*HAKƘI*
_Labari a kan rayuwar wasu ƴan matan!_
*TSARAWA DA RUBUTAWA*
*Hafsat Tukur Bello*
{AUTAR MAMA}Follow me on Wattpad @AutarMama56.
*Wannan littafin sadaukar wane ga duk masu hali irin na Mariya, da ma waɗanda suke shirin afkawa*
1️⃣
"Yanzu ke Mariya har yanzu bakiyi wannan wanke- waken ba dama? Ga rana ta take kuma kin sani sarai zakiji makaranta ko? Zunɓuro baki Mariya tayi tana danna wayar dake hannunta ƙirar infinix smart 5 ta ce " Wallahi Mama kin fiye takura, ina Farida ki kirata tazo tayi wanke-wanken mana! Sai kace ni baiwa ce haba, ko wani aiki ace Mariya ace Mariya" Riƙe baki Mama tayi cikin faɗa ta ce " Wato abin naki har ya kai haka Mariya? Nifa ba yarki bace, mahaifiyarki ce" Tashi tsaye Mariya tayi tana turɓune fuska ta ce " Toh ni me nace? Abi a takurawa mutum" Daga haka ta shige cikin ɗaki tana doka kafa da ƙarfi.
Girgiza kai Mama tayi a fili ta ce " Allah ya shiryeki Mariya" Tabarmar da Mariya ta tashi daga kai ta nannaɗe tana jingine ta jikin bango. Sallama a kayi, wata budurwace me ɗan tsayi ta shigo cikin gidan fara ce sosai, tana kama da Mariya sai dai Mariya chocolate color ce, kuma da alama Mariya ta girme mata dan wannan bazata wuce 15yrs ba Mariya kuma zata kai 18. Ƙarasowa cikin gidan tayi bayan Mama ta amsa sallamar. Cikin alamun nuna gajiya ta kalli Mama ta ce " Ga kayan miyan, wallahi kuka tsada take yi yanzu ga wahalar samu shine na siyo kuɓewa" Murmushi Mama tayi tana karɓar ledar hannunta ta ce " Bakomai sannu, jeki huta bari nazo na haɗa wuta a ɗora girki saboda makaranta" Mariya ce ta fito daga ɗaki tana danna wayarta ta kalli budurwar ta ce " Me kika ce? Kuɓewa wace iriyar kuɓewa? Danya ko bushasshiya? "Bushasshiya ce, idan kina da kudin ɗanyar kije ki siyo" Mama ta faɗa tana barin wajen.
"Ai kuwa sai dai kuci kayarku, Allah na gani bazanci kuɓewa bushasshiya ba, ke Farida ga wanke-wanken chan kije kiyi" Idanun budurwar na kawo kwallah ta ce " Aunty Wanki fa zanyi yanzu 12 ta kusa kuma kinsan ƙarfe 1:30 ake shiga makaranta" Cikin faɗa Mariya ta ce " Ni kike so na miki wanke²? Mama dake wajen soro tana ƙoƙarin kunna icce ta juyo ta kallesu ta ce " Farida yi haƙuri kiyi wanke² ni zan miki wankin idan na haɗa wutar, Allah ya shi miki albarka" Share hawaye Farida tayi ta ce " Amin Mama" Daga haka ta nufi bakin fanfo danyi wanke².
Taɓa baki Mariya tayi ta koma ɗaki ta cigaba da chatting ɗinta ko a kwalar rigarta.......
Yawan comments yawan typing.
Comment and vote pls
Autar Mama ce.
YOU ARE READING
HAKƘI ✓
General FictionStory of 2 young ladies Mariya and Farida, it's all about love, regrets, destiny and sacrifices.