Gaba daya ta koma kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da suka zo gidan Waziri haka take zama wata saliha, bata sakewa har sai sun bar gida, wannan karon kuma zuwan gaba daya tai dan bata san ranar komawarta ba.
Gashi nan tana jinta kamar tana gidan yari, domin yaran Baba Waziri basa fita ko'ina daga makaranta sai gida sai kuma wata hidimar idan ta tashi, gara ma a can masarautar tana iya yin karyar zuwa wani guri Ammy ta barta ko ta samu Sirleem ya fita da ita ko Hajiya Karama, nan fa? Gaba ta kasa sakewa ko breakfast bata fitowa ayi da ita kamar yadda aka saba yi tare da kowa sai ta shige cikin daki ta zauna ita kadai sai idan an kawo mata nata abun karyarwa haka ma da rana, gashi nan dole ne taje makaranta kuma school bus din da bata so ce take kai ta kullum ta dauko ta.
Gaba daya ta rasa yadda za tai, wata zuciyar na raya mata ta ari wayar wani ta kira Hajiya Babba ta fada mata dan ita kadai ta ke da tabbacin zata taimaka mata ta cireta daga wannan kangin.Misalin karfe biyu da yan mintuna Motar Hajiya Karama ta shigo gidan, ta window Nana ta leka tana hangota ta sauka saman gadon da sauri ta fita a guje har tile din na kokarin zameta ta fadi. Zainab na kokari rufe motarta sai ga Nana ta fito da gudu ta zo ta rumgume ta, Zainab ta saka dariya tana cire gilashin idonta.
“You miss us right”
“Yes Hajiya Karama ki ce Ya Shattima am sorry kuma zan ce ma Ammy sorry pls ya maida ni gida”
Zainab ta taba kumatunta tana mata dariya.
“Shattima ma baya garin nan, ya koma aiki”
“Ni bana son nan Hajiya dan Allah”
“Dukanki suke?”
“No”
“Tau why? Kanen mahaifinki ne Nana yayansa kuma yan'uwanki ne, ni kaina idan na gaji da zaman gidan can wani lokacin a nan nake zuwa na kwana biyu sannan na koma, a gida nan ma ina da gata komai kike so za ayi miki, komai kike so shi zaki ci to miye matsalar ki Nana?”
“Ba a zuwa ko'ina kuma dole sai an je school both islamiya and boko”
Zainab ta rika fuskarta.
“Can baya na san kina son makaranta yanzu miyasa ba ki so?”
“Ni dai bana so kuma, kuma.... Ni bana son na gama bokon saboda kar na auri Sirleem”
Kyalkyalewa Zainab tai da dariya.
“Saboda ba ki son Sirleem sai ki lalata karatunki? To idan ba ki son zuwa makaranta ai sai ya ce ayi muku auren da wuri, Nana ki kwantar da hankalinki idan ba ki son babu dole ki bada lokaci kawai zan yi supporting din ki na hana auren Sirleem”
Nana ta zare ido.
“Har da Hajiya Babba ma za ta goya min baya ko? Shikenan ma na huta”
“Ya za ayi Hajiya ta goyi bayanki, ki ki auren danta na cikinta? Ke har yanzu ba ki da wayo?”
“Ai tana so na”
“Amman ta fi son danta dake, ki daina wannan tunanin, yanzu dai zuwa nai na ganki kuma na dauke ki muje mu sha ice cream dan san kina so”
“Yes yes, amman kina shiga cikin gidan nan Hajiya Maryam ba zata bari ba, zata ce Baba Waziri yace kar na je ko'ina”
“Okay je ki dauko veil ko hula mu je”
Da gudu Nana ta juya ta koma dakinta dake cikin gidan ta dauko wani karamin veil ta saka a kanta, ko da ta fito har Zainab ta yi reverse ta bude nata front seat. Da sauri ta shiga Zainab ta fara tukin tana kai hannunta ta dauki kwakwarda ke gefenta ta ci sai kuma ta dauko wata ta mikawa Nana, ita kuma ta karba ta fara ci, tafiyar ta su ba tai nisa ba Nana ta hango AA tsaye kusa da wani gida mai karamar kofa yana waya.
YOU ARE READING
FULANI
FanfictionFULANI -The story of unwanted girl, she always had a strong sense of destiny...! The story of a Prince and his kingdom. witchcraft, distorted relationships, hidden secrets, selfishness.