*TSANTSAR YAUDARA.*
*✍🏽'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban*
*Sad'aukarwa ga habibaties💃🏼💞*
*Kuyi following d'ina a wattpad😰*
https://www.wattpad.com/user/Naanarh2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=QUEENNASMERH08&wp_originator=Dc2LE0SO%2FHWLF8SESpNia9X2tmmDswdF2yVF%2FzkeABanEPiB8ElGpzFZb%2BI0yUUGqaOTCo28dfUw3u4i2mEF9RHgjz8oxYHgjF%2Fb0pqg0Ccscg9BjMmx%2BSBdzfiFB2K%2B*Shafi na 11*
Hajiya Saratu, Abdurrahman, Feenart da kuma Fanal suka bi sauran 'yan uwannasu da kallo zuciyarsu cike da bak'in cikin abin da suka yi wa mahaifiyarta su, wato hakan yana nufin cewa sun juya mata baya kenan sun fi son mahaifinsu a kanta kuma suna goyan bayan airen Khausar da zai yi, wani irin wahalallen kuka ta shiga rairawa abin ban tausayi, Abdurrahman ya dinga bata hak'uri har ta yi shuru, Hajiya Saratu ta uzura sai an sallameta a ranar, gashi ba wani sauk'i ta ji ba, idan da so samu ne tayi kwana biyu a asibitin ana bata kulawa ta musamman, amman ganin yadda take kok'arin tayi musu hauka a cikin asibiti yasa dole suka sallameta suka tafi gida.
Suna isa gidan suka tarar da motar Alhaji Saleh haka ya nuna alamar cewar yana cikin gidan, ga kuma motar su Abdulfatah, cikin zafin nama Hajiya Saratu ta bud'e motar ta fito, ta nufi hanyar da zata sadata da babban falon gidan, su ma Abdurrahman fitowa sukayi suka rufa mata baya da saurinsu, Hajiya Saratu da shiga falon ba tare da tayu sallama ba, Alhaji Saleh ta gani Abdulfatah,Abdul'aziz,Abdullahi da kuma Meenal duk suna fallon sun saka shi a gaba suna yi hirarsu ta duniya suna dariya, ganinta ne yasa kowannansu ya tashi yana kok'arin hucewa b'angarensa, cikin murya b'acin rai ta dakatar dasu da cewa "Munafikai ku dawo ku zauna, wad'anda basa k'aunar farin cikin mahaifiyarsu wato ku zama ku ke yi wannan d'an iskan yana yi muku hira kuna dariya hankalinku a kwance" Alhaji Saleh yay kanta yana shirin kai mata duka yaranta suka shiga tsakani suna bashi hak'uri,cikin rawar murya ya ce "Ni ne d'an iskan Saratu wato rashin mutuncin na ki ya kai ga haka, a gaban yarana ki ke tozarta ni"
Hajiya Saratu tayi masa wani irin kallon kask'anci ta ce "To kai daman ka na tunanin zai iya d'aga maka k'afa ne, banza mayaudari maha'inci azzalumi, mai budurwar zuciya saboda asara yarinyar da suka yi soyayya da d'anka ita zaka zagaye ka je kace ka na sonta saboda zuciyarka ta gama mutuwa".
Abdulfatah ya ja hannun Abba ya ce "Abbanmu dan Allah ka tafi b'angarenka dan Allah ka da ka ce zaka tsaya anan har ku yi abin da bai dace ba kai da Mummy" Alhaji Saleh ya nufi b'angarensa ba tare da ya ce komai ba zuciyarsa na yi masa zafi, wayarsa ya d'auka ya shiga kiran number Khausar amman sai ya jita a kashe, kansa ya dafe tare da cewa "Ohhh ashe wayar babu chaji" Kwanciya yay yana jero addu'o'i kala-kala har ya samu nutsuwa a zuciyarsa, Hajiya Saratu kuwa Abba na shiga b'angarensa ta nufo wajen da su Abdulfatah suke cikin fushi, da sauri suka tarwatse kowa ya shige d'akinsa tare da saka key.
Abdurrahman ya kama hannun mahaifiyarta su ya kai ta b'angarenta sannan ya fito ya shiga d'akinsa ya kwanta a kan gadonsa, gaba d'aya ransa duk a dagule yake bak'in cikin abin da Abbansa yake shirin yayi musu ya san shi zai kasheshi, wayarsa ce ta shiga ringing da sauri ya kalli screen d'in wayar "Habibaty❤️" Sunan da ya sakawa number Fad'ima kenan da sauri ya d'aga tare da yi mata sallama cikin dasasshiyar muryarsa "Assalamu alaikum" Fad'ima wacce take kan gado ta dora k'afarta d'aya kan d'aya tana karkad'asu ba tare da ta amsa sallamar ba ta ce "Habibina na san mun yi nasara ko" Abdurrahman ya ce "A'a Habibaty ba mu yi nasara ba kuma ba za mu tab'a yin nasara ba, Saboda Khausar ita ce za ta auri Abbana yayarta Rahma kuma zata auri Abbanki" Wata irin zabura Fad'ima tayi tana cewa "Rahma ce zata auri Abbana, Khausar abin da ta shiryo mana kenan to ni ba zan tab'a barin wannan k'udurin na ta ya cika ba ni sai na tarwatsata sai na lalata mata rayuwarta" Tana gama fad'ar haka ta kashe wayar.
_Hy! Habibaties karku ce na takura muku 😰tuni nake yi muku dan bana son ayi baku a littafin da nake rubutawa me suna SO SHU'UMI🥺daga jin sunan kun san zai yi cakwakiya ki biya kud'inku ta wannan account number 0017770369 Unity bank, Aisha Yusuf Muhammad sai ku turo shaidar biya ta wannan number 08122188717 naira 300 ne kacal_
Abdurrahman ya ajiye wayar ta gefe yana sauke wata wahalalliyar ajiyar zuciya yana cewa "Khausar kin zame min masifa a rayuwata, nayi dama sanin soyayya da ke" Tashi yay ta shiga toilet ya doro alwala sannan ya dawo ya shimfid'a dadduma yay sallah raka'a biyu, bayan ya idar ya zauna yay addu'a sosai har sai da zuciyarsa ta daina yi masa zafin da take yi, kwanciya yay a gadon bacci b'arawo ya sace shi.
*** *** ***
Fad'ima kuwa tana kashe wayar ta fad'a toilet wanka tayi ta dawo ta shirya cikin wata doguwar riga tayi kyau sosai, irin yadda tayi kwalliya sai ka yi tunanin babu abu da yake damunta a cikin ranta, mukullin motarta ta d'auka ta fito falo babu kowa dan haka ta saka kai ta fita ba tare da ta sanarwa da kowa inda zataje ba, motarta ta shiga ta ja ta yi tafiya mai nisan gaske sannan ta isa wani katafaran gida mai girman gaske kallo d'aya za ka yi masa kasan an zubar da kud'i sosai wajen gina shi, parking tai ta fito cikin takunta na isa ta shiga kwankwasa gate d'in gidan, mai gadin gidan ya bud'e mata kofar ta shiga tayi tafiyar kusan second 60 ba tare da ta isa babban falon gidan ba, wata kofa na ga ta nufa tun kafin ta k'arasa kofar ta bud'e da kanta, shiga tayi babu sallama wata kyakkyawar yarinya ce ta nufota da gudu ta rumgumeta tana cewa "Oyoyo sweetheart"Fad'ima ta zame daga rumgumar da tayi mata ta koma zauna a kan kujera tana cewa "Maryuda ki barni yanzu ba na cikin yanayin farin ciki" Da sauri Maryuda ta zauna a kan kujerar da Fad'ima take tana cewa "Sweetheart kodai kayan da mukayi order ne aka kama, dan Allah indai wannan ne kada ki damu ina kiran waya za'a sakar mana abun mu" Fad'ima ta ce "Kin san inda wannan ne ba zan ma damu ba saboda ni da kai na ma na ishesu, babu wanda ya isa ya saka a kama mana kayanmu"
Maryuda ta ce "To Sweetheart meya saka ki cikin damuwa" Fad'ima ta zauna ta fad'awa Maryuda duk abin da yake faruwa sannan cikin kuka ta cigaba da cewa "Maryuda na rasa yadda zan yi, ban tab'a tunanin Khausar za ta iya yi mana haka ba"
Maryuda ta saki wani irin lallausan murmushi ta ce "Tabbas sweetheart kin yi babban sakaci, amman kada ki damu ni zan san yadda zan yi naga an fasa auren Abbanki da Rahma da kuma Khausar da Abban Abdurrahman, Fad'ima ta ce "kin ga ni ko baki yi yadda ki ka yi anfasa auren Khausar da Abdurrahman ba ki ka saka aka fasa auren Abbana to su suje chan su k'arasa su suka sani wannan bai shafeni ba, kowa kansa ya sani" Dariya sosai Maryuda tayi ta ce "To ai shi ke nan" Suka cigaba da hirar order kayan mayen da sukayi, daga karshe Fad'ima ta tashi ta tafi gida.
*** *** ***
"Khausar! Khausar!! Khausar!!!" Da sauri Khausar ta fito daga d'akinta tana amsa kiran da Rahma ta ke yi masa "Na'am Sister mie" Rahma ta ce "Zauna muyi wata magana" Zama Khausar ta yi tare da tattaro hankalinta gaba d'aya gurin sauraro abun da Rahma zata fad'a mata "Sister mie yanzu Fad'ima da Abdurrahman sun san cewa Ni zan auri Abban Fad'ima ke kuma Abban Abdurrahman to na san ko wannan shashashan yaron bai d'auki matakin komai ba to tabbas Fad'ima sai ta yi yunk'urin raba auren, ya kamata muyi babban shiri a kan wannan" Khausar ta saki murmushi tana cewa "Sister mie na san da haka dole Fad'ima zata cewa sai an fasa auren nan, amman ba za ta tab'a yin nasara ba wannan alk'awarina ne sai mun cika muradinmu"
Rahma ta ce........................📚✍🏽
*_HABIBATIES INA MAI K'ARA SANAR DA KU CEWA LITTAFIN BABANA NE SANADI BOOK 2 ZAN CIGABA DA TYPING 1st OCTOBER🔥🔥 KU TANADI NAIRA 200 DOMIN KI SHA KARATUNKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI WANDA BAI KARANTA BOOK 1 BA TO KU BIYONI TA WANNAN NUMBER 08122188717 BOOK 1 FREE NE ZAKU IYA YIN PAYMENTS D'INKU TUN DAGA YANZU🔥🔥IDAN HAR DA SO SHU'UMI KUKE SO TO ZAKU BIYA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0017770369 UNITY BANK, AISHA YUSUF MUHAMMAD, SAI KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08122188717_*
*MRS BREAKER*
08122188717
YOU ARE READING
TSANTSAR YAUDARA
RomanceBazan iya fada muku irin cakwakiyoyin da ke cikin littafin nan ba ku dai kawai ku biyoni 'yar mutan zazzau don jin yadda labarin yake