*_ASHOBE_*
©️ *HUSSY SANIEY*
*______________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https:/
*HAƘƘIN MALLAKA*
*Hussy Saniey**NA SADAUKAR DA SHI GA MATE ƊINA 'YAN WTC KATSINA*
*BABI NA Uku*
Salamatu ce gaban madubi sai ƙoƙarin ɗaura ɗanƙwali ta ke yi, fuskarta ta ci uwar ƙwalliya, da ƙyar ta samu ta ɗaura ɗanƙwalin akanta, kallon kanta ta yi a madubi ta ga komai ya yi mata yarda ta ke so, sanye ta ke da wata haɗaɗɗiyar rigar bubu ta wani haɗaɗɗen lace mai ruwan makuba an masa ado da ruwan zaiba, murmushi ta saki tare da jujjuyawa a gaban madubin ta dai ƙara tabbatar da komai ya mata yarda ta ke so dan haka sai ta ce,"Yauwa na yi kyau sosai, Allah ka ba ni sa'a Abban Zarah ya ba ni kuɗin nan gobe in yi safkon tafiya Katsina."
Tana gama maganar sai ta yi hanyar fita daga ɗakin, har ta kama hannun ƙyauren sai kuma ta yi jim na tunanin abin da za ta faɗi idan ta je gaban shi dan bata son ta kwabsa, gaban madubi ta koma ta kalli kanta cikin madubin sai ta langaɓe kanta kamar kadangare, ido guda ta kashe sai ta ce,"Abban Zarah barka da safiya!" Girgiza kai ta yi tare da yamutsa fuska alamar hakan bai yi ba.
"Sweet Husbyna ka tashi lfy?" Ta faɗa tare da murmushi, ganin ta ɗan bada kala sai ta ce,"Wannan ma ya yi amma dai zan ɗan yi ƙasa da murya irin cikin shagwaɓar nan dan ya bani kuɗi masu yawa ba tare da yasan ma ya bani ba."
Dariya ta yi ita kaɗai tamkar sabon kamu sai ta yi maƙale murya tare da yin fari da idanuwa ta ce,"Barka da safiya rabin raina!" Ganin yadda ta yi sai kawai ta daka tsalle tare da faɗin,"Yeeeeeeeh...woni Salamatu haka zan yi, ashe dai haka na iya kissa? Ba ri na yi sauri na je wurin shi."
Tana faɗin haka cikin azama ta fita daga ɗakin, ɗakin Abban Zarah ta nufa har ta kusa fita daga ɓangarenta sai idanuwanta suka faɗa akan abin aje takalmanta.
"Yauwa bari in samu takalma masu tsini yadda kafin na isa sautin takalmin zai sanar da shi, Ni kuma sai in ɗan ja aji a bakin ƙofa sai bayan wasu sakanni lokacin ya ƙosa ya ga wanda zai shigo sai ni kuma in shiga."
Tana gama maganar ta nufi wurin takalman, wasu golden half cover ta ɗauka masu tsini, ƙafarta ta sanya a cikin takalmin ba laifi ya haska ƙafar sosai, kuma ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu saboda tana fara takawa takalmin ya fara sakin irin sautin da ta ke buƙata abin ka da mai tsini akan tayil, gangarawa ta yi a barandar ta shiga ƙofar da za ta sadaka da ɗakin Abban Zarah, sai da ta ja aji a bakin ƙofa sannan ta tura ƙofar cike da yanga, sai dai kash babu kowa a falon, tunani ta yi ƙila yana ɗakin barci yasa ta nufar ɗakin ga takalminta na ta sakin jiniya, tura ƙofar ta yi tare da yin sallama cikin wata makirar murya, ganin Abban Zarah akan gado duƙunƙune yasa murmushin fuskarta ɗaukewa a fusace ta nufi gadon tana faɗin.
"Abban Zarah! Abban Zarah!!" Salamatu ta faɗa tana bubbuga ƙafar Abban Zarah.
Motsawa ya yi a hankali ya buɗe idanuwan shi da ke cike da bacci, kan fuskar Salamatu ya tsaida idanunwan shi, ganinta cikin shiri ya sa shi buɗe idanuwan shi sosai akanta, gasgata cikin shirin dai ta ke ya sa shi ce wa,"Ina za ki haka?"
Baki ta turo gaba sai ka ce shantu, haushin bai yaba ƙwalliyar ba yasa ta manta da wata shagwaɓa da za ta yi sai ta ce,"Kuɗin ashoben za ka bani."
Jin abin da ta faɗa yasa shi tashi zaune ya ce,"Wane irin ashobe kuma?" Ya tambaya cike da mamaki dan shi dai bai san da wani ashobe ba.
"Ƙawata ce za a yi bikinta a Katsina shi ne na ke son ka ban kuɗin ashoben dan tun gobe zan tafi Katsinar!"
Ta faɗa tare da ɗaure fuska dan ma kar ya kawo mata wasa dan ta ga alamar ba badawa zai ba.
Cikin mamakin abin da ta faɗa ya ce,"Wai kina nufin ƙawarki za ta yi aure shi ne za ki tafi Katsina bikin? Ba ma wannan ba yaushe ake bikin?"
"Saura ƙwana goma amma gobe zamu haɗu gidan Super admin kowa zai bada kuɗin ashoben."
Ta faɗa babu fara'a ko kaɗan a fuskarta, dan gani take idan ta yi dariya ba zai barta zuwa ba.
"Kuma duk ba ki tashi faɗa man ba sai yanzu hakan da ki kai kin yi daidai ke nan?"
Ya faɗa tare da kafeta da idanuwan shi, ganin haka yasa ta janye tata fuskar.
"Ka yi haƙuri toh!" Ta faɗa tare da ƙara ɗaure fuska. Ganin abin da ta yi yasa shi ce wa.
"To har bikin ba ki zuwa sai ki je idan kin isa."
Tana jin abin da ya faɗa sai ta fashe da kuka, banza ya yi ya kyaleta amma har cikin ran shi ya ke jin sautin kukan, ganin ta ƙi yin shiru yasa shi lallashinta har ta yi shiru. Ganin ta yi shiru ya ce,"Kamar yadda na faɗa maki da farko babu inda za ki je gaskiya sai lokacin bikin, ki ba da account(asusun banki) ɗin da zan tura masu kuɗin ashoben amma daga yau idan har kika ƙara yi man irin wannan tambayar wallahi babu inda za ki je!"
Yana faɗin haka ya miƙe tare da nufar banɗakin da ke cikin ɗakin.
"Ni fa gaskiya sai na je da kaina."
Ta faɗa tare da zunɓuro baki gaba, jin abin da ta faɗa yasa shi juyowa a fusace ya ce,"Tun da abin na ki ya zama haka har kuɗin na fasa badawa kuma babu inda za ki je."
Yana faɗin haka ya yi shigewar shi ba tare da ya tsaya jin abin da ta ke faɗa ba, daga cikin banɗakin yana jiyo gunin da ta ke, banza ya yi ya kyaleta har ta gaji ta fita daga ɗakin.
Sai da ya gama duk abin da ya ke lokacin ya nufi ɗakinta, babu kowa a ciki dan haka ya tura ƙofar banɗakinta nan ma babu kowa, mamaki ya kama shi na inda ta shiga, kitchen ya leƙa can ma bata nan, bakin gate ya nufa wurin Maigadi dan ya ji ko ya ga fitarta, yana zuwa suka gaisa, sai Maigadi ya miƙa ma shi wata guntuwar takarda, buɗewa ya yi rubutu ne ɗan kaɗan _*Na tafi gidanmu*_ iya abin da ke ciki ke nan, cikin gidan ya koma dan ya ɗauki wayar shi, falo ya zauna bayan ya ɗauko wayar zuciyar shi cike da tunanin wannan rashin hankalin da ta aikata, wayar yayanta ya kira sun daɗe suna magana kafin ya kashe ya ɗauki makullin motar shi ya fita daga gidan.Hussy Saniey.✍️
YOU ARE READING
ASHOBE
ActionLabari ne akan yadda mata ke hana kansu zaman lafiya saboda ashoben biki.