*TSANTSAR YAUDARA😭💔*
*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏽*
08122188717*Sadaukarwa ga habibaties💃🏼*
_Habibaties ina me sanar da ku cewa jiya na fara littafin kud'i mai suna SO SHU'UMI💃🏼akan kud'i naira 300 daga jin sunan littafin kun san akwai cakwakiyoyi a cikinsa, yau zan gama free page dan haka kada ku bari a baku labari✨_
*Shafi na 8*
Alhaji Lawal ya yi murmushin yak'e tare da cewa "Bakomai ya kike?? Da fatan dai kina lafiya??" Rahma ta d'an yatsine fuska tare da cewa "A'a ni ba na lafiya kuma ba zan tab'a lafiya ba tunda har za ka iya b'oye min damuwarka" Alhaji Lawal ya saki wani murmushin jin dad'i tare da cewa "Gimbiyata kenan, nagode sosai da irin kular da kike ba ni, kuma ni ba b'oye miki komai nake ba, kin san dai idan aka ce yau mutum yana da iyali ya fad'a mata zai k'ara aure musamman ma idan ta san matar to zai ta had'uwa da b'acin rai kala-kala" Rahma tayi wani k'ayatatcen murmushi a zuciyarta tana cewa "Alhamdulillahi anzo wajen, dai-dai inda nake son azo Hajiya Laure yanzu wasan ya fara" Amman a fili ta ce "Allah sarki habibina kayi hak'uri insha Allahu komai zai huce" Alhaji Lawal ya ce "Allah yasa" Rahma ta amsa da "Amin" Suka cigaba da hirar soyayyarsu kamar kullum.
Sai wajen k'arfe 7pm na dare ya tafi kowannansu cike da kewar d'an uwansa.
Rahma tana shiga gida ta fad'awa Khausar abin da Alhaji Lawal ya fad'a mata, wani irin ihu Khausar tayi tare da buga tsalle tana cewa "Allah mun gode maka yanzu wasan zai fara" Sai kuma Khausar ta kalli Rahma tana cewa "Amman sister mie akwai matsala guda d'aya fa da nake hango mana ita" Rahama ta kalleta sannan ta ce "Allah ya rabamu da matsala wallahi ni sam ba na hango matsalar komai, domin duk wata kofa da nasan zata kawo mana matsala sai da na bi na tosheta" Khausar ta ce "baki toshe kofar da idan Fad'ima ta gayawa Abdurrahman cewar Abbanta zai auri Khausar shima daga baya idan ya san cewar Abbansa zai auri Khausar ya kike ganin abun zai kaya, tabbas hakan zai iya lallata mana shirinmu" Rahma ta tintsire da dariya tare da cewa "Wannan kofar ita na toshewa" Khausar ta saki baki cike da mamaki ta ce "ban ga ne ba?" Rahma ta ce "Na fad'awa Alhaji Lawal cewa ni sunana Rahma na gaskiya amman ana ce min Khausar, kuma ina da k'anwa ita ma sunanta Khausar kuma"...... Irin yadda Khausar ta saki ihu tare da rumgume Rahma ne yasa tayi shuru tana dariya, Khausat ta ce "Wallahi Auntyna kin cinye wasan, ko baki k'arasa ba ki ka tsaya anan ma ya yi" Rahma ta dan zame jikinta tana cewa "To Dan Allah ki bar ni haka sister mie, jibi Baba zai dawo saboda Alhaji Lawal Yana so ya Aiko ayi maganar aurenmu, Kuma kema na ji kamar Kaka jiya da na je wajenta tana cewa kema jibin Alhaji Saleh zai Aiko ko?" Khausar ta ce "Nima dai a wajen Kaka na ji, kin san har yau bai dawo daga Abuja ba shiyasa ban ji kan Zancen ba, sai waya ku ke dashi Kuma kin san ba zai yi yu na tambayeshi akan maganar aurenmu" Rahama ta ce "Gaskiya kam" Rahma ta shiga d'akinta dan ta gyara shi Khausar kuma ta d'auki wayarta ta Kira Alhaji Saleh suka Sha soyayyarsu daga k'arshe kowannansu ya kashe wayar.
*WASHE GARI💥*
"Ke Khausar dan ubanki kina ina ki fito nan wallahi idan ki ka bari muka had'u da ke tabbas sai na kashe ki, kina ina 'yar gidan talakawa" Fad'ima ce ta shigo gidansu Khausar ko sallama babu, fuskarta a d'aure hannunta rik'e da wata zabgegiyar wuk'a.
A tare Rahma da Khausar suka fito daga d'akunansu suna yi wa Fad'ima wani irin kallon mara hankali, Khausar ta bud'e baki za ta yi magana Rahma ta rigata da cewa "Ke dabba meya kawo ki gidanmu?? Ki yi gaggawar fita idan ba haka ba tabbas zan cire miki d'an 'karamin haukan da yake damunki, Dan ni d'in nan da ki ke ganina ba k'aramar tantariyar mara mutunci ba ce" Fad'ima ta ce "Ke Kuma wacece?? Rahma ki ke ko wa, to ki mai da hankalinki jikinki idan ba haka ba, wannan tsohon zai dawo ya tarar da gawa biyu Kuma"....... Wani irin mahaukacin mari Rahma ta wanketa da shi hagu da dama, sai da ta fad'i k'asa wuk'ar hannunta tayi wani irin tsalle ta sauka a gaban Khausar, Rahma cikin zafin nama ta fara magana da cewa "Ke 'karamar dabba ce, wallahi ina me tabbatar miki da cewa idan ki ka sake ki ka yi yunk'uri tab'a Khausar to yau sai na cire miki k'afa, shashasha dabba kawai" Khausar ta ce "Sister mie barta ta ma zo ta ce zata tab'a ni, wallahi sai mun saka Ubanki ya yi wa wannan dabbar uwarta ki saki uku, Khausar d'in yanzu daban take da ta daa ina fad'a miki da babbar murya ki fita daga shirgina"
Fad'ima ta tashi dakyar tana kallonsu zuciyarta fal bak'in ciki ta ce "Ke Wai a kan na ce ina son Abdurrahman shine ki ka yanke shawarar wato Bari ki auri Abbana, to Khausar bari ki ji nayi miki Alk'awarin guda d'aya Ni Fad'ima Lawal Abdulkarim Mata a gurin Abdurrahman ba zan tab'a barinki ki auri Abbana ba" Wata iriyar dariya Khausar tayi ta ce "Ni Kuma Khausar Muhd Lawal nayi Alk'awarin sai na tarwatsa burinkanki gaba d'aya sai na kuntata muku ke da mahaifiyarki, Kuma aure ne babu fashi mu zuba mu gani" Rahma ta finciki Fad'ima tayi hanyar waje da ita, suna zuwa kofar gida Rahma ta wurgar da ita, ta fad'i tare da buguwa da wani k'aton dutse, Rahma ta kulle kofar gidan sannan ta koma cikin gidan.
Fad'ima kuwa ganin babu me zuwa ya taimaketa yasa ta mik'e jiri na dibanta kanta yana fitar da jini
Mrs breaker ce
YOU ARE READING
TSANTSAR YAUDARA
RomanceBazan iya fada muku irin cakwakiyoyin da ke cikin littafin nan ba ku dai kawai ku biyoni 'yar mutan zazzau don jin yadda labarin yake