Fadime ta kara lakkamo Ma'u tana dariya
"Wallahi kuwa"
Ma'u da rufe baki tana zaro ido.
"Kuma Wallahi da gaske koko na sa da safen nan, Fulani da gaske kin iya"
Wani kalar dadi ya kara rufe Fadime jin ta canki abun da Ma'u ta karya da shi yau, bayan ta gama fada mata ita tana da aljannu kuma suna sa ta gane komai na mutum.
"Yanzu kenan za ki iya fadawa mutum abun da zai same shi"
"Eh amman sai na yi bachi, amman dan Allah Ma'u karki fadawa ko sai wanda kika yarda da shi, idan Bappa ya ji zai min fada ko ya doke ni ma"
"Ba zan fada ba"
Fadime ta yi dariya.
"Inna tace masu irin wannan abun kudi ake ba su, idan kina ga wani na son a masa ya bada kudi ki kawo shi zan masa amman a boye"
"Aiko zan ta kawo miki mutane Wallahi, sai ki sammin wani abu ni ma"
Sai da hantsi ya bude sosai sannan Fadime ta bar kofar gidansu Ma'u ta dawo gida. Kai tsaye ta nufi bukkatarta ta dauko biro da littafinta ta fara rubuta hau Amo tace zata kawo mata miji, kuma ta fadawa kawarta Ma'u cewar tana dubi.
Gaba daya wunin ranar wuni tai cikin farinciki da jindadi kana ganinta kasan dadi take ji tana murna wai Amo ta mata miji kuma a bunni.
Amo dai sai kallonta take a ranta tana fadin'Zaka si ubanka idan ka aureshi mutuwa za kai, idan ka gagaran ci ai ba ka gagari wani ba'
Ta fada tana dan murmushi sai da Fadime ta mike tsaye tana kora shanu zuwa daji Amo ta lura yau wutar nan bata biye da ita, a razane ta mike tsaye tana bin bayanta da kallo.
Inna ma ta mike tsaye daga can cikin bukkar da take zaune tana kallon Amo, wacce razanar ta bayyana, Inna daman can ta dade tana zargin Amo da maita ba tun yau ba, tun daga lokacin da ta bata labarin cewar suna da maitar gado wacce ake bawa yara tun suna kanana amman ita Allah ya tsareta ba a bata ba, ga yayan wabin da Inna tai ta yi a duk inda take neman magani sai ace manya ce take cinye mata yaya, wani cikin ma tun kan ya zo duniya zata yi barinsa, Fadime ce kawai ta rayu ita ma daker dan babu kalar ciwon da ba tai ba, Allah ne dai ya rata ta da kuma addu'oin da take yawan yi mata, Bappa ma yana mata sosai har rubutu yake mata ya bata ta sha, tun a wacan lokacin idan Inna ta fada masa tana zargin Amo sai ya karyarta yace baya son tashin hankalin, har yake ganin kamar kamar Inna tana haka ne saboda Amo kishi, bayan kuma ita ta zo ta tararda Amo.Sunsunsun Amo ta shige bukkarta da mugun mamaki, ta sani wani sa'in ana samun akasin abun da tai mata, sai dai ba ko yaushe ba, domin Fadime babu ruwanta da addu'a sai dai idan yi mata akai, kuma wannan wutar ta dade da saka mata ita tun Fadime na karama, taya yau rana daya za a wayi gari babu ta? Ko dai Inna ta karbo mata wani maganin ne? Idan ba haka ba gaya wutar ta bar binta? Adakin ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya.
A kullum idan Fadime zata je kiwo sai ta saka shanun gaba tana binsu a baya, ban da kwana biyun nan da take son sake ganin Wasim, kullum baya take baro shanun sai idan sun kawo kansu. Tana isa ta haye saman dutsen ta fara kiransa.
"Mai busa"
Haka take kiransa a duk lokacin da ta iso gaban dutsen, duk kiran da zata masa kuma ba zata ganshi ba, ba zata ji busar ba, bata kuma fasa kiran ba. Sai dai shi yana saukowa kasa ne ya boya jikin dutsen yana kallonta har tai abunda za tai ta gama.
Sai da ta sauko saman dutsin sannan ta ganshi kasa tsaye ta inda zata ganshi yana kallonta fuskarsa da murmushi, dan tsoro ta ji."Kenan shi aljanin dutse ne?"
Ta raya a ranta, a fili kuma sai ya kara hayewa saman dutson alamar ba zata sauko ba. Ganin hakan yasa ya fara haurowa saman dutsen still yana mata murmushi.
YOU ARE READING
FULANI
FanfictionFULANI -The story of unwanted girl, she always had a strong sense of destiny...! The story of a Prince and his kingdom. witchcraft, distorted relationships, hidden secrets, selfishness.