*TSANTSAR YAUDARA😭💔*
'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏽
08122188717*Sadaukarwa ga habibaties💃🏼*
Shafi na 7
"Kai Sister mie har kinsa na ji kunya, bari na je na sameshi kafin sweetynki kema ya zo" Rahma tayi wani yalwatatcen murmushi "Ai kuwa dan yana hanya ina tunanin dan na ga yamma tayi na san ba lallai ya zo da daddare ba" Khausar ta ce "Hakane kam, na tafi sister mie ki kula da kanki" Rahma ta ce "To luvly sister" Tayi maganar tana zaunawa a kan wata kujerar tsugunno da ke kusa da d'akinta tana kallon mudubi, Khausar kuwa ta fita wajen Alhaji Saleh tana takunta d'ay-d'ay, Tun fitowarta ya kafeta da idanuwa yana kallonta fuskarsa d'auke da murmushi mai bayyanar da tsantsar farin cikin da yake ciki, tana k'arasowa kusa dashi ta sakar masa wani irin shu'umin murmushi tare da cewa "Barka da yamma Alhaji" Murmushin kan fuskarsa ya k'ara fad'ad'a "Barkanki dai gimbiyar mata, da fatan kina lafiya??" Khausar wacce ta kafeshi da ido tana yi masa wani irin kallo mai gigita mutane ta ce "Lafiya alhamdulillahi da fatan kai ma haka?","Nima haka nake gimbiyata" Khausar ta ce "Mu shiga daga ciki mana, na ga rana dana haskoka, kuma na san da zafi sosai" Alhaji Saleh ya ce "Duk yadda ki ka ce haka za'ayi, nagode sosai da kulawarki" Khausar ta d'an yi masa wani kallo irin bata ji dad'in maganar da ya fad'a ba ta ce "menene abin godiya kuma?? Ai yi wa kai ne babu godiya a tsakaninmu ka ji" Alhaji Saleh ya ce "tuba nake masoyiyata" Khausar ta saki wata dariya mara sauti sannan tayi gaba Alhaji Saleh yana biye da ita a baya, wani d'an k'aramin d'aki suka shiga, babu komai a d'akin sai babbar taburma da ke shimfid'e a k'asa, Khausar ta d'auko wata dadduma ta shimfid'a a kan taburmar sannan ta ce "Bismillahi Alhaji ko zaka iya zama a d'an akurkin na mu" Alhaji Saleh ya zauna yana cewa "Wannan ne akurki??? Dan Allah masoyiyata karki k'ara kiran wannan gidan da akurki dan sam bai ma yi kama dashi ba, shin san ma menene akurki kuwa???to idan baki sani ba yau ki sani akurki shine gurin da ake saka kaji" Ya yi maganar cikin yanayin b'acin rai, Khausar ta zauna tare da had'e hannuwanta waje d'aya alamar tana neman afuwa ta ce "Ayi min hak'uri nayi laifi ba zan sake ba amman insha Allahu daga yau ka ji masoyina" Ta yi maganar tana murmushi, shima murmushin ya yi mata ya ce "To ko ke fa" Khausar ta ce "Da fatan ka zo lafiya ya gida ya yarana" Alhaji Saleh ya ce "Lafiya lau na zo, yaranki kuma suna nan zasu zo gaisar da Mummynsu" Khausar ta ce "Ina maraba dasu a duk lokacin da suka zo","Khausar tun ranar da nazo gurinki neman soyayyarki ban iya bacci ba, saboda tsorona d'aya kada na zo ki ce ba za ki iya aurena ba" Alhaji Saleh ya yi maganar cike da damuwa, Khausar tayi wata 'yar dariya tare da cewa "me zai sa na k'i amincewa da soyayyarka?? To yau ina so ka je ka kwanta ka sha baccinka har da munshari dan Khausar kam ta ka ce kai kad'e, babu mai kwace maka ita ka ji ko" Alhaji Saleh ya yi wata dariyar jin dad'i yana cewa "Ai kuwa na ji dad'in wannan maganar taki tabbas yau akwai bacci mai dad'i" Khausar ta ce "Yauwa masoyina haka nake son ji" Daga nan suka cigaba da hirarsu ta masoya, sai wajen k'arfe 6:00pm na yamma Alhaji Saleh ya tafi gidansa zuciyarsa fal murna, ita ma Khausar ta shiga gidan tana jin wata sabuwar kwarin guiwar d'aukar fansar abin da Abdurrahman da Fad'ima sukayi mata, tana shiga ta tarar da Rahma ta cire kayan jikinta tana tuk'a tuwo, da sauri ta k'arasa wajenta tana cewa "Sister mie Alhaji Lawal bai zo ba ne???" Rahma ta kalleta tana murmushi "Ya zo mana mun sha soyayyarmu kamar zamu cinye juna" Dariya Khausar ta tsintsire da ita tana cewa "Gaskiya hakan ya yi kyau na ji dad'i kuma" Rahma ta ce "Ya ce ma zai dawo gobe, yanzu ma kin ga dashi muka gama waya yake ce min har ya isa gida" Khausar ta ce "Ahhhh gaskiya abu ya yi sweet sosai Allah ya k'ara dankon Love, nima yanzu sahibina ya tafi amman shi ba zai dawo gobe ba saboda yana da meeting d'in da zai je a Abuja zuwa jibi zai dawo" Rahma ta ce "Allah sarki! Allah ya dawo dashi lafiya" Khausar ta ce "Amin ya Allah" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu har Rahma ta gama yin tuwo Khausar ta taimaka mata suka kwasheshi suka d'ora ruwan miya sannan suka shiga d'akin Rahma suka yin hirarsu abin gwanin ban sha'awa.
_Habibaties yau ban da lafiya😭zazzab'i nake ku yi mim addu'a wallahi dakyar nake iya yin typing😭😭_
*HAJIYA LAURE😅*
"Alhaji ban tab'a tunanin haka halinka yake ba sai yau, ashe kai azzalumi ne ban sani ba??? To wallahi ba zai sab'u ba yadda ka ke nunawa Fad'ima soyayya daaa yanzu ma dole ka cigaba da nuna mata saboda ko yau ka fad'i ka mutu ita ce magajiyarka" Dariya Alhaji Lawal ya yi sosai yana cewa "Laure ban tab'a tunanin ke dabba ba ce sai yau, Alhamdulillahi gwanda da Allah ubangiji yasa yau kika fito fili ki ka nuna min asalin halinki wato so kike na mutu ki ci gado ko??? To wallahi daga ke har 'yar ta ki babu wanda ya isa ya sani abin da ban yi niyya ba mayaudarar banza mayaudaran wofi kawai, kuma ina so ki shirya karb'ar wannan yarinyar dai da 'yarki ta yaudara a matsayin kishiyarki" Daga Hajiya Laure har Fad'ima da ke kwance kan kujera zabura sukayi jikinsu na rawa suka mik'e, Fad'ima bakinta na rawa ta ce "Abbah kar dai ka ce min Khausar zaka aura??" Wani irin kallon banza ya yi mata tare da cewa "Tabbas ita ce zan aura nan da watanni biyu masu zuwa" Hajiya Laure ta nufeshi gadan-gadan tare da cukumeshi tana cewa "Wallahi baka isa ba, ka yi kad'an da kayi min kishiya, idan kuma ka dage sai ka aurota to tabbas ka shiga karb'ar gawarta dan a ranar da ta zo zan kasheta wannan alk'awarina ne wallahi" Alhaji Lawal ya daddage ya d'auketa da wani mahaukacin mari tare da fisge cukumar da tayi masa "Laure idan baki fasa kashe Khausar ba, kada Allah ya baki abin da ki ke so duniya da lahira banza shashasha kuma aure ne babu fashi dole sai na aureta, sai dai ki mutu" Yana gama fad'ar haka ya fita waje da sauri motarsa ya shiga ya ja ta da gudu ranshi gaba d'aya a b'ace yake ya nufi gidansu Khausar, Hajiya Laure kuwa durkushewa tayi a k'asa tare da dora hannuwanta a kai tana cewa "Na shiga uku ni Lauratu na mutu na lallace, yanzu da raina za'ayi min kishiya" Fad'ima ta rumgumeta ta baya tana wani irin kuka mai cin rai, dan ta san a duniya babu abin da Mummynta ta tsana irin kishiya, "Mummy ki yi hak'uri dan Allah na san ni na ja miki wannan matsalar Khausar ta ci amanata me yasa zata auri Abbana??? Wato saboda ta rama abin da nayi mata, to wallahi bata isa ba idan ta sake tayi gangancin shigowa gidan nan a matsayin matar Abbana wallahi ko ni ko ita dan sai na kasheta, wallahi sai na kasheta" Ta k'arasa maganar tana kuka, haka suka zauna suka kuka kamar gidan makoki, Alhaji Lawal kuwa yana isa gidansu Khausar, ya kira Rahma a waya ya ce mata yana kofar gida, da yake Rahma ta san da zuwan nasa ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa tayi kyau sosai, ta fito kofar gidan tana tafiya kamar ba za ta taka k'asa ba, kallo d'aya tayi masa ta gano cewa yana d'auke da tarin b'acin rai "Sweetheart me ya faru na ga yanayinka yau babu dad'i????"
*Manage😭 ban da lafiya ne yau wallahi😔*
*Share ita fisabilillahi👏🏽👏🏽👏🏽*
*MRS BREAKER💞*
YOU ARE READING
TSANTSAR YAUDARA
RomanceBazan iya fada muku irin cakwakiyoyin da ke cikin littafin nan ba ku dai kawai ku biyoni 'yar mutan zazzau don jin yadda labarin yake