BABI NA BIYAR

3 1 0
                                    

*_ASHOBE_*



©️ *HUSSY SANIEY*
         *OUM DEEDAT*

   *______________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

*NA SADAUKAR DA SHI GA MATE ƊINA 'YAN WTC KATSINA*

*BABI NA BIYAR*

Zumbur Naja tayi daga dogon tunanin da ta faɗa jin muryar ƙawarta Hussy na dosa sallama.

Da sauri ta fito daga cikin ɗakin nasu tana gyara ɗaurin ɗankwali.

Umminsu Najar ce daga kitchen ta shiga amsa salamar, tana mai faɗin "Wai Naja ba zaki fito ba ne? Tun ɗazu kin zauna kin yi zugum, ni na rasa wannan dalili wallahi."

"Gani Ummu" Najar ta faɗa, tana mai kallon ƙawar tata, ta sakar mata murmushin yaƙe.

"Ƙawata ke ce? Kaman kinsan a kusa wallahi na ke neman ki"

"Nima neman naki na ke ƙawata mu shiga daga ciki dan Allah kiji"

Gaba Najar ta wuce zuwa cikin ɗaki, Hussyn na biye da ita a baya. Ita dai Ummin rakasu ta yi da idanu.

"Yara duk sun bi sun firgice saboda anko?" ta faða a fili tana mai taɓe baki, tare da cewa "Allah shi kyauta maku, ya yaye maku abin da  ke damun ku"


"Yauwa dama neman ki nake yi wallahi Hussy maganar..."

"Ashoben Fatee Tukur" Hussyn ya caɓe zancen, tana mai kai zaune bakin gadon su Najar.

"Humm kedai bari wallahi, ma kaɗa na raya, abu fa yaci tura, ke in taƙaice maki dai, wallahi ýan samarin ma duk wanda na kira da yaji maganar kuɗi sai ya zille ýan banzan, ai wallahi aka gama bikin nan korar kare zan ma su hegun"

Najar ta faɗa tana mai ƙutawa.

"Bani ruwa in kora Naja, ƙanwar duk ja ce, yo ni ke kinga wahalar da nasha yau neman bashi?"

"Bashin me? Ba naji kince zaki siya ba? Adashe kike jira?" Najar ta faɗa tana mai dire mata ruwa cikin moɗa a gaban ta.

Harara Hussyn ta maka mata, ke banson iskanci, duk tunanin ne ya saka ki kawo man ruwa a moɗa? "

Zaro idanu Naja tayi, tana mai faɗin "Na baki, wallahi jug na ajiye a ƙasa zan zuba maki, sai na zarto dasu nan, na bani ni AjaBalaaaa ke wallahi na kusa zaucewa"

"Ke zaki zauce ko Hauwa Abu?" cewa Hussy.

"Yo Hauwa Abu bata siya ba ita ma har yanzu? Gashi fa abun yana ta matsowa"

"Ai tashin hankalin kenan, ke   Hauwa Abu fa kuka ta saka man, wallahi bakiji halin da take ciki ba."

Sake dire jug ɗin ruwan Naja tayi a gaban Hussyn, sannan ta koma ta zauna daga ƙasa gaban Hussyn kaman mai neman gafara, tana mai sake rafka uban tagumi"

"Ai mu duka kun faɗo warwas wallahi, indai bamu samu yin ankon nan ba, ke ko leshin dubu ɗari zaka saka ka rufto, daga inda aka ce ba'a ganka da anko ba"

Cewa Najar, tana mai kallon yanda Hussy ke ƙyanƙyamar ruwa.

"Masalan ma dai mu da muke unguwa ɗaya, babban tashin hankalin ma ace ranar meeting tazo baka samu ka siya ba, ni nan wallahi da kika ganni banson kallon uku saura kwata, duk inda mafita take dole mu nemo ta a yanzun nan, Shiyasa ma kika ga nazo"

"Ko baki zo ba, dole nima na nemo ki, ko dai amaryar zamu kira a sirrance muce ta ara mana cikin kuɗin ƙunshin da za'a bata, kafin mu samu?"

Zaro idanu Hussy tayi. "Lallai Najar nan baki da hankali, Zarar ce zata wani baku rancen kuɗi? Kina ji ma ance har Bridal shower zatayi angon ya hana, ita kuma tace ba zata ji kunyar ƙawayen ta ba, pherty kala biyar wai zatayi? Wallahi kika bata kuɗi yanzu itama amsa zatayi, ƙarya dai ce da kowa ya ɗora ma rayuwar shi"

"Humm. Ashe kema kinji ƙawata?" Naja ta faɗa tana taɓe baki.

"Yo naji mana, maganar duniya na ɓoyuwa ne? Mu dai duk ta gama, ko kala nawa zatayi sai mun halarta, kuma sai mun kece raini a wajen ƙawaye"

Cewar Hussyn, ta faɗa tana gyara zama.

"Ƙawata akwai shawara. Me zai hana idan kina da turamen da aka kawo ɗinki baki yanka ba, muje mu jinginar dasu ko mu siyar, idan an gama bikin sai mu samu mu maida masu"

Kwalalo idanu Najar tayi kaman an shaƙe mage.

"Ummi ta kashe ni kenan? Bar ma wannan maganar wallahi ba zata yuwu ba, ni da wayata nake tunanin siyarwa, ummi ba zata ce komai ba, dama Abdul ne ya siya man ita, shi kuma tsaf zan linke shi, amman Ummu kar take kallon mu"

"Kin kuwa kawo shawara, yo ke da kina da wannan tunanin kike zaune? Tashi kuje kawai ai" cewar Hussyn tana mai miƙewa. Itama Najar miƙewa tayi tana mai jawo gyalen ta.

A tare suka fito.

"Ummi zan raka ta gidan Super Admin"

"Wacece kuma haka?" Cewar Ummin, tana  daga kitchen har yanzu bata fito ba.

"Au Zainab Maman Eeman nake nufi"

"Ai to ku gaishe ta, kada dai ku jima"

"To Ummi in sha Allah." Najar ta faɗa.

"Ummi sai anjima" Cewar Hussyn, "To ki gaida Maman ku Usaina"

Ummun ta sake faɗa itama, tana mai bin su da kallo.

"Bai dai wuce maganar ankon ai, aiki ya same ku wallahi" Ummun ta faɗa tana mai cigaba da abunda take yi.

Cikin ikon Allah, wayar Naja  kasuwar tsai tsaye an taya ta dubu shidda da ɗari da hamsin, nan ma wai dan masu siyen sun san Hussy ne.

"Ke ƙawata ban iyawa, zo mu tafi kawai, ki dubi wayar nan fa, har WhatsApp nake yi da abuta, Amman zai mata siyen wulaƙanci dan yaga mun matsu"

"A'a Naja, ki bari dai a daidaita, idan kin tafi ina zaki samu wasu kudin, ba gara idan ciko ne za'a nema a nema ba?"

"Eah to kuma haka ne Amman gaskiya ya ƙara"

"To na ƙara ðari ukku, gaskiya kinga Hajiya, idan ba zaki siyar mun a haka ba, ga wayar ki kije wani wajen kiji, wallahi na siya da daraja, dan ma Hussyn ta saba kawo mana muna siya tana dillanci anan wajen

Oum deedat ce✍️

ASHOBEWhere stories live. Discover now