❤️ *ZUCIYA CE*❤️
*Nana Halima*😎
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📖*
*15&16*
Haka aka wuni a gidan Daddy jikin kowa a sanyaye dakyar aka samu Gwaggo tayi shiru ta daina kuka amma har lokacin ko kallan Abba tak'iyi sabida haushin abinda ya aikata shi kansa haushin Kansa yake ji in ya tuna.
A 6angaren Hafsat sosai ta shiga damuwa tana kewar y'ar uwar ta ko lectures ta kasa zuwa sabida yadda jikin ta yake a mace a haka Fahad ya kira jiki a sanyeye murya a dashe ta d'auka daga can 6angaren yace,"Hafsat wai lafiya kike cikin kwanakin nan?." Shiru tayi bata amsa masa ba sai da ta kwashe second 1,2,3 sannan tace,"Babu komai kawai bana jin dadi ne kuma ina kewar Haleema." Da sauri yace,"Ina Haleema ta tafi?." Sai da tayi jimm kana tace,"tayi tafiya ne zata dawo nan da wasu kwanaki, ya aikin naka? Ta fad'a dan ta kawar da zancen Haleema dan baza ta iya fad'a masa cewa Abba ne ya Kore ta ba, "Aiki Alhamdulillah Maiduguri ma nake so na lek'a end of dis week." "Allah ya kaimu lokacin." Ya amsa sa amin kafin tace,"Bara nayi sallah" daga haka bata jira me zaice ba kawai ta kashe wayar. Bin wayar yayi da kallo kafin ya sauke numfashi kome ya tuna sai kuma ya ja tsaki yace,"Ta 6ata wayon ta a haka kamar baza ta aika ta ba" a fusace ya mike ya fice daga d'akin gabad'aya.Washe gari.
A 6angaren Haleema a cikin daren shak'uwa sosai ta shiga tsakanin su da yarinyar da lokacin bata san sunan ta ba itama bata san nata ba, haka suka kwana a daji ga sanyi yadda yarinyar take rawar sanyi ga zazzabi a jikin ta ta dole Haleema ta kwance dankwalin kanta ta rufa mata ta zauna da hijjabin ita, gari yayi haske kowa yayi jugum-jugum ga yunwa da take addanabar su.
"Oga jiya an kawo kudin fansar yarinyar can." Ya fad'a yana nuna yarinyar dake jikin Haleema da hannu, kallan Inda yake nuns masa ogan yayi kafin yace,"Ka fad'a musu Inda zasu same ta?." "Eh na fada musu." Sai da yayi numfashi kana yace,"Ka dauke ta ka kaita Inda zasu zo dauke ta duk wacce aka kawo kudin ta ku sake ta." "To oga, amma waccan yarinyar mai hijjabin can har yanzu banji kayi magana a kanta ba." Sai da ya kalli Haleema ya cize lips din sa yace,"Zamu yi maganar ta anjima, yanzu kaje ka dauke wad'an can aje a San abinyi." A guje ya juya yana zuwa Inda su Haleema suke ya ja burki ya kalle ta da jajayen idon sa yace,"kee! Saki yarinyar nan." Sai da ta firgita sabida yadda ya d'aga murya babu yadda ta iya haka ta d'aga yarinyar daga jikin ta suka mike tsaye tare, hannu ya saka ya finciko yarinyar da take rike da dankwalin Haleema ta rike shi gam sabida sanyin da take ji, haka ya shiga Jan yarinyar tana juyowa tana kallan Haleema har suka b'acewa ganin ta, komawa tayi ta zauna jiki a sanyaye ta zabga uban tagumi tana tunanin yadda rayuwar ta zata kasance cikin wannan yanayi. "Ke!" Yadda aka ambata da karfin gaske ya saka ta firgita sosai tare da d'agowa ta kalli wanda ya kira ta da kee din, "Uban ki shine Muktar Sani gagarimin dan kasuwa Wanda yake zaune a unguwar Tudun yola, ki bamu number sa yanzu a kawo mana kudin fansa in ba haka ba kuma na kashe ki" ya fad'a yana harba bindiga sama, jikin ta ya dauki rawa tsoro ya cika ta rasa me zata furta ma sabida yadda ya firgita dashi, "ba magana nake miki sai na fasa miki kai zaki min magana" ya fad'a yana saita bindigar kan goshin ta, kara ta saki bakin ta na rawa tace,"Bani bace ni ba y'arsa bace, dan Allah kada ka kashe ni." "Kee ni zaki yiwa karya? Bake bace Yar lelen sa wacce yafi so kaf y'ayan sa ba?." "Bani bace ni ban sanshi bama." Da kallon mamaki kawai ya bita kafin yayi kwafa ya bar ta tana kuka. Yana Barin wajan wata daga cikin wanda suke hannu su ta matso kusa da Haleema ta dafa ta tace, "Kinga baiwar Allah tunda suka tambayi number gwara ki basu kawai a sanadin irin wannan gaddamar suka harbe wata a kan idon mu in ba so kike ki bakunci lahira ba gwara ki yi musu abinda suke so." Kuka Haleema take sosai harda shashshek'a ta d'an tsayar da kuka tace,"Bani bace wacce suke nema ni marainiya ce bani da kowa number wa zan basu? Sai dai su kashe ni din amma bani da number wanda zan bayar." Jinjina kai tayi ta matsa gefe kawai bata sake ce mata komai ba.
Tana zaunen nan tana kuka an fitar da yara da manya sama da mutum goma ya rage saura su uku daga ita sai wata ka'aramar yarinya sai kuma wata wacce zasuyi sa'anni, ita dai kallan ikon Allah kawai take tana addu'a a zuciyar ta duk da wakar da suke sakawa tana dauke mata hanakli.*BORNO.*
Kowa k'ank'ame ta suke kowa yana shafa fuskar ta cike da farin ciki babu kamar Mahmah ma da take k'ankame da Musleeha tana shafa kanta. "Yanzu ki kaita d'aki kiyi mata wanka taci abinci a bata magani sai ta kwanta." Kamar jira take ta kama hannun Musleeha suka shiga d'aki. Mummy ta sauke ajiyar zuciya tace,"Alhamdullilah Allah ya fito mana da Musleeha lafiya, Allah ya sake kare ta su kuma masu aikata hakan Allah ya tona musu asiri." Da Amin Daddy da sauran y'ayan ta suka amsa kafin su mike kowa ya fita.
Bayan wasu awanni Musleeha ta tashi ta fito sosai ta ware kamar ba ita ba hannu ta d'auke sa dankwalin Haleema ta zauna a jikin Mummy tace,"Mummy na kinga d'ankwalin Aunty na." Kallan Mummy tayi tace,"Aunyn ki kamar Yaya kenan?". "Aunty wacce muka hadu a Inda aka d'auke mu tana sona taita bani abinci ina kwanciya a cinyar ta." Kallan Mahmah Mummy tayi itama ita take kallo zata sake magana Mummy tace,"Kinga Musleeha maza kuje ga kanin ki Khalil can yana neman ki kuyi wasa" ajjiye dankwalin tayi ta fice a guje tana kwalla masa kira. Kallan Khadeeja Mummy tayi tace,"Kenan cikin kidnapper din ne wata take san Musleeha ko kuwa cikin wanda akayi kidnapping din ne?." "Mummy sai dai cikin kidnappers din wanda akayi kidnapping ina shi ina kula da wani shima yana ta kanta sai dai cikin Wanda suka sace ta din." Girgiza kai Mummy tayi ba tare da tace komai ba, Mahmah tace,"indai haka ne tabbas tazo da sauki na tabbata Musleeha zata gane ta duk Inda ta ganta kinga sai a kamata in yaso ta fito da saura ko a samu a rage iri a Nigeria. " "Amma kina ganin cikin wanda suka sace ta za'a samu mai tausayin harda ta taimaka mata?." "Mummy za'a samu mana ba tasan dangin ta na da kudi ba zata iya samun wani Abu ta hanyar soyayyar da ta nuna mata, ai kawai Auta nake jira ya dawo ta kwatanta mana kammnin ta a samo me zane ya zana ta." Girgiza kai Mummy kawai tayi tace, "To shikenan ai, yanzu dai ki shirya ki koma gida tunda anga musleehan." Bata ce komai ba kawai ta mike ta fad'a daki.******
A cikin awannin an fitar da kowa a wajan ya rage daga Haleema sai wannan wacce take sa'ar ta da alama ita bata da galihu kudin da suka nema an kasa samu, gabadayan su suka k'araso wajan suka kalli Haleema da d'ayar d'aya daga cikin su yace,"Dukkan su basu da amfani oga kawai a aika su." "A'a daya zamu aika d'aya mu barta zatayi mana amafani." "Amfanin me kenan?" Macen cikin su ta tambaya tana kallan Ogan, "Amfanin Amfana mana bakya ganin zubin tane" ya fad'a tare da zubawa Haleema ido, jin hakan ya saka suka yi dariyar mugunta banda macen sa ta had'e rai. Da kai Ogan yayi alama ba tare da bata lokaci ba ya harbi d'ayar a goshi ta fad'i a wajan matatciya, k'arar da Haleema ta saki ya saka su ka kalle ta yanke jiki tayi ta fad'i a wajan a sume.
*Gaskiya kin samu a duhu waye yayiwa Haleema ciki?🤔 Waye kuma yayi kidnapping din ta?😳 kenan haleema Yar iska ce? Wacece yarinyar da suke tare a Inda aka sace ta?* wannan shine tarin tambayoyin da nake karo dasu, ku kwantar da hankalin ku fan's komai zai bayyana nan bada jimawa ba ku cigaba da comments kawai.😊😊🤗
Comments and share.
YOU ARE READING
❤ZUCIYA CE❤
Fantasy"Abba gaskiya kana nuna banbanci tsakani na da Haleema kamar ba kai ka yafe ni ba." Kallan ta yayi cike da takaici yace,"Banbancin ki da Haleema kenan Hafsat baki da labadi ko kadan." ***** "Wayyo wai me nayiwa Haleema ne? Ta raba ni da Abba na yanz...