Page 2

1 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na biyu*

 
*ALƘALAMIN HASSANA YAHAYA*
  _Maman Noor_

Kimanin shuɗewar awa guda ke nan da fitar Amna amso gishiri gidan Lantana, tun  Umma na baza idanun ganin dawowarta har ta fidda rai. Dole badan taso ba  haka ta sauke miyar, Ganin zata ɓatawa kanta lokaci a iska sanin ɗan banzan yawon da Amnah ke dashi ya sanyata  saurin tashi ta ɗauro  alwala, ta nufi  k'uryar ɗakinta da zumar  tada sallah sai dai yadda gabanta ke faman tsinkewa yana faɗuwa ya sanya ta tunani anya lafiya, kuwa a daddafe dai  ta idar da sallar  amma  zuciyarta kam babu  nutsuwa haka dai take tamkar ace ket ta zura a guje ga wani irin  dunkullewa da cikinta keyi waje ɗaya.

Shigowar Malam ne gidan da mamaki ya gama cikawa zuciya jin gidan nasa  shiru babu motsin Amnah da 'yan wake-wak'e da ta saba,wadda da zarar ya shigo gidan suke fara masa maraba, Zuciyarsa ce ke faɗa masa anya yau  Amnah nan tasa lafiya take. A hankali  ya ɗaga baki ya k'ira sunanta "Amnar Babanta lafiya kike yau ko dai ɗan masassaran nan ne  jiki da jini zo nan  ki karɓi yalon bello da goriba bakin naki ya washe  ". shiru yaji babu amsa ya sake maimaitawa a karo na biyu.

Umma  dake zaune   hannunta rik'e da carbi tana ja, duk da dai  jan kawai take  da zaka rutsata da bindiga kace ta faɗi abinda take cewa baza ta iya  faɗa maka ba,  da sauri ta fito tana faɗin  "Sannu da dawowa Malam! sam ban ji shigowarka ba, sai da ka kira Amah! tukunna wallahi Malam daga aikenta gidan Lantana ta amso min gishiri shike nan ta tafi yawon gantalewarta amma  bari na le'ka na gani ko wani aikin ta sanyata   kasan  Lantana da sa yara aikin tsiya babu zarar yaro ya shiga gidanta shi kenan ta samu na mora".
  a fusace Malam ɗin  ya dubi Umman da ke faman zuba  zance uwa an kuna sabuwar redio bakinsa har kumfa yake yace .

"Wai ke Ladidi sai yaushe ne zakiyi hankali,  ace mutum babu tunani. Na fahimci   kina da sakaci akan amanar da Allah ya ɗora miki na yarinyar nan,  gishiri-gishirin ma sai kin aika da dare nan rokonsa ana  tsula wannan ruwan ,yo ko ba'a ruwan dama can bakya tashi roke-roken nan naki na tsiya sai kinga magariba ta gabato lokacin da sheɗannu ke tsula tasu tsiyar sannan naki aiken ke tashi,  dan lalacewa ga bakinki babu alheri sai aukin tsine-tsine!da gantale-gantale ai shi ke nan kin kyauta tunda kin gantala wa duniya ita sai ki fita nemanta". Hakuri ta bawa Malam ɗin  ta nufi gidan Lantanar tun daga kofar zauran gidan ta fara   kwaɗawa Amnah kira har ta iso tsakar  gidan.

Lantana da ke fitowa   daga banɗaki hannunta rike da buta  jin kiran da   Umman ke faman yi ne  babu ji babu gani yasan yata fitowa bata gama abinda ya kai taba. A hanzarce   ta kalli Umman ta ce  "Maman Amnah shigo daga ciki mana  wace Amnah  ? ai ni rabon da  nasa Amnah a idona  tun shekaran jiyan   da kika aikota na baki yajin daddawa ban kuma sanyata a ido na ba.".  Dafe k'irji Umman tayi ta jingina da bangon tsakar gidan ta shiga rera sallati da sallalami tana faɗin.

" Kina nufin bata zo nan gurinki amson gishirin ba ke nan? na shiga uku ni Ladidi to ina ta tafi  wannan gantalalliyar yarinyar ana tsuga ruwa nan  gidan uban wa zata dan barbaɗa".

Kallonta Lantana tayi ta ce.

"To ko gidan  Suwaiba uwar 'yan mata  ta shiga kinsan Suwaiba da tara  yaran mata a gidanta kinga muje gidan mu  gani ko can tayi dan fitina ana tsuga wannan ruwan kema da roke-roken ki, yo Allah na tuba ina mutum zai je  wallahi ki hanata shiga gidan nan dan kuwa ana zargin ita Suwaibar da 'yan shaye-shaye da neman mata ke an ce har saida tabar wiwi  take yi a wannan ɗan gidan nata mai kama da zuciyar talaka! muje dai mu gani ko can tayi.".

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now