❤️ *ZUCIYA CE*❤️
*Nana Halima*😎
*13&14*
Babu Wanda ya iya rintsawa a cikin gidan kowa da nasa kalar tunanin har garin Allah ya waye, karfe bakwai da kwata Hajiya Gwaggo tayi dirar mikiya a cikin gidan babu Wanda yasan da ita sabida babu Wanda ya fito babban falo tana zaune ita kad'ai ta hakimce tana kallan tv, basu suka fito ba sai karfe tara shima Mama ce ta fito dan d'ora breakfast yanayin da suka kwana jiya ya saka ta makara, ganin Gwaggo a zaune ya saka tayi saurin dawowa Inda take tana fadin,"Hajiya Gwaggo sannu da zuwa, ban San kin shigo ba ai." Da fara'a ta kalli Mama tace, "Ai shigowar Sassafiya nayi kuna ciki kuna bacci." "Barka da safiya" Mama ta durkusa har k'asa ta gaishe ta, "Barkan ki, fatan mun same Ku lafiya, ya gajiyar tafiya kuma?." "Babu gajiya Gwaggo, amma ai da kin Shiga ciki kya zauna a nan ga sanyi." "Babu komai ai nan din ma yayi, ina Hafsatu da takwara ta?" ta fad'a tana fad'ad'a murmushin ta. Gaban Mama ya yanke ya fad'i jikin ta ya sake yin sanyi hawaye suka taru a idon ta dakyar ta iya furta, "Suna d'aki bacci suke" daga haka ta kasa cigaba da tsayawa a wajan ta fad'a kitchen tana hawaye. Kan Gwaggo ya d'aure ganin yadda yanayin ta ya canja lokaci d'aya nan ta sake tabbatar da lallai da Matsala a gidan daman jikin ta yana bata haka gashi kuma ta sake tabbatarwa yanzu, Hafsat ce ta fito fuska a kumbure abinka da farar fata ta koma ja musamman hancin ta da kumatun ta, kitchen ta nufa da niyar d'ora breakfast din itama ganin Gwaggo ya saka ta d'an saki fuska ta k'arasa ta zauna kusa da ita tare da fad'in, "Hajiya Gwaggo mutanen Cairo sannu da zuwa, ina kwana." "Lafiya lau, ya karatu?" Itama ta tambaya da fara'a a fuskar ta, "d'an kwantar da kanta tayi a kafadar Gwaggo tace, " Karatu Alhamdullillah, kun dawo lafiya?." "Lafiya qalau, me malama d'aga ni kar ki k'arasa ni kaga y'a da San jiki kamar mage, ina Takwara tane ita?." D'aga ta tayi a hankali maimakon ta bata amsa kawai sai ta fashe da kuka, "ke wai lafiya kuke a gidan nan? Daga tambaya sai kuka, fad'a min abinda yake faruwa Tun a yanayin Babar ki nasan da matsala meye? Meya samu Haleeman?". Sai da ta tsayar da kukan tace, " Abba ne yace kada ta sake shigo masa gida gashi bata da lafiya ciwon zuciya gare ta da taji abinda Abba ya fad'a a asibiti shine ta bar asibiti babu Wanda yasan Inda ta tafi yanzu" ta k'arasa tare da fashewa da sabon kuka.
Dafe kirji Gwaggo tayi tace, "Wanne irin yace kada ta sake shigo masa gida? Shi Muntarin ne ya fad'i hakan akan Haleema?" D'aga mata kai tayi cikin kuka, "Hadiza!" Gwaggo ta kira Mama cikin d'aga murya, da sauri Mama da take sauraron su ta goge hawayen ta fito tace, "Na'am Gwaggo gani." "Hau sama ki kira min Muntari yanzu nan." Bace komai ba ta juya ta saura sama ta tura kofar d'akin ta Shiga da sallama, amsawa yayi ba tare da ya d'ago ba yana zaune a gefen gado ya dafe kai da hannu biyu Kansa a k'asa, "Hajiya Gwaggo na k'asa Tun dazu tace ka sakko yanzu tana Neman ka" bata jira abinda zaice ba kawai ta fito dan harga Allah haushi yake bata, fad'uwar gaban Abba ta k'aru dan bai San yadda zasu kwashe da Gwaggo ba, jiki a sanyaye ya mike ya fito tare da sakkowa, a hankali yake takawa kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki ya k'araso kusa da Gwaggo ya durkusa yace, "Barka da safiya." Kallan fuskar sa tayi da take cikin farin glass tace,"Shiga d'akin Takwara ta ka kira min ita yanzu." Jin hakan ya sake sunkuyar da kai yayi shiru ba tare da ya amsa ba, "ba magana nake maka ba?." "Kiyi hakuri" ya fad'a can k'asan mak'oshi. "Hakuri kan me? Nace ka tashi kawai ka kirawo min ita." "Kiyi hakuri Gwaggo tsautsayi ne na yanke hukunci cikin fushi gashi yanzu ina dana sani dan ..." Saurin katse shi tayi da hanyar fad'in, "Kenan abinda aka fad'a min gaskiya ne kenan ko? Kai yanzu in ma da gaske ne Haleema tayi ciki sai ka Kore ta? Baka yadda da qaddara ba kenan ko? Balle ma wallahi ban yadda Haleema zata iya ciki ba amma ka kore ta harda fad'awa yaran ka in aka Sanar damu baka yafe musu ba itama kace taje wajan wani naka baka yafe mata ba, kai game yara ko? Kana ganin ka isa dasu ai." "Kiyi hakuri sharrin shaidan ne wallahi kwana nayi ina tunani jiya ko runtsawa ban iya yi ba." "Yadda kake ganin ka isa da yaran ka kake ganin ko wanne irin baki kayi musu zai bisu nima haka na isa da kai ko wanne baki nayi maka zai bika dan haka na Baka nan da dare duk Inda Haleema take ka nemo ta ta dawo in ba haka ba kada ka sake kallo na matsayin mahaifiyar ka".
A razane ya d'ago ya kalle ta zaiyi magana tayi saurin d'aga masa hannu tace,"Kaje ka fara neman ta dan maganar ka baza ta amfane ka da komai ba, Hafsatu kiran min Baban yaya yazo mu koma gida." Babu yadda Abba ya iya haka ya mike ya koma sama yana tunanin ta Inda zai fara neman Haleema. Breakfast din da ba'a Dora ba kenan kowa jiki ya sake mutuwa sabida hukuncin da Gwaggo ta yanke akan Abba koda Yaya Shamsu yazo fad'a sosai ya dinga yiwa Abba kamar zai dake ransa ya baci shima ya goyawa Gwaggo baya akan hukuncin da ta yanke, saura y'an uwan sa duk da suka ji labari hakan suka ce shine dai-dai hukuncin da Gwaggo ta yanke Wanda yake bin Abba Wanda yake yawan tafiye-tafiye dan a lokacin ma yana garin Katsina wato Adam ji yayi kamar ya dawo ya k'ara zuga Gwaggo sabida abinda yayan nasa yayi ya b'ata masa rai over.duniya tayiwa Abba zafi babu yadda ya iya haka ya d'auki mota ya Shiga zaga gari ko Allah zai saka ya ganta, in ya nufi gabas to Sadik zaiyi yamma Khamis yayi kudu Babban Yaya Wanda suke kira da Daddy yayi arewa duk cikin Neman Haleema.A 6angaren Haleema Tun daren jiya bata sake sanin Inda kanta yake ba sai safiya a hankali take bud'e ido har ta bud'e shi tsaf yana k'arewa Inda take kallo, fargaba da tsoro suka dirar mata ganin ta a cikin ciyayi a tsakiyar daji baka jin k'arar komai saina tsuntsaye sai kukan wata yarinya da yake tashi a hankali, "oga wannan kasar fa ta farka" wani gansamemen mutum da yake tsaye a bayan ta ya fad'a hannun sa d'auke da bindiga. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine abinda take maimaitawa a ranta da ta fahimci sace ta akayi kenan kidnapping dinta akayi, "kee tashi ki koma cikin y'an uwan ki" Wanda aka kira da Oga yazo wajan fuskar sa d'auke da facemask baki ga bakin glass a fuskar sa Baka gane ko fatar jikin sa sabida ko ina a kulle yake da bakin Abu,jikin tane ya soma rawa zuciyar ta ta Shiga harbawa da sauri da sauri dakyar ta iya mik'ewa amma ta kasa tsayawa sabida bala'in ciwon kan da yake damun ta haka ya koma ta zauna yana hawaye,tsaki ogan yayi ya cafki dantsen ta ya mikar da ita ya Shiga janta da karfin tsiya har suka k'arasa wani waje me d'auke da rumfar buhu, yara ne k'anana y'an kimanin shekara biyar wasu uku wasu bakwai wasu goma, gefe kuma y'an mata ne masu shekarun ta su kuma sun girme mata, cikin yaran suka saka ta sabida yadda take zare ido tana kallan y'an matan cike da tsoro,wata macece ta fito daga wata y'ar bukka itama fuskar ta a kunshe da facemask da glass hannun ta d'auke da wani tray na shinkafa da manja ko arzukin yaji ko magi ba ta nufo wajan da suke zaune, dungurar musu da abincin tayi tare da juyawa ta bar wajan, yaran ne suka matsa kawai suka fara cin abinci y'an matan cikin su kuma ko wacce ta zabga tagumi tana kallan su, ko wacce a cikin su yunwa take ji amma sun San in suka ci abincin yaran baza su samu ba su zasu iya jurewa yaran kuma baza su iya ba hakan ya saka ko wacce tayi shiru tare da tagumi suna kallan abincin, wata yarinya da take zaune kusa da Haleema da tun d'azu take kuka tana kiran Abba Haleema ta kalle ta cikin tausayawa ta rike hannun ta tace,"kije kici abincin kema." "A'a ni dai a kaini wajan Abba na." Kwantar da kanta yarinyar tayi a jikin Haleema tana kuka tana kuma rike ciki, ganin hakan ya saka Haleema ta matso ta k'araso wajan ta saka hannu ta d'ebo abincin ta kai bakin yarinyar, abin mamaki sai ta bud'e baki tana k'arba tana kuma kuka, sai da taci kamar loma biyar sannan ta kawar da kai tana kuka. Kwantar da ita ta sakeyi a jikin ta tana shafa kanta. K'arar kida ce ta cika wajan Haleema sai da ta toshe kunne sabida yadda k'arar speaker ta cika wajan gashi daji ne babu gida ko Kad'an sai kidan ya k'ara tashi sosai. Wakar jeoboy alcohol suka saka suka k'araso wajan a fusace suna kallan bakin kowa nan da nan suka fara bi dan akan rashin bin wakar a gaban su suka harbe wata. Haleema da take bakuwa a wajan duk sai ta rud'e ganin yadda suma na wajan suka rud'e suka d'au wak'ar kamar karatu, bin baki take kawai tana tunanin meye amfanin wakar da ake yi.
Kusa da wata budurwa mai kamar shekarun ta ta matsa kusa da kunnen ta tace,"Meye amfanin wannan kidan?." Itama kunnen ta ta matsa tace,"Sabida ki shagalaa da jin kid'a babu ke babu addu'a shiyasa suke sakawa." Jikin Haleema ya soma rawa tabbatarwa da tayi tabbas anyi kidnapping dinta yanzu wa za'a sanarwa, yarinyar da take kwance jikin ta sake rik'e ta tana kuka itama Haleeman kukan take na tausayin kanta.
*Borno.*A kwance take a jikin Mummy tana kuka Mummy na shafa kanta tana fad'in, "Kiyi hakuri Khadeeja zata fito lafiya insha Allah addu'a zakiyi mata ba ki zauna kina kuka ba." "Mummy Musleeha tana hannun su sunki su fad'i fad'ar nawa za'a bayar Mummy kada su kashe ta." "Baza su kashe ta ba insha Allah ki cigaba da yi mata addu'a zata dawo cikin koshin lafiya insha Allah."
Daddy dake tsaye ya sauke ajiyar zuciya yana jin tausayin Khadeeja har cikin ransa, "Daddy dan Allah kada Ku sanarda Fahad kun sanshi da tsanani yanzu sai yace sai an Sanar da y'an sanda kuma sunce in aka sanar dasu sai sun kashe ta" ta k'arasa tana hawaye. Numfashi ya sauke kawai ya fice daga gidan yana Allah wadai da wad'an nan kidnappers din a zuciyar sa.*****
"Bana ce maka kada ka sake zuwa Inda nake ba matsawar baka gano Inda Takwara ta take ba?." Share gumi Abba yayi ya sake durkusawa yace,"Gwaggo na duba ko ina wallahi bamu same ta ba karshe ta hanyar cctv din asibitin mun samu labarin ta." "To tana ina yanzu? Fad'i mana?." Khamis ne yayi karfin halin cewa,"Gwaggo lokacin da ta fito har ta kai karshen layin asibitin mun gani a camera amma daga nan bamu sake ganin ta ba sai labari muka samu daga mazauna unguwar duk da hanyar ta kasance shiru babu mutane amma kwantacen ta da mukayi da na kamnin ta da kayan jikin ta wani ya bamu tabbacin sace ta akayi." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na Shiga uku ni Haleema, yanzu kana nufin yan satar mutane sun sace ta ko kuma garkuwa akayi da ita?". Ajiyar zuciya Khamis yayi yace, " Shine abinda bamu sani ba, in sace ta akayi tabbas da wata manufa akayi hakan ko ayi mata fyad'e ko kuma ayi amfani da wani sassan jikin ta, in kuma garkuwa akayi da ita to zasu yo waya su fad'i abinda suke so a basu kudin fansa yanzu kawai addu'a ce tamu." "Hasbunallahu wa'ni'imal wakil, Allah ka Kare min jika ta Haleema Allah ka bata kariya dan danajar annabi Muhammad S.A.W."
Jikin Abba yayi sanyi ya goge hawayen da suka sakko masa zuciyar sa cike da dana sani.Billahillazi a kara yawan comments🤒🤒🤒
Comments and share.
YOU ARE READING
❤ZUCIYA CE❤
Fantasy"Abba gaskiya kana nuna banbanci tsakani na da Haleema kamar ba kai ka yafe ni ba." Kallan ta yayi cike da takaici yace,"Banbancin ki da Haleema kenan Hafsat baki da labadi ko kadan." ***** "Wayyo wai me nayiwa Haleema ne? Ta raba ni da Abba na yanz...