BABI NA TARA

1 1 0
                                    

*_ASHOBE_*



©️ *HUSSY SANIEY*

         *OUM DEEDAT*
*______________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya

*NA SADAUKAR DA SHI GA MATE ƊINA 'YAN WTC KATSINA*

*BABI NA TARA*

"Wayyo daɗi kaheni!" Oum Deedat ta faɗa lokacin da idanuwanta suka dira akan bakon da ke hannun amarya.
"Dillah ki mana shiru, ke Fati Tukur miƙo man tawa." Shamsiya ta faɗa lokacin da take dallah ma Oum Deedat harara.
"Ke Shamsiya ba dan fa kin samu kin siya ba za ki rinƙa hantarar mutane ba yadda kika siya haka kowa ma ya siya dan haka babu wata fafa da za ki yi mana fatan kin gane?" Hauwa Abu ta faɗa tana zare idanuwa ita ala dole sai an ji tsoronta.
"Ke Hauwa Abu ina ruwanki ko kin ji na sako da ke? Ashoben da ma rancen kuɗin kika yi!" Shamsiya ta faɗa tare da turo kallabi gaba ita ga mai kuɗi.
Kusan a tare Hussy, Hauwa Abu, Naja Bala, Kangiwa suka zaro idanuwa jin sirrinsu ya fito.
"Karku cinyeni ɗanya ban dahu ba malamai ƙarya na yi ba rancen kuɗin ta yi ba ne kuma..."
"Ke Shamsiya bamu san iskanci fa, wane munafikin ne ya faɗa maki rancen kuɗin ta yi?"
Naja Bala ta faɗa har tana sarƙewa da miyau.
"Ke Naja Bala babu abin da ban sani ba fa dan haka ni ku kyaleni in ba so kuke na ida tonawa ba!"
Shamsiya ta faɗa tare da gyara zamanta irin hajiyar nan.
"Ke Shamsiya dakata ki ji bari ganin dan kina da kuɗi kin siya ashobe hakan ba yana nufin ki rainamu ba ne!" Hussy ta faɗa fuska ɗaure.
"Faɗa mata dai Hussy wallahi yanzun nan mun raba abin hiɗi, in ma ban da tana 'yar iska ina ruwanta da rancen da wani ya yi?" Kangiwa ta faɗa dan tana tsoron ita ma a tona mata asiri.
"Ku dai wallahi kun ji haushin halinku duk inda kuka haɗu sai kun saida hali? Dan Allah ku yi mana shiru mu yi abin da ya tara mu a gidan nan." Enu ta faɗa cikin jin haushin wannan abin kunyar da suke rabawa a tsakaninsu.
"Faɗa masu dai Enu, ni wallahi har sun fara ɓata man rai, yadda kika san kaji haka suke da zarar sun haɗu." Fati Tukur ta faɗa tare da neman wuri ta zauna.
"Dan Allah ku yi haƙuri a zauna mu gabatar da abin da ya taramu anan." A'isha Hamisu ta faɗa cikin sanyin murya dan duk cikinsu babu wanda ya kaita sanyi.
"Shi kenan ya wuce A'isha." Shamsiya ta faɗa tana harararsu Hauwa Abu.
"Mu ci abinci sai mu gabatar da taronmu dan marece ya fara." Oum Deedat ta faɗa tare da jawo filet a gabanta.
"Acici mala'ikun tauna!" Zeey Hamid ta faɗa tana dariya.
"Ban fa son iskanci." Oum Deedat ta faɗa tana mazurai.
Dariya gaba ɗayansu suka ɗauka, sai akai sa'a babu wanda ya sake magana, sai da aka yi nisa da cin abinci sannan Farida ta matsa kusa da Shamsiya ta yi ƙasa da murya cike da son jin gulma ta ce,"Wai Ƙawata waya faɗa maki Hauwa Abu ranto kuɗin ashoben nan ta yi?"
Kallonta Shamsiya ta yi tare da murmushi, dan tasan ƙawarta ta ƙware wurin son jin gulma, ita ma da ya ke Shamsiyar gwana ce a nan ɓangaren sai ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Ƙawata ni kin sanni da neman labari to wallahi wurin..."
"Wai ku gulmar meye kuke yi da kuka yi ƙasa da murya."
Oum Deedat ta faɗa dan ita bata son ta ga wasu sun haɗe kai wuri guda ana magana ƙasa-ƙasa.
"Ina ruwanki toh?" Farida ta faɗa cikin jin haushin katse masu firar da aka yi.
"Kuna ƙamshi ina binku da Humra!" Kangiwa ta faɗa cike da iskanci.
"Ke dai wallahi sai kin canza halinki, ni ba dan ƙwalliyar da na ke so ki man ranar kamu ba ai da na shuka maki shika-shikan rashin mutunci." Shamsiya ta faɗa tare da hura hanci gaba.
"Ku wallahi banzaye ne na ajin farko, in ba haushi kuke bani ba shegiya na ke baku da aikin yi sai masifa." Hussy ta faɗa cikin jin haushi.
"Ji banza dillaliyar waya uban wa yafi ki masifa duk nan wurin?" Hauwa Abu ta faɗa tare da hararar Hussy.
"Sai an canzoku gaba ɗayanku wallahi, yanzu haka zamu je wurin kamun ku yi ta raba abin hiɗi?" Fati Tukur ta faɗa.
"Ke wannan naman nawa ne kika ɗauke."
Biyoo ta faɗa tare da kai ma Fati Jafar cafka ga hannu.
"Ba ki iya ce wa na baki sai kin jinyatani? Ga shi nan tai ki yi ta ci tun da gida babu ai dole ki yi salama." Fati Jafar ta faɗa tare da jifar Biyoo da ƙashi a goshi.
Biyoo na jin saukar ƙashi a goshinta sai ta duƙe, nan fa aka tashi aka yo kanta.
"Innalillahi! Sannu Biyoo gaskiya Fati Jafar ba ki kyauta ba!" Enu ta faɗa tare da kallon Fati Jafar.
"Enu karta fa ta kai man da waɗannan yatsun nata duk akai fa!" Fati Jafar ta faɗa cikin jin haushi.
"Yi haƙuri Biyoo ɗago kan na luliya maku." A'isha Hamisu ta faɗa tare da kama kan Biyoo, ɗagowar da Biyoo za ta yi kawai sai wurin ya ɗauki shiru na 'yan sakanni, daga baya kuma suka bushe da mahaukaciyar dariya tamkar zasu shiɗe, wasu har da faɗuwa ƙasa ganin yadda goshin Biyoo ya koma kamar jirgi zai sauko ƙasa, ko magana sun kasa yi sai dariya da nuna goshin Biyoo da hannu, ganin abin da suke mata yasa hawaye zubowa daga idanuwanta.

Hussy ce✍️

ASHOBEWhere stories live. Discover now