"YA ZA'AYI IN GANKI?
my romantic journey.Diff! naga an dauke wutar lantarki, lokacin da nake kokarin fitowa daga bandaki, naji takaicin da yasa har nayi tsaki, zuciya cike da mamaki, a Kasata in kaga wadatacciyar wutar lantarki, to sai a unguwar Mawadata ko masu mulki, kashh! Ya Allah ka gyara Al'amuran Kasata bisa babban tafarki,
Addu'ar da nayi a zuciyata kenan sa'ilin dana iso daki, dayake irin dakin nan ne dake hade da bayi aciki, gefen Gadona nayi birki, na lalubi wayata jikin soket din dana makalata, don inyi cajinta, ina dauka cikin hanzari na kunna cocilarta, haske ya tabbata, yayinda agogon dake fuskar wayar ya nunamin karfe daya dai-dai, dayan dare nake nufi mai karatu karka manta dai, ayam! sai ga wani sako ta watsap da yake a kunne nabar data ta, lambar ba suna bare har in shaidata, sai na gyara zama don in karanta."Aslm Muhsin, barka da warhaka, nice Marshak mai matukar kaunarka, duk abinda zaka jii daga gareni don Allah karkayi shakka, kar ya tsorataka, yanzu haka ina kallonka, saboda ina tare dakai acikin dakinka....
A firgice na wawwaiga banga kowa ba, duk kusurwoyi hudu na dakin na hanga amma banga komai ba, nayi ajiyar zuciya karanta sakon na cigaba, "basai na rantse maka ba, amma ka gasgata ina tare dakai ba karya nake maka ba, ni mutum ce tamkar ka ba tsorataka nake ba, duk abinda nakeyi sone yasa haka ba don in cutar dakai ba, da babu So' da zuciya ta huta, da dani dakai babu wata alaka ta abota, sakon bankwana daga zuciyata zuwa taka shine, natsuwa, nishadantuwa, da karuwa zasu kaurace gareka matukar bani na aureka ba, Asuba tagari ya farin duba.Ina gama karanta sakon, data ta na kashe nayi zumbur na mike lungu da sako na dakina na lalleko, lokacin hunturu ne saboda ana muku-mukun sanyi amma duk da haka zufa ajikina ta safko, akwai matsala! sakar da zuciyata keyi kenan tana dako, husshh! hakika ahalin yanzu tsoro agareni yayi sammako, donkuwa lakka, bargo da jijiyoyin Jikina sun saki sunyi sakwo-sakwo, hahmm Marshak! wacece kuma haka?
Tambayar dana yiwa kaina kenan zuci har baka, na cigaba da sakar zuci tamkar rashin sa'ar cinikin Dandako, na dawo na zauna gefen gadona hade dayin tagumi nayi cirko-cirko, kwatsam! sai naji wata dariya abisa iska ilahirin dakin na amsawa tamkar amo irin na ecko, hade da furicin wasu kalamai cikin tattausar murya kamar ta Mairoko, ko ince wanda yazo yin biko,
"Kaga irinta ko? kawai ka yarda ayi mana baiko, Ka huta in huta mu more rayuwarmu babu tsaiko.Dan danan na hau kyarma jikina na rawa, sama da kasa na kama duddubawa, cikin hanzari nayi yunkurawa, kofar daki nayi dosowa, ina isa nayi budewa, na shigo falo nayi haskawa, sam-sam babu kowa, nayi ajiyar zuciya sai na sake jin motsi a bayana tamkar ana tahowa, a razane cikin hanzari nayi waigawa, sai naga inuwa tamkar suffar Mace tayi gilmawa.
Yayinda naji an sake cewa, " Nafa riga na fada maka babu Kai babu sauran natsuwa, kuma babu abinda zaisa in canza kudirina akanka ina kara jaddadawa"
Daga sa'in muryar tayi yankewa, cikina ya tsure amma zuciya ta fara dakewa, na tsaya cak na kasa motsawa....
YOU ARE READING
Ya Za'ayi in ganki?
Romancemy romantic journey, it's a tale of unusual situations of Love, that seems to be a night mare, but naturally real......