewa "Bro tashi ka zauna, ina son yin magana da kai" Ba tare da ya ce komai ba, ya shiga kok'arin mik'ewa zaune, tare da taimakon Abdulfatah ya zauna yana kallon Abdulfatah d'in ya ce "Ina sauraronka, wace magana ka ke so muyi?" Abdulfatah ya ce "A kan Khausar" Abdulrahman ya yi saurin kallonsa zuciyarsa sai da tayi wani irin bugu da ya ji Abdulfatah d'in ya fad'i sunan Khausar, wasu zafafan hawaye ne ya shiga zubo masa ya ce "Meya faru da Khausar d'in?" Abdulfatah ya ce "Babu komai kawai dai ina ji a jikina kamar abin da ku ka yi mata ne Allah ya fara nuna muku ikonsa, kai kanka bro kasan kun ci amanar Khausar tayi matuk'ar yarda da ku, ku ka yi mata tsantsar yaudara" Abdulrahman ya sauke ajiyar zuciya "Abdulfatah ya kamata ka gane cewa Allah ya riga da ya k'addara ban dace da Khausar ba, Fad'ima ita ce dai-dai dani suna da kud'i muma haka, ita kuma Khausar 'yar talakawa ce sam bai kamata ace ta zama matata ba, kuma da ka ke cewa munyi mata tsantsar yaudara to hanata jin dad'i ku ka yi?? Ko kuma turawa mukayi a kasheta??? Ko kuma cewa mukayi kada wanda ya aureta?? Ni dai a tunanina wad'annan abubuwan dana lissafo shine idan akayi wa mutum za'a ce anyi masa tsantsar yaudara, nasan cewa bamu kyauta mata ba amman ni ban yaudareta ba" Ya k'arasa maganar cikin nuna ko a jikinshi yana tab'e bakinsa, Abdulfatah da yake yasan halin d'an uwan nasa da rashin son ace ya yi laifi bai k'ara cewa komai ba ya ja bakinsa ya yi shuru, amman a cikin zuciyarsa yana tsananin ganin laifin Abdulrahman dan duk wanda ya ji labarin abun da sukayi mata tabbas zai san sun yaudareta, sun cuceta, sun zalinceta kuma sun ci amanarta matuk'a ainun, Mik'ewa ya yi tare da yiwa Abdulrahman sallama ya fita zuwa d'akinsa, shi kuma Abdulrahman binsa da kallo ya yi har ya fita ya yatsine fuska tare da zamewa ya kwanta, yana jan tsaki.

*FAD'IMA🤔😨*

"Wallahi Mummy na tsani Abban habibina saboda ya rabani da farin cikina, wallahi Mummy ni nasan mutuwa zan yi ba zan iya jurewa ace har sai nan da wata biyu sannan zan auri Abdulrahman ba, dan Allah Mummy ku k'ara komawa gidan mu rok'esu dan a dawo da d'aurin auren gobe" Fad'ima ce durk'ushe a gaban mahaifiyarta tana kuka, Hajiya Laure ta sauke nannauyan ajiyar zuciya dan ita ma gaba d'aya wata iriyar muguwar tsanar Alhaji Saleh take ji, dan a cewarta saboda mugun halinsa ne yasa 'yarta take neman fita daga cikin hayyacinta gaba d'aya ta rasa nutsuwarta, "Auta ki daina wannan kukan haka dan Allah, zuciyata ba za ta juri ganinki cikin wannan yanayin ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ni kai na na tsanin Alhaji Saleh fiye da tunaninki kuma nasan kawai mugunta ce yasa ya hana a d'aura aurenki da d'ansa kuma insha Allahu zan san abun yi dan ya yi kad'an wallahi" Fad'ima ta d'ago kanta tana cewa "Mummyna kin tabbatar zaki cika min burina" Hajiya Laure ta ce "Tabbas wannan haka yake daughter, zan cika miki burinki nan ba dad'ewa ba" Murmushin k'arfin hali Fad'ima tayi tare da kwantawa a jikin Mummyn na ta, "Ai baku fara ganin tashin hankali ba, tunda ku babu abin da ku ka iya sai yaudara da cin amana, Hajiya Laure keda wannan mayaudariyar 'yar ta ki ai yanzu ku ka fara ganin ruwan k'uri'un bala'in masifa da bala'i" Gaba d'ayansu suka juya cike da tashin hankali had'i da mamakin wanda ya yi maganar.....................................😉

*Kuyi min sharing dan Allah, Ya Allah duk wanda ya karanta labarin nan ya yi min sharing kuma ya yi comments Allah ka haskaka kabarinsa kayi masa tsararran gidan a aljanna🙏🏽🤲🏽ka cika masa dukanin burinsa na duniya da lahira🥰*

*Please🙏🏽👏🏽👏🏽*

*Share👏🏽👏🏽*
*Comments mai fasa waya🙏🏽*

*MRS BREAKER💥❤️*

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now