*TSANTSAR YAUDARA*
*✍🏽'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban*
08122188717*Sad'aukarwa ga habibaties💃🏼🥰*
Kuyi following d'ina a wattpad😩🙏🏾
https://www.wattpad.com/user/Naanarh2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=QUEENNASMERH08&wp_originator=Dc2LE0SO%2FHWLF8SESpNia9X2tmmDswdF2yVF%2FzkeABanEPiB8ElGpzFZb%2BI0yUUGqaOTCo28dfUw3u4i2mEF9RHgjz8oxYHgjF%2Fb0pqg0Ccscg9BjMmx%2BSBdzfiFB2K%2B
*Ku turo kud'in littafin SO SHU'UMI ta wannan account number 0017770369 Unity bank, Aisha Yusuf Muhammad ko kuma katin waya ta wannan number 09033927841 MTN #300😍*Shafi na 10
"Abba, Khausar karku yi min haka karku tarwatsa min farin cikin mahaifiyata, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un meke shirin faruwa damu ne, wannan wace iriyar muguwar k'addara ce take shirin fad'owa cikin rayuwarmu" Haka dai yay ta sambatu ya d'auki kusan awa d'aya yana abu d'aya daga k'arshe ya mik'e ya shiga mota ya ja ta jikinsa gaba d'aya a sanyaye yake kamar anyi masa duka, ni kuwa 'yar mutan zazzau nace Abdurrahman baka ga komai ba ma😹🔥.
Kai tsaye gida ya huce yana zuwa yay parking ya fito daga cikin mota yana tafiya yana had'a hanya har ya isa babban falon gidan, ko sallama bai iya yi ba ya zube a kan kujera, Mummy wacce ta fito zata shiga kitchen ganin Abdurrahman haka yasa ta k'araso wajen da yake tana cewa "My son lafiya kuwa??" D'agowa yay idanuwansa sun chanza kala yana cewa "Mummy, Abva zai kashe mu da bak'in ciki wai Khausar fa zai aura" Hajiya Saratu ta tafi gaba d'aya ta fad'i 'kasa sumammiya, a gigice Abdurrahman ya mik'e yana kiran sunan mahaifiyarta sa "Mummy! Mummy!! Mummy dan Allah ki tashi" Yay maganar yana zubar da hawaye, su Abdulfatah ne suka fito daga d'akinsu saboda jiyo kukan Abdurrahman da sukayi, ganin mahaifiyarta su kwance a k'asa ne yasa suka k'araso wajen da gudu suna tambayarsa "meya faru da Mummy" Abdurrahman yana kuka ya fad'a musu abin da ya fad'awa Mummyn ya sa ta fad'i, hannu Fanal ta dora akai tana cewa "Mun shiga uku Khausar, Abba zai aura wayyoo Allah na" Meenal ta ce "Yaya ba fa kuka zamu tsaya yi ba, ya kamata akai Mummy asibiti" Abdulfatah ya ce "Gaskiya kam, yanzu ba lokacin kuka ba ne" Haka suka kama Hajiya Saratu suka fita waje da ita, a mota suka sakata, Abdulfatah, Abdulrahman da Abdul'aziz su suka shiga motar da Hajiya Saratu take, Sai su Meenal su ma suka shiga motarsu ta, suka jaa da sauri mai gadi ya bud'e musu gate suka fita daga gidan da gudu, wani asibitin kud'i suka nufa da ita, suna zuwa daman Minal ta kira mai asibitin ta ce gasu zasu kawo mahaifiyarsu, nurses suka fito da gadon d'aukar mara lafiya, fito da Hajiya Saratu sukayi aka dorata a kan gadon suka nufi EMERGENCY ROOM da ita, Abdurrahman suka zauna jugum-jugum zuciyoyinsu cike da tsantsar bak'in ciki.
8pm⏰
K'arfe takwas na dare Doctor Sharaddeen ya fito daga d'akin da aka kwantar da Hajiya Saratu, Abdurrahman ya nufosa da sauri har yana tuntub'e yana cewa "Doctor ya jikin Mummyna" Doctor Sharaddeen ya bi sa da ido yana cewa "Ta ji sauk'i amman gaskiya ba zan b'oye muku ba, Mahaifiyarku tana cikin tsananin damuwa, zuciyarta tana kok'arin bugawa lokaci d'aya, ya kamata ku dinga kula da ita sosai" Abdurrahman ya dafe kai ba tare da ya ce komai ba dan wani irin sarawa kan na sa yake yi, Doctor Sharaddeen ya huce office d'insa yana tafiyarsa ta isa da izza, Abdul'aziz ne ya shiga d'akin da sallama su Abdurrahman suka rufa masa baya su ma bakinsu d'auke da sallama, a kwance suka ganta tana zaune tana shan kuka, k'arasawa kusa da ita sukai kowannansu ya samu kujerar roba suka zauna, amman Abdurrahman a kusa da ita yana cewa "Mummyna ki kwantar da hankalinki ki daina kukan nan kada kanki yay ciwo, insha Allahu ko Khausar ta auri Abba babu abun da zai faru sai alkhairi" Hajiya Saratu ta ce "Abdurrahman wallahi mutuwa zan yi, ni na san ba zan tab'a iya rayuwa ba muddin idan Abbanku ya auri wannan yarinyar" Abdul'aziz ya ce "Mummy ba za ki mutu ba, babu abin da zai sameki kada ki damu kanki dan Allah kije ki kamu da wani ciwon" Minal ta ce "Gaskiya kam Mummy ki kwantar da hankalinki ko Abba ya auri Khausar ai ba wani abun".........Wani irin mari Fanal ta wanketa dashi cikin zafin nama ta fara magana "Ai daman ke bakya tab'a ganin laifin Abba, komai yay je dai-dai ne a wajenki shashasha wacce bata kishin uwarta" Finat ta ce "Kyaleta Fanal ai ita daman bata son Mummy kwata-kwata, banza kawai kina yin abu kamar wata dabba" Hawaye ne ya shiga zuba daga cikin idanuwan Meenal, Abdulfatah cikin jin haushin abin da Fanal da Feenat sukayi wa Meenal ya daka musu wata muguwar tsawa da sai da suka razana gaba d'ayansu ya ce "Ke Fanal har kin isa ki mareta saboda ke dabba ce tana fad'ar gaskiya shine za ki daketa, ki bata hak'uri bata hak'uri nace" Ganin Fanal d'in tak'i ba wa Meenal hak'uri ya sa ya daddage ya zabga mata wani wawan mari da sai da ta tsugunna k'asa ta dafe gurin da ya mareta, Mummy cikin yanayin b'acin rai ta ce "Wato Abdulfatah bakwa sona kwata-kwata baku ma damu da ni ba, kawai ku ta Abbanku ku ke yi ai shi ke nan" Ta k'arasa maganar tana kuka, Abdullahi ya ce "Mummy gaskiya su Yaya Abdulfatah suke fad'a dan Abba ya auri Khausar ba wani abu ba ne, idan anyi la'akari da irin yaudarar da Yaya Abdurrahman yay mata, koma wace mace ce dole wannan matakin za ta d'auka" Abdurrahman ya yunk'ura zai mari Abdullahi yay saurin kaucewa ya nufi kofar fita daga d'akin, Abdulfatah ya kama hannun Meenal suka fita su ma, Abdul'aziz shima ya bi bayansu da sauri da kuwa ba zai zauna ayi fad'an rashin gaskiya dashi ba, su suka ja duk abin da Khausar tai yi musu da wanda za ta yi musu nan gaba dan ya san akwai babbar drama a gidan nan idan Khausar ta shigo cikinsa.
Mota suka shiga suka koma gida zuciyoyinsu babu dad'i sam📚✍🏽
*Hi habibaties shim kun shirya cigaba da karanta littafin BABANA NE SANADI book 2???? To idan eh ne amsarku maza ku matso kusa dani domin zan fara yi muku posting d'insa 1st OCTOBER kowannanku zai biya #200 domin cigaba da karantashi na saka shi October ne dan kowa ya biya ya samu damar karantashi, idan shi da SO SHU'UMI ka ke so to zaka biya #500 shi amman SO SHU'UMI har na fara posting d'insa zaku iya fara yin payments d'inku tun daga yanzu ta wannan account number 0017770369 Unity bank,Aisha Yusuf Muhammad, sai ku turo shaidar biya ta wannan number 08122188717*
*Ni dai na shirya tsaf domin ganin yawan adad'in fans d'in BABANA NE SANADI idan baki karanta book 1 ba to ki biyoni ta wannan number 08122188717 domin na baki shi book 1 free ne book 2 ne paid book😍💃🏼*
*Please🙏🏾*
*Share😰*
YOU ARE READING
TSANTSAR YAUDARA
RomanceBazan iya fada muku irin cakwakiyoyin da ke cikin littafin nan ba ku dai kawai ku biyoni 'yar mutan zazzau don jin yadda labarin yake