RUHI BIYU

24 1 0
                                    

Dare mahutar bawa in ji 'yan falsafa. Dare mai saka a manta da  wahala. Dare kayan rabbana a zuba da rana a kwasa da dare. Daga cikin tarin baiwa da ni'imar da buwayi jallalla ya yi wa dan'adam; ita ce  duk tsananin hunturu ake tsalawa a waje sarari kana cikin ɗaki kwance; a kan luntumemiyar katifa lullub'e da tattausan bargo. Saɓanin dabbobi waɗanda bazara da hunturu kai har ma da damana duk a kansu suke ƙarewa, Allah Gwani ba na koyo ba.

Ƙwance nake a kan tafkeken gadona lullub'e da bargo k'irar 'yan k'asar Libiya; na lafe a ciki tamkar magen da ke dakon abinci. Baccina nake sadidan cikin walwala da jin daɗi a irin yanayi na an kar da mutuwa an kuma adana ciwo. Mutsu-mutsu na shiga yi bayan na ja wani ɗan siririn tsaki; na fara shirin mik'ewa daga daddɗan baccin da nake sakamakon ma'adanar fitsarina da ta yi dam da ruwa ta na buƙatar ɗauki haɗi da barazanar yin bindiga muddin a ka ƙi cika umarninta. Cikin matuk'ar kasala da lalaci na mik'e tsaye domin tsiyayar da dattin da jinina ya tace. 

Hanyar bandaki na nufa,  bayan na zari wayata da ke ajiye a kan dirowar gefen gadona. Mahaskar wayar na kunna ina matse cinyoyina domin ka da abin da nake rik'ewa ya yo waje.

Motsi da kuma k'arar zubar ruwan da na ji a band'akin ne ya dakatar da ni; cikin yanayi mai d'auke da matuk'ar mamaki na kai hannuna ga masagalin k'ofa domin share wata tantama gam na ji k'ofar alamun an sakace daga ciki. Gumi ne ya fara karyo min daga kowace kafar gashina duk da d'arin da ake tafkawa.

Hankalina ya fara sama kasantuwar mafitsarata da ke niyar tarwatsewa ga kuma mugun tunanin da ke d'arsuwa a raina.
Yatsu huɗu na tanƙwashe haɗi da buga k'ofar duk da yak'ini da nake da shi, na ba ni da wani musharaki a cikin d'akin.

Shiru shi ne sak'on da ya biyo bayan k'wank'wasawar da nake, hakan ne ya ba ni zimmar tattara k'arfina waje guda domin wangale k'ofar da na haƙƙaƙewa raina; tsananin sanyin da a ke tafkawa ne ya sanyata cijewa sai dai a banza wai an taka leda.

Wata sa'ar na sake gwadawa ta k'ara murd'a masagalin k'ofar duk da na san ba za ta tab'a aiki ba, sab'anin d'azu a yanzun murd'awa d'aya na yi k'ofar ta hangame tamkar ita ta bud'e kanta.

Ban wani tsaya mamaki ba na kwashi k'afafuwana cikin hanzari na danna su cikin bayi ba tare da yi  ko tunanin kulle k'ofar ba. Sai bayan na sauke abin da marar tawa ta k'unsa ne wani mugun tunani ya d'arsu a raina. Fitilar wayata na saka ina daɗa haska band'akin tamkar an saka tsumma an goge ko'ina; babu alamun d'igon ruwan da na ji ya na zuba d'azu. A tunanina ni ce na yi sakacin barin famfo a kunne. Wurin makunnan lantarki na k'arasa domin k'ara wani hasken.

Kunna lantarkin da na yi, ya yi daidai da ƙarin wani abin al'ajabi, ruwa ne ya ɓalle tamkar ruwan ɗufana. Ƙasan banɗaki ya cika taf cikin daƙiƙu biyar hatta da baho, mazaunar kashi gurin alwala duk a cike su ke har ta kai ruwan ya fara silmiyowa ƙasa.

A matuƙar tsorace na fara ɗaga ƙafafuwana da niyar ficewa daga cikin banɗakin ruhina tamkar zai yo waje. Ƙiƙam na ji ƙafata ta tsaya cak na kasa gaba ko baya, ƙafata a karon farko ta bijirewa umarnin ƙwaƙwalwata na tafiya. Hankalina ya kusa barin gangar jikina sakamakon tafasasshen ruwan da na ji ya fara ƙona ƙafafuwana har tsakar kaina. Cikin rashin madafa na fara ihu haɗi da hauragiyar neman taimako domin yau fa rana ta kuɓcewa mazajen fama.

Ƙiris ya rage maliyar tafasasshen ruwan ya kawo min maƙoshi, na ji tsananin iska ya fara shigata. Wannan loton ma dai ruwan ya ƙara ƙafewa babu shi babu alamunsa.

Cikin hanzari na ƙara ɗaga ƙafafuwana da niyar ficewa a bin da idaniyar ganina ya hasko min ne ya dakatar da ni daga yunƙurin da nake na barin banɗakin. Jini ke malala ta ko'ina maimakon ruwa yau dai karon farko na yi sha'awar neman taimakon mahalicci sai dai harshena ya gaza ba ni haɗin kai, bugu da ƙari ma zuciyata ba ta san kalar addu'ar da a ke yi idan an afka ga wata musiba ba.

A miliyan na fice daga banɗakin, domin tsira daga sharrin cukurkuɗaɗɗen rikicin da ke faruwa a banɗakin. Haƙi nake tamkar wacce ta yi tsere da ƴar damisa.

Tamkar a tsakkkiyar rana haka ɗakin da na shigo shi cikin duhu ya koma. Wata mahaukaciyar iska mai kama da guguwa ce ta saɗaɗo zuwa ɗakin take komai na ɗakin ya hau juyawa; kai ka ce ƙaƙƙarfar iskar nan ta rita ke kaɗawa. Gefen gado na laluba da niyar zama domin zuwa yanzun na san ƙiris ya rage min ban ci da baka ba, tamkar wani kumbo haka gadon ya fara ta shi ya na juyi a tsakar ɗakin .

Runtse idanuwana na yi zuwa yanzu na fara marmarin Azara'ilu ya kawo min ziyara fiye da ganin wannan musibar. Cak! Komai ya tsaya da-ɗai-da duniya babu abin da ya faru. Wutar da ta kunna kanta ta mutu wani baƙin duhu ne ya mamaye haske. Kwanciya kawai na gyara a kan gadon wani tsananin zafi mai ratsa ɓargo ya shiga tsakar jini ne ya ziyarci ƙasusuwana; gumi ne ya shiga karyo min tamkar wacce a ka yi wa tsomen shayi. A kiɗime na miƙe da niyar kunna na'urar sanyaya ɗaki sai dai kafin yunƙurina bai kai ga kaiwa ga gaci  ba; a ka hankaɗo murfin ɗakin da  da ƙarfin tuwo tamkar aikin samudawan farko cikin wata ƙaƙƙarfar tafiya samfurin takun doki.

A wannan karon dai na aro ta sadaukan mazaje na samu na saƙa kalmar,"Waye?" Da kyar na samu damar wafta kalmar daga ƙasan maƙoshina.

"Ni ce?" Ƴar siririyar murya mai kama da ta yara ƴan shila ta amsawa tambayata.

Takun ne ya cigaba da ƙaruwa tamkar tafiyar zagaye duniya. Takun tafiyar ya dakata a daidai inda nake ɗofane a kan gado; kafin na samu damar wani yunƙuri wutar nefa ta ƙara kunna kanta.

Zumbur na miƙe a cikin wani mugun yanayi, wata halitta da ba zan taɓa mancewa da ita a doron duniya na yi arba da ita; ido cikin ido na ke kallon halittar hantar cikina na kaɗawa tamkar ƴaƴan cikina za su yo waje. Dukkanin abin da ya faru sharar fage ne a kan ganin wannan halittar da na yi ban san sanda wani fitsarin ya ƙara kawo min ziyarar bazata ba take na fara sakinsa raina a ɗimauce nake bin halittar da kallo cikin mawuyacin hali na ce...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 02, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RUHI BIYUWhere stories live. Discover now