Part Two Page Eleven

414 17 15
                                    



DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU yayin da 'YAR JAGORA ta dauki KARA DA KIYASHI a rashin sani.......

Littattafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu

*I dedicate this Novel to my late twinnie Hauwa'u Muhammad sani,i truly loves u sis*

Guys i lost another sister on 25th feb please pray for her to rest in peace and may jannah be her final abode thank you 🙏

Part Two
Page Eleven.

•••Zama yayi shima a qasan ya soma gaishe da Alhaji Lawal kafin ya gaisar da Hajiya Hadiza.

Alhaji Lawal ya Kalli Aneesah dake kallon Mooha yace "Aa baza ki gaida yayan naki bane."

Dan shy murmushi tayi sannan tace "Good Morning."

Jinjina kai yayi yace "How are you."

A taqaice ta amsa "Am fine." Daga nan ta maida hankalin ta kan plate din fruits din dake hannunta tana ci.

Hajiya Hadiza ta qwalawa Mai aikinsu mai suna Kaltume kira tace ta qaro plate da cup wa Mooha.

Cikin sauri yace "No Mama wallahi a qoshe nake ina gama cin abinci na taho ko a jirgi ruwa kawai na iya sha."

Murmushi Alhaji Lawal yayi yace "Toh ai ko fruits din kasha ko?"

Ya gyada kansa yace "Toh Baba."

Murmushi Aneesah tayi tace "Mum And Dad are their names."

Kallon ta yayi su kuma iyayen sukayi Murmushi kawai suna girgiza kai a tare kamar sun hada baki,baice komai ba ya maida hankalin sa kan plate din da Kaltume ta ajiye masa ta gaishe shi ya jawo shi gabansa amma bai zuba fruits din ba har saida Hajiya Hadiza tace "Bismillah mana Muhammad ko in zuba maka?"

Da sauri yace "Aa zan zuba nagode."

A hankali ya tsakuri kowanne fruit ya hada a plate din yasa fork ya soma ci yana nazartar falon cikin salo wanda ba wanda zai gane a cikinsu.

Falo ne qaton gaske wanda yaci set na kujeru guda biyu kowanne daban daban kenan za a cewa falo biyu ne a cikin daya,daga can gefe dinning area ne da dinning table mai kujeru takwas sai gefensa drawer ce ta kwanukan cin abincin da cokula.

Daga inda suke zaune tsakanin falukan guda biyu yana iya ganin yanda hotunan Aneesah suka yiwa falon qawanya,daga kowacce kusurwa akwai kamar guda biyu zuwa uku wasu ita kadai ce wasu da iyayen nata da wasu mutanen da yake kyautata zaton kakaninta ne,tun tana yarinya har kawo yanzu da take gabansa a matsayin budurwa.

Kana ganin yanda aka dauki hotunan suke kalmar data fi dacewa ka kira Aneesah dashi shine er so.

Satar kallon ta yayi ta gefen idonsa tana nan zaune yanda ya shigo ya same ta ta kalmashe qafafunta ta zura su a cikin doguwar rigar data saka kanta sanye da turban kalar rigar,hannunta wani littafi ne da alamu novel ne na turanci wanda daga dukkan alamu karatun sa yayi mata dadi sosai don lokaci lokaci take sakin Murmushi ita kadai.

Kamar tasan ita yake kallo ta dago kanta ta kalle shi shi kuma yayi saurin maida hankalinsa kan plate din dake gabansa kamar daman can shi yake kallo bata yi magana ba ta juya hannunta tana kallon agogon hannunta tace "Paa ina son zuwa salon daga can zan dan je shopping." Ta qarasa tana miqewa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now