*❤️ ZUCIYA CE*❤️
*Neat Lady*
*45&46*
"Sake maimaita abinda ka fad'a Fahad ban ji dakyau ba" Mummy ta fad'a tana matsowa kusa dashi, ganin yarda fuskar ta ta canja lokaci d'aya ya sa jikin sa yayi sanyi a hankali yace,"Mummy Na sake ta kuma ni nace ta nisance mu". Zuba masa ido kawai tayi sabida ta rasa wanne hukunci zata yanke masa sabida bacin rai, "Abbah da kai da Yaya kuyi sauri Ku bi hanya ko Allah zai saka ku ganta" ta fad'a hawayen takaici yana sakko mata ta dafe kai jiri Na d'aukar ta, da sauri suka k'araso suka rik'e ta ta zauna Abbah yayi saurin bata ruwa da yake ajjiye a kusa da ita gabadaya sun rud'e rabon da suga hawayen mahaifiyar su tun lokacin da Fahad yayi accident, da sauri shima ya k'araso da niyar rike tayi saurin d'aga masa hannu ya tsaya cak yana kallan ta mayar da hankalin ta ga sauran tana share hawayen ta, "Mummy dan Allah ki daina kuka ki fad'a mana abinda kike so mun miki alkawarin samo miki shi insha Allah". "Haleemah ita tayi silar daina zubar hawayen nan a lokacin da Fahad yake kwance babu lafiya, tunda ta shigo rayuwar mu hawayen nan ya k'afe k'aff ta tauye haqqin kanta ta zauna da Wanda bashi da banbanci da Mara hankali bata tab'a kawo min korafi a Kansa ba, ta d'auki cikin sa duk da rashin tunanin sa ta amince ba tare da tunanin makomar ta ba in ya dawo tunanin sa yau shine wannan butulun da ya kore ta ya kuma yi mata sakin wulaqanci, dan Allah kuje Ku nemo min ita Indai kuna so hawayen nan ya daina zuba kuje" ta k'arasa fad'a tana hawaye. Kamar jira suke suka mik'e suka fice aka bar Fahad a tsaye a wajan kamar an dasa shi ko motsin kirki bayayi wani irin zafi yake ji a zuciyar sa in ya kalli Mummy ya tuna akan sa take zubar da hawaye wannan dalilin ya sanya tsanar Haleema ta sake ninkuwa a zuciyar sa, juyawa yayi shima a hankali ta fita jiki a sanyaye ya rasa abinda yake masa dad'i.
Sun zaga gari sosai amma basu ga kai kama fa Haleema ba ko aiki basu samu sunje ba sabida basu dawo ba har bayan azahar yawo suke ko Allah zai saka a dace amma babu ita babu alamar ta.
Sai gab da la'asar suka dawo gidan Mummy Na ganin su ta mik'e ta tare su a bakin k'ofa tana fadin,"Ina Haleeman take? Kun nemo ta?". Kallan juna sukayi kafin Yaya yace,"Wallahi Mummy mun duba iya inda zamu iya amma bamu ga me kamar ta ba, amma mun bada cigiyar ta ko Allah zai saka a dace." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ina zanga yarinyar nan? Allah dan darajar ka ka bayyana min wannan baiwa taka cikin aminci." "Dan Allah ki daina kuka Mummy zamu ganta insha Allah ki kwantar da hankalin ki hawayen ki Na tayar mana da hankali sosai." "Me zanyi in ba kukan ba? Ya kuke so nayi? A wanne hali amanar da aka bani take? Ban Sani ba bani kuma da hanyar da zan sani kuma ace bazan yi kuka ba". " zamu nemo ta mu dawo miki da ita insha Allah. "
"Waza'a nemo?" Daddy ya shigo falon tana kallan su one by one, "sannu da zuwa Daddy" suka fad'a a tare banda Mummy da take goge hawaye, "bayani zakuti min wa za'a nemo?". " idan ka huta zamu sanar dakai komai Daddy ka samu ka zauna." Ba musu ya zauna ya kalli Mummy da take zaune bata ko motsa ba ya dawo da kallan sa da yaran nasa yace,"Ku nake saurare malamai." Tiryan-tiryan suka zayyane masa duk abinda yake faruwa basu b'oye ba Daddy hankalin sa ya tashi ya cire hula ya ajjiye yace, "Amanar da Na karb'a daga hannun kanin mahaifin ta nayi alqawarin rike ta shine Fahad yayi silar Barin ta gidan ba tare da an San inda ta nufa ba? Ina Fahad din yake yanzu?". " tun dazun ya fita har yanzu bai dawo ba." "Gashi k'anin mahaifin ta ya Sanar dani jikin mahaifin ta yayi tsanani akan rashin ganin ta gobe zai zo ya d'auke ta su je Kano yanzu in yazo me zance masa? Nace masa ta b'ata ko kuma ta gudu? Wai ta ya akayi aka bar ta bar gidan nan? Meye amfanin ma'aikatan gidan?" Cikin b'acin rai yake magana kamar su Abbah ne suka yi masa laifin. Shiru sukayi babu Wanda ya amsa Kansu a ƙasa dan basu San abinda zasu ce masa.
Daddy ya katse shirun da fad'in, "kuje Ku nemo min Fahad sannan a cigaba da zagayawa ko zaku samu Haleeman in ba'a ganta ba dukkan Ku da safe zamu dira a kano in Allah ya kaimu" yana gama fadar hakan kawai ya mike ya haura sama cike da damuwa.
Haka suka bazama yawo Neman Haleema amma babu ita babu dalilin ta har dare dole suka dawo gida aka siyi ticket din zuwa kano bayan Daddy ya sanar da Uncle basai yazo ba suna hanya su, mummy da Daddy ko kallan arzuki Fahad baya samu daga wajan su gwara ma Daddy amma Mummy ko gaisuwa bata amsawa a haka aka lokacin kwanciya bacci yayi.
ESTÁS LEYENDO
❤ZUCIYA CE❤
Fantasía"Abba gaskiya kana nuna banbanci tsakani na da Haleema kamar ba kai ka yafe ni ba." Kallan ta yayi cike da takaici yace,"Banbancin ki da Haleema kenan Hafsat baki da labadi ko kadan." ***** "Wayyo wai me nayiwa Haleema ne? Ta raba ni da Abba na yanz...