Page 1

129 14 0
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

Nana Halima😎

*Ban yadda wani ko wata su canja min salon labari ba ban yarda a d'auka min labari a mayar dashi audio ba tare da izini ba.*

1&2

Tsaye take ta juya baya ta hard'e hannu a kirji tare da zubawa taga ido tana sauke ajiyar zuciya hannun ta dafe da saitin zuciyar ta, a fusace ta juyo ta fad'a kan gado tare da fashewa da kukan da bashi da amfani a wajan ta, bud'e dakin da akayi ya saka ta mik'e da sauri tare da goge hawayen fuskar ta tana zare ido, "Sadiya kizo ku gaisa Fahad yana waje yana jiran ki". Murya a can k'asa tace, "To ina zuwa." "Baki da lafiya ne?." Mikewa tayi tare da saka hijjabi tace, "Eh kusan hakan ciwon kai ne yake damu na, muje." Tare suka fito daga d'akin suka fito wani katafaran falo Na isa da tak'ama kafin su bude kofar falon su fito harabar gidan, tunda ta hango shi gaban ta yake fad'uwa amma haka ta daure suka karasa jikin motar da yake xaune yana danna waya, "Hubby ga Sadiyallen na fito maka da ita" Hafsa ta fad'a fuskar ta d'auke da fara'a tana kallan Sadeeya, murmushi yayi Wanda ya bayyanar hushiyar sa yace,"Sadeeyalle laifin me nayi ne aka ki zuwa mu gaisa?." Dariya ya bata a yanayin yadda yayi maganar ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun ta tace, "Laifi kuma Yaya Fahad? Kaina ne yake ciwo shiyasa ban fito ba". "Ayya sorry amma kin yiwa kanki allura ko?." Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, "is okay,Leema koma gida sai Na shigo" ta fad'a tare da murtuke fuska tana kawar da kai gefe, kamar jira take ta juya da sauri tayi cikin gida ko waiwayowa bata yi ba,kallan sa ya mayar kan Hafsa da ta had'e rai yayi murmushi tare da fadin, "Gimbiya ta sarauniya ta, wannan had'e fuska haka kar kisa na kasa bacci fa.
"Wait! Meye tsakanin ka da Halima ne? Indai kazo gidan nan baza ka tafi ba sai ka tambaye ta in tazo kuma kai tayi mata murmushi, I don't like it gaskiya." Sake sakin wani murmushin yayi tare da zubawa fuskar ta ido yace,"Haba Queen yanzu daman kishin naki har akan Halima ne? Naga kanwar kice fa jinin kice har kina tunanin wani abu a tsakani na da ita?." "To in ba wani abun ba meye zaka dinga yawan tambayar ta kana yi mata murmushi kuma?." "Kanwar kice fa why dan nayi mata murmushi? Ko baki yi min kara ta nuna ta matsayin kanwata ba ai Na nuna ta matsayin kanwar matata ko? You know I love you soo much bana tunanin wata mace zata zamu gurbi a zuciyar ta sabida kin mamaye ko ina Hafsat, pls ki daina magana akan Halima." Murmushi ta saki tare da yin farrr da manyan idon ta tace, "ina shiga farin ciki a duk lokacin da ka kira ni da matar ka nakan rasa Inda zan saka raina sabida farin ciki." Sai da ya lumshe ido kaunar ta na sake ratsa ko wanne sassa na jikin sa yace, "kece matata ta har abadah ko a aljannah ina fatan ki kasance tare dani." Sosai maganganun sa suka sata farin ciki har ta manta da wata Halima ma, "Yanzu in kaje Barno din yaushe zaka dawo?." Juya kwayar idon sa yayi alamun tunani yace,"Maybe next week insha Allah, I missed Mom that's why ma zanje na ganta." "Allah ya kaika lafiya ya dawo dakai lafiya, a gaishe min da Mummy na sosai." "Zata ji insha Allah my Queen, sai munyi waya ko?." Bata bashi amsa ba sai d'aga masa gira da tayi ya ja murfin motar sa ya rife ya motar ya bar gidan.
A 6angaren Haleematu kuwa tunda ta bar wajan ta shige d'aki ta fad'a kan gado tare da sakin kuka mai cin raiii, wani irin zafi da rad'ad'i take yi a zuciyar ta gashi bugun ta ya canja tana bugawa very fast hakan ya sa ta saka hannu ta danne side din zuciyar tana sauke numfashi, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan wacce irin kaddara Allah ya d'ora min? Saurayin Yaya ta wacce take jina na Wanda zai aure ta fa? Meyasa so zaka min haka? Sam ban yiwa kaina adalci ba ta yaya zan fad'a tarkon sa Wanda zai auri Yaya ta? Allah na rok'e ka dan matsayin annabi Muhammad S.A.W Allah na rok'e da ikon ka dan Isar ka ka bani ikon cinye wannan jarabawar ya hayyu ya qayyum ka cire min San wannan bayan naka a zuciya ta" ta k'arasa fad'a tana sakin kuka mai ban tausayi, sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta shiga band'aki dan taji ana kiran sallar magariba. Har ta idar da sallah bata shigo ba ta mike ta cire hijjabin ta dan itace zata yi girkin dare ta fito falo, babu kowa a falo shiyasa bata tsaya ba ta fad'a kitchen ta d'ora tuwon semo da miyar kuka kamar yadda Mama tace ayi, tana cikin yi aka kira sallar i'sha ta kashe gas din ta idar da sallah sannan ta cigaba da aikin ta.
Sai da ta gama kaf ta jera akan dining table sannan ta nufi hanyar da zata sada ta da karamin falo da tasan suna zaune a can, da sallama ta shiga kamar yadda tayi tunani kuwa dukkan su suna nan ana hira kamar kullum, "Mama na sarkin aiki badai har an kammala abincin ba?" Wani dadtijo ya fad'a yana kallan ta da murmushi me cike da so da kauna, "Eh Abba na gama shiyasa nazo na kira ku." "Har kin gama fa kika ce Halima?" Mama ta tambaya cike da mamaki, sai da tayi yar dariya sannan tace, "Na gama tun dazu abinci Ku kadai yake jira." Tare suka mike gabadaya suka fito babban falon suka zazzauna akan dining table din mai kujera shida Halima ta fara serving din su kafin ta gama ta zauna ta fara ci itama, "Mama ina su Yaya Sadik?" Hafsat ta tambaya tana cin abinci, kafin Mama tayi magana dogayen samari biyu suka shigo falon da sallama suka karaso dining table din, "Shikenan ma gasu nan ai" Mama ta fad'a ba tare da ta kalle su ba, shiru wajan ya d'auka babu mai magana sai karar plates da cokula kad'ai ake ji Abba ne ya katse shirun da fad'in, "Mama na jiya me naji kina cewa kina so naki ya lalace?". Sai da ta had'iye abincin bakin ta sannan tace," Waya tace ta samu matsala nace Yaya Sadik ya canja min yak'i" ta fad'a cikin shagwab'ar da take yiwa Abban nata, murmushi Abba yayi yace,"Kada ki damu dan dai waya ni zan siya miki da kaina, wacce kike so?." "Galaxy S22" ta fad'a cikin fara'a da murna. "Kar ki damu Auta gobe in Na fita zan tawo miki da ita." "Nagode Abba Na Allah ya saka da alkhairi." "Amin Mama na."
"Abba nima ina son wayar" Hafsat ta fad'a tana tab'e fuska. Sai da ya juyo ya kalle ta kafin ya cigaba da cin abincin sa yace,"I think wayar ki ko two weeks batayi a hannun ki ba right?" "Yau kwana goma da siya." "Good, to sabuwar me za'a siya miki? Itama tata dan ta lalace ne kuma lokacin dana siya miki waccan ai ban siya mata ba ita."
Rau-rau tayi da ido tace,"Amma Abba ai nima...." "Enough Hafsat! Bazan siya miki ba" daga haka ya mike ya wuce sama bai ko waiwayi inda suke ba.
Kallan Yaya Sadik tayi ta kalli Yaya Khamis ta kalli fuskar Mama da take kallan ta sai kawai ta fashe da kuka ta mike a guje tayi d'aki, jikin Halima yayi sanyi itama sai kawai ta mik'e ba tare da ta gama cin abincin ba ta shige d'akin kusa da Wanda Hafsat ta shiga.

❤ZUCIYA CE❤Where stories live. Discover now