page 9&10

37 3 0
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

*Nana Halima*😎

*9&10*

Zaro manyan idon ta tayi cike da firgici da takaici tace,"Karuwa! Karuwa fa kace? Haleeman ce karuwa? K'anwa ta fa nake nufi wacce ta shige yanzu ba wata daban ba." Sai da yaja dogon tsaki tare da zabga mata harara yace,"K'anwar taki fa ita nake nufi, ko kina tunanin zan mata k'arya ne?." "A'a kada muzo nan fa gaskiya kada Na sake ji ka kira sister Na da karuwa me tayi na karuwanci?." Kallan up and down yayi mata tare da ta6e baki yace,"Shikenan ai tunda kin k'aryatani banga amfanin fad'a miki ba." "Daman babu abinda zaka fad'a min kuma kada ka sake kiran sister na da karuwa bana so pls." Wayar sa dake gefe ya d'auka tare da mik'ewa tsaye yace,"Okay, lokaci yana tafiya nikam na tafi" bai tsaya yaji me zata ce ba kawai ya fice daga falon sabida ko kad'an baya san ta cigaba da yi masa maganar Haleema dan ransa b'aci yake ba kad'an ba. Tsaki Hafsat taja cike da b'acin rai ta mik'e ta fad'a d'aki dan taji haushin abinda Fahad ya fad'a akan Haleema ba kadan ba. Haleema kuwa koda ta shiga d'aki a jikin wardrobe tana sauke ajiyar zuciya, sosai jikin ta yayi zuciyar ta na bugawa da sauri-sauri hawaye Na bin fuskar ta, zame tayi a wajan ta zauna ta had'a kai da guiwa tana kuka, _Mai yake shirin faruwa dani Haleema? Wacce irin Zuciya gare ni? Meyasa zan fad'a soyayyar Wanda zai auri Yaya ta? Ashe haka masoya suke ji in suka samu sab'ani? Meyasa Na damu da abinda Fahad yayi min? Wayyo Allah na, Allah ka kawo min sauki cikin lamaru na, Allah ka bani ikon cinye jarabawar da nake cikin ta_ abinda take ta maimaitawa kenan a zuciyar ta, zuciyar ta nayi mata zafi da k'una kamar ana zuba mata ruwan zafi ana tafasa zuciyar, sulalewa tayi ta kwanta a wajan tana cigaba da sauke ajiyar zuciya lokacin kad'an zazzab'i ya rufe ta jikin ta yana rawa kamar mazari hak'oran ta na had'uwa da juna.
Hafsat ce ta shigo d'akin da niyar bata hak'uri akan abinda Fahad yayi mata dan ita harga Allah ta manta da batun wata Aunty Salamatu, "Innalillahi, Haleema lafiya? Meya same ki?" Ta fad'a da sauri tana k'arasawa wajan cikin tashin hankali, jikin ta ta ta6a taji zafi zau da sauri ta mik'e ta fita bata ba sai gata itada Yaya Khamis zuwa lokacin numfashin ta ya fara sama kamar zai bar jikin ta, "Subahanallah Hafsat meya same ta haka?" Ya fad'a yana tsugunawa a kusa da ita, "Wallahi ban sani ba a haka na shigo Na same ta." D'ago ta yayi ya mik'ar da ita yadda jikin ta yake fitar da zafi shi kansa sai da ya tsorata ya kalli Hafsat da take kok'arin dauko mata takalimi yace, "Yauwa saka mata takalmi muje." Haleema kuwa tana jin duk abinda ake amma ji take kamar a mafarki idon ta a rufe ruf sabida biyu-biyu take gani kanta na juya mata,ko takalmin bata iya sakawa ba ya rik'o ta suka fito, tun kafin k'arasowar su ya danna remote din motar tayi k'ara alamun ta bud'e a hankali suke k'arasawa ya bude baya aka shigar da Haleema Hafsat ta zauna kusa da ita ya Shiga mazaunin driver ya kunna motar suka fice daga gidan, wani private hospital dake kusa dasu suka k'arasa aka shiga da ita da sauri, kati Hafsat ta kar6a Khamis dake rik'e da Haleema suka k'arasa Inda ake kwantar da mutane, dake a asibitin tayi practical babu Wanda bai Santa ba aka shiga bata taimakon gaggawa. Sai da aka jima kafin likitan da ya shiga da duba ta ya fito, "Dr me yake damun ta?" Hafsat ta tambaya hankali a tashe. Dr ya kalle ta ya d'auke kai yace,"Ina mijin ta?." Kallan Khamis Hafsat tayi ta kalli Dr kafin tayi magana Khamis yace,"Bata da aure fad'a mana me yake damun ta?". Ajiyar zuciya yayi likitan yace,"okay auren tane ya mutu kenan?." "An fad'a maka bata da aure bata ta6a aure ba ka fad'a mana abinda yake damun ta" Khamis ya fad'a a d'an fusace sabida ya fara 6ata masa rai, "Sister ku tana cikin wani condition na Heart attack ma'ana dai Sister din ku zuciyar ta tana gab da kamuwa da ciwo, sannan kuma tana d'auke da ciki da sati biyu." Wata irin guguwar tashin hankali da fad'uwar gaba ne suka ziyarci Hafsat nan take jikin ta ya soma rawa murya Na rawa tace, "Dr Haleema Muktar Sani fa muke magana, itafa yarinya ce she just 18yrs kuma bata da aure wallahi ta yaya zatayi ciki." "Ta yaya zan San ta yadda ta samu ciki? Daman ai basai kana da aure kake ciki ba ko? Forget about it akan condition din heart dinta ya kamata ku mayar da hankali ba wai cikin dake tare da ita ba wancan condition din yafi worst akan wannan sabida tana cikin hatsari yarinya kamar ta under 20 years ace ciwon zuciya Na k'okarin kamata ai da problems." Banda rawa babu abinda jikin Hafsat keyi so take tayi magana amma ta kasa sai bakin ta dake rawa, Khamis da tunda aka furta Kalmar ciki yaji kamar an dora masa wani dutse mai nauyi a kirji shi kansa hawayen yake so yayi amma ya kasa sai cize baki da yake yi sam baya fahimtar abinda Dr yake cewa, ganin kamar basa hankalin su ya saka Dr ya bar wajan dan yana da aiki da yawa baya tsaya yana tayi musu bayani basa ganewa ba.
Gefe Hafsat ta koma ta zauna dab'as a k'asa tana kuka sosai, shima Khamis waje ya samu ya zauna ya dafe kai kawai zuciyar sa nayi masa wani irin k'una, sai da suka kwashe over 30mints a wajan kowa da abinda yake tunani kamar an tsikari Khamis ya mik'e d'akin da aka kwantar da Haleema ya shiga a dai-dai lokacin da ta farka ta mik'e zaune hannun ta d'aya yana side din zuciyar ta hannun ta d'aya yana dafe da kanta, kafin ta d'ago kai taji saukar wani gigitattcen mari akan fuskar ta kafin ta dawo dai-dai wani ya sake sauka a fuskar ta tayi baya ta kanta ya daki karfen dake jikin gadon, kanta yayi kamar zai shake ta sai kuma ya fasa ya naushi iska hannun sa na rawa ya nuna ta amma ya kasa furta mata komai, Haleema kuwa zuwa lokacin ta kasa banbance me take ji sabida yadda marin ya shige ta ga ciwon da kanta yake mata ta lumshe ido sai hawaye dake sakkowa daga idon ta so take ta bud'e baki amma ta kasa, Yaya Sadik ne ya shigo d'aki ya kalli Khamis dake huci yace,"Haba Khamis da hankalin ka da tunanin ka me ya kaita aikata abinda kayi? Ka Bari ta samu lafiya mana Baka jin irin yadda take cikin hatsarin wancan ciwon ne? Ka dawo hankalin ka Malam." K'arasawa gaban gadon yayi ya kalle ta yace,"Haleema sannu ya jikin naki." Tana jin me yake cewa tana so ta amsa koda da gangar jikin tane amma ta kasa jin ta take kamar ba'a duniyar take ba, numfashi ya furzar ya fita bai jima ba suka dawo da likita yayi mata allurar bacci tare da d'aura mata ruwa, haka suka zauna a d'akin ko wanne ya zuba uban tagumi babu Wanda yake yiwa d'an uwan sa magana basu suka tashi a wajan ba sai da akayi kiran sallar magariba.
Har lokacin Haleema bacci take bata tashi ba, bayan sunyi sallar i'sha sun dawo sun zauna babu Wanda yake wa d'an uwan sa magana kowa da abinda yake ransa, Yaya Sadik ya kalli Hafsat da ta zubawa Haleema ido tana kallan ta kuma tana hawaye sai da ya sauke numfashi sannan yace,"Hafsat ki zauna ku kwana a nan in ta farka ki tabbatar kin kira mu ." jajayen idon ta ta d'ago ta kalle shi tace, "Ban tawo da waya ba na barta a gida." Hannu ya saka aljihu ta d'auko wata k'aramar waya kirar nokia ya bud'e bayan ta ya zare sim card guda d'aya ya mayar kan babbar wayar sa sannan ya rife k'aramar ya mika mata yace, "akwai layin glo na kan wannan da kuma kud'i a ciki ki tabbatar kin sanar damu duka abinda ake ciki." D'aga kai kawai ta iya yi sabida bata tunanin zata iya cewa wani abu, basu bar asibitin ba sai tara da rabi na dare har lokacin kuma bata farka ba.

❤ZUCIYA CE❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora