Page 1

12 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya samar da alƙalami, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga ango Aisha miji ga Kadija, Shugabanmu fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalen gidanShi.*

*Wannan littafi hakkin mallakar Kainuwa Writers Association ne, ba a yarda a juya shi ta kowacce siga ba ba tare da izinin kungiyar ba.*


*Shafi na ɗaya*

*Alƙalamin Muntasir Shehu✍️*

*G.R.A KANO*

Yammacin cike yake da sassanyar iska wacce ta ke zarce fatar jiki ta tafi har zuwa cikin ƙashi ta samar da daddaɗan yanayi ga jikin duk wanda ya rabauta da kasancewa cikin yanayin.

A wannan yammaci a daidai lokacin da duk wasu ma'aikatan gwamnati ko kuma 'yan kasuwa suke haramar komawa zuwa gidajensu, daidai lokacin motar Hajiya Amina ta faka a kafceciyar harabar gidan nata wacce ta kwashi sarari mai yawa da zai iya wadatar talakawa a ƙalla guda goma su gina matsugunnin da za su rayu har ƙarshen numfashi.

Ta fita daga motar a hankali cikin nutsuwa, ga duk wanda zai kalli allon fuskarta a lokacin, take zai karanto kwantacciyar damuwa da ta mamaye fuskar, wacce hakan ke nuna alamun zuciyarta ma a jagule take, tun da an ce labarin zuciya a tambayi fuska.

Kai tsaye ainahin ginin gidan ta nufa cikin takunta na isa, wanda duk tsanani ba ta iya raba kanta da shi, mukullin motar tata da ke riƙe a hannun hagunta ta ke karkaɗawa a hankali har ta isa ƙofar shiga falon.

Ta danna ƙaraurawar da ke aika sanarwar isowar baƙo daga waje. Yaranta biyu Shaheed da Shahuda da suke zaune a falon suna kallon tashoshin turawa a tauraron ɗan Adam suka ɗaga kai lokaci guda suka kalli bakin ƙofar.

Shaheed ya mayar da duban sa ga agogon da ke manne a bangon falon sannan ya dawo da kallon nasa ga Shahuda.

"Momy ce fa, je ki buɗe mata."

Shahuda ta miƙe ta je ta buɗe ƙofar.

"Momy! Ashe dai ke ɗin ce, yau kin dawo da wuri fa."

Hajiya Amina ta yi ƙoƙarin ƙawata fuskarta da murmushin ƙarfin hali.

"Haka ne my dear, yau mun samu sassaucin aiki ne."

Daidai lokacin Shaheed ya ƙaraso wurin shi ma, suka rungume ta kamar yadda ya zame mu su al'ada.

"Ya school ɗin naku? Ina fatan dai babu wata matsala."

"Babu matsalar komai Momy, idan ma akwai ai muna da ke a matsayin maganin dukkan damuwoyinmu." Cewar Shahuda.

Suka yi murmushi duka, sannan suka rankaya zuwa cikin falon.

Shaheed ya koma mazauninsa da ya tashi, yayin da ita kuma Shahuda ta nufi ɗakinta don dubar wayarta da ke caji.

"Hajara! Hajara!"

Hajiya Amina ta shiga ƙwala wa mai aikinta kira, a gaggauce Hajarar ta fito daga sashensu na masu aiki tana amsa kiran.

Bayan ta rusuna gaban Hajiyar ta umarce ta da ta shirya mata abinci a dinning.

Ta kai aƙalla mintuna goma tana juya cokali cikin haɗaɗɗen girkin da ke fitar da azabar ƙamshi amma ta kasa kai koda rabin loma ne bakinta, da gaske take jin damuwa na yi wa zuciyarta luguden duka, yayin da ƙwaƙwalwarta ta toshe tsaf ta kasa samar mata da zaruruwan tunanin da za ta saƙa. Wannan yanayi da take ciki shi ya haifar wa da jikinta kasawa a kan duk wani aiki da jiki ke yi a kullum, ta ji sam ba ta son cin abincin gidan, komai ma na gidan ba ya burge ta.

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now