page 23&24

41 3 0
                                    

❤️ *ZUCIYA CE*❤️

*Nana Halima*🌚

_Hakika naji dadin ydda kuka nuna kulawar Ku a kaina, Alhamdullillah yanzu ya samu lafiya nagode da addu'oin ku Allah ya bar zumunci._

*23&24*

Jikin Mummy har rawa yake hankali a tashe suka fita daga gidan basu wuce ko ina ba sai asibiti a lokacin Fahad yana emergency ana bashi taimakon gaggawa, haka suka dinga safa da marwa a wajan har lokacin da Abba ya fito daga emergencyn yana sharce gumi jikin sa a sanyaye, "Abbah ya jikin Autan?" Daddy ya tambaya a rud'e, "an samu yanzu dai numfashin sa ya daidaita amma bai farfad'o ba har yanzu kuma ya samu karaya a hannun sa na dama sai kuma y'an ciwuka k'ananu amma yaji ciwo a kansa sosai"ya fad'a jiki a sanyaye yana sauke numfashi. Khadija da ta iso lokacin tace,"To Abbah zamu iya ganin sa yanzu?." "A'a gaskiya badai yanzu ba sai dai nan gaba." Cikin lokaci kad'an maganar accident din Fahad ya karad'e dangi cikin lokacin k'ankani an cika asibiti kowa yana masa fatan samun lafiya.

*******

"Ke Hafsat! Wai me yake damun kine cikin kwanakin nan haka?." A hankali ta mike daga kwancen da take ta zauna ta kalli Mama tace,"Babu komai har yanzu b'atan Haleema ne bai bar jiki na ba ina kewar ta sosai" ta karasa fada idon ta na cikowa da kwallah. "Addu'a zaki dinga mata Allah ya bata kariya a duk inda take amma bayan wannan akwai wani abun da yake damun ki na lura dake cikin kwanakin nan Baki da walwala kamar da." Dan jimmm tayi zuciyar ta na dukan tara-tara tace, "Babu komai Mama wannan ne kawai." "To ai shikenan Allah ya bayyana mana ita" ta amsa da amin Mama tace, "yanzu mahaifin Fahad ya kira Abban ku fahad ya samu hatsari akan hanyar sa ta zuwa Borno yanzu haka yana asibiti." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Mama amma dai da sauki ko?". Kallan ta tayi Na wani mintina tayi murmushi dan san da Hafsat take yiwa fahad yana bata mamaki tace,"yana asibiti dai bana ce miki da sauki ko babu ba tunda ba ganin sa nayi ba." "To Mama yaushe zamu je duba shi?." Zaro ido Mama tayi tace, "Hafsat maigurin zamu je?." Shiru tayi bata amsa ba ta sunkuyar da kai sai a lokacin taji kunyar zakewar da tayi, murmushi Mama tayi tare da girgiza kai tace,"Kiyi masa addu'a kawai Allah ya bashi lafiya in ma za'a je sai dai Abban Ku yaje ai" ta fada tare da mikewa ta fice daga d'akin.
Dafe kai Hafsat tayi cikin wani irin yanayi sosai take jin zuciyar ta Na harbawa kamar zata fito jingina tayi da gadon tana sauke numfashi ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Borno sosai hankalin ta ya tashi, wayar ta ta fara laluba har zata kira Fahad sai ya kuma ta tsaya tunowa da tayi yana kwance ta wurgar da wayar ta mike ta fito falo.a falon ta Tarar da yayyen ta maza zaune kusa da Mama ana tattauna maganar da aka saba tattaunawa kullum maganar Haleema, waje ta samu itama ta zauna tare da yin lokaci daya maganganun Aunty Salamtu suka fara dawo Mata jikin ta sake yin sanyi zuciyar ta Na fada mata ta fada musu abinda ya faru amma wata zuciyar tana hana ta fadar abinda take ranta, "yanzu Mama shikenan Haleema an rasa Inda take?" Sadik ya fada cikin nuna damuwa, "to ya zanyi Sadik addu'a muke mata Allah ya dawo mana da ita in muna da Rabon ganawa." Baice komai ba suka yi shiru kowa yana sake-sake sab'anin Hafsat da ta zagba uban tagumi tana kukan zuci.

Da daddare Abba yana zaune a falon sa yana dan cin abinci kamar baya so Dan tunda Haleema ta bar gidan aka daina cin abinci tare ya kuma daina cin abinci sai kadan-kadan,  Mama dake gefe ta kalle shi tace,"rashin cin abincin nan naka bazai haifar da d'a mai ido ba sai dai ya haifar maka da wani ciwon kuma Na daman addu'a zaka cigaba da yi insha Allah zamu ganta." "Ya zanyi ne Hadiza? Bani da nutsuwa da kwanciyar hankali a kullum cikin tunani da mafarkan Mama Na nake ina zan ganta? Anya zata yafe min kuskuren dana aikata mata? Dole Na kasa cin abinci in Na tuna ita a wanne hali take yanzu." "Nasan duk zaka ji haka amma Na fada maka babu abinda hakan zai haifar maka sai ciwo ka daure ka cigaba da addu'a Allah zai bayyana mana ita." "In kuma bata raye fa?" Ya tambaya tare da zubawa Mama ido, gaban tane yayi mummunar faduwa tayi saurin fadin, "tana Raye ma insha Allah ka daina wannan tunanin dan Allah." Ajiyar zuciya yayi maimakon ya cigaba da cin abincin sai kawai ya mike ya fada daki.Dafe kai Hafsat tayi cikin wani irin yanayi sosai take jin zuciyar ta Na harbawa kamar zata fito jingina tayi da gadon tana sauke numfashi ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Borno sosai hankalin ta ya tashi, wayar ta ta fara laluba har zata kira Fahad sai ya kuma ta tsaya tunowa da tayi yana kwance ta wurgar da wayar ta mike ta fito falo.a falon ta Tarar da yayyen ta maza zaune kusa da Mama ana tattauna maganar da aka saba tattaunawa kullum maganar Haleema, waje ta samu itama ta zauna tare da yin lokaci daya maganganun Aunty Salamtu suka fara dawo Mata jikin ta sake yin sanyi zuciyar ta Na fada mata ta fada musu abinda ya faru amma wata zuciyar tana hana ta fadar abinda take ranta, "yanzu Mama shikenan Haleema an rasa Inda take?" Sadik ya fada cikin nuna damuwa, "to ya zanyi Sadik addu'a muke mata Allah ya dawo mana da ita in muna da Rabon ganawa." Baice komai ba suka yi shiru kowa yana sake-sake sab'anin Hafsat da ta zagba uban tagumi tana kukan zuci.

❤ZUCIYA CE❤Onde histórias criam vida. Descubra agora