Babi na ɗaya

5 1 0
                                    

*_ASHOBE_*



©️ *HUSSY SANIEY*

*______________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/

*ASHOBE*
              (*Gajeren labari*)
    *HAƘƘIN MALLAKA*
*Hussy Saniey*

*NA SADAUKAR DA SHI GA MATE ƊINA 'YAN WTC KATSINA*

*BABI NA ƊAYA*

"Oh ni! Halilos yanzu ga bikin Fati Tukur ya kusa amma ban da anko ko ya zan yi? Amma bari ki gani in kira ƙawata Hussy in gani ko zan samu mafita."
Tana faɗin haka ta jawo rugujajjiyar wayarta da glass ɗin wayar duk ya fashe, ganin wayar duk ta yi ƙura yasa ta tofa miyau  akan screen ɗin wayar ta jawo gefen rigarta ta goge, sai da ta goge wayarta tsab sannan ta lalubo lambar Hussy ta danna mata kira bugu biyu Hussy ta ɗaga, tun kafin Hussy ta ce komai Halilos ta rigata magana ta ce,"Ƙawata ina cikin yanayi wallahi!"
"Innalillahi! Ƙawata me yafaru ne?"
Hussy ta faɗa cikin faɗuwar gaba, jin yanayin da Hussy ta yi magana yasa Halilos faɗin,"Ke ki ƙwantar da hankalinki ba wani abu ba ne akan ashoben Fati Tukur ne ga biki ya zo amma har yanzu ban siya ba."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hussy ta saki sannan ta ce,"Wallahi Ƙawata kin tada man hankali na yi tunanin wani abu ne ya faru."
"Haba ai dole na damu yanzu kina ganin bikin ya kusa amma babu abin da na siya."
Halilos ta faɗa tamkar marainiyar Akuya, jin a yanayin da ta yi magana yasa Hussy fashewa da dariya ta ce,"Kai ƙawata irin wannan marairaicewa haka?"
"Ban son iskanci wallahi ni kike ma dariyar?"
Halilos ta faɗa a fusace, dariya Hussy ta sake yi ta ce,"Ƙawata ba ke na ke ma dariyar ba Naja Bala na tuna!"
Hussy ta ƙara fashewa da dariya saboda tunawa da Naja Bala da ta yi.
"Ke fa banza ce ya za kiyi ta man dariya a kunnuwa, ɗan bani labarin abin da ya faru da Naja Bala ɗin."
Halilos ta faɗa cike da son jin gulma, dariya Hussy ta sake yi ta ce,"Naja Bala ce ta kai wayarta kasuwa dan ta siyar ta samu kuɗin sayen anko, amma ana amsar wayar aka duba sai aka ce mata an saya dubu uku da ɗari biyar."
Wata irin dariya Halilos ta fashe da ita sai da ta yi mai isarta kafin ta ce,"Ƙawata nima fa da wayata zan siyar in sayi ankon sai in samu mai malatsai in ɗora wayata, amma jin wannan maganar ta Naja Bala har kin sanya jikina ya yi sanyi."
Murmushi Hussy ta yi dan tunawa da ta yi da yadda wayar Halilos take ta wani ɓangaren ma har gara ta Naja Bala duk da dai garar ba wata ba ce.
"Kin yi shiru ƙawata ya kike gani?"
Halilos ta faɗa cikin sanyin murya.
"A'a ba matsala ƙawata zan ma yi maki rakiya wurin da za ki siyar."
Hussy ta faɗa tana murmushi, jin haka yasa Halilos yin murmushi wanda har Hussy na jiyo sautin shi ta ce,"Ƙawata nagode ƙwarai gobe zan zo gidanku sai ki rakani."
"Ba matsala ƙawata sai kin zo."
Hussy ta faɗa tana dariya tare da kashe wayarta, duk idan ta tuna da yanda wayar take a fashe sai ta sake fashewa da dariya.
Kiran waya ne ya sake shigowa cikin wayar Hussy ko da ta duba sai ta ga Hauwa Abu ce, tana ɗagawa Hauwa Abu ta ce,"Hussy wai ya ake ciki maganar ankon Fati Tukur ne?"
Hauwa Abu ta faɗa ko gaisawa bata bari suka yi ba, murmushi Hussy ta yi ta ce,"Hauwa Abu ni dai tun turmin yinin biki da na siya da head babu abin da na sake siya ke fa?"
"Haba ai ke Hussy da sauƙi wallahi ni fa head kaɗai na siya, dan Allah Hussy ina zan samu rancen dubu goma na siyi ankon bayan biki sai na biya?"
Hauwa Abu ta faɗa tamkar za ta yi kuka, jin abin da ta ce yasa Hussy sauke ajiyar zuciya ta ce,"Hauwa Abu rancen dubu goma a wannan lokacin? Gaskiya ba na ce ba."
Hussy ta faɗa a hankali saboda tausayin da Hauwa Abu ta bata.
"Dan Allah Hussy ki taimaka man yanzu idan aka ce ban yi ankon Fati Tukur ba ai akwai matsala wallahi, kin dai san mu ne kirjin bikin!"
Hauwa Abu ta faɗa tare da fashewa da kuka.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Haba Hauwa Abu me ya kai na kuka dan Allah ki yi shiru zan bincika maki mu gani ko za a samu bashin amma dai babu tabbas ɗin za a samu."
Hussy ta faɗa saboda tausayin Hauwa Abu da ya mamaye mata zuciya saboda ita mutum ce mai tausayi.
"To shi ke nan nagode Hussy ina saurarenki."
Hauwa Abu ta faɗa tare da ƙara fashewa da kuka, da ƙyar Hussy ta samu Hauwa Abu ta yi shiru daga ƙarshe kuma suka yi sallama.

Hussy Saniey✍️

ASHOBEWhere stories live. Discover now