*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________**Shafi na uku*
*ALƘALAMIN HUSSY SANI*
"Wayyo Allahna ku taimaka min ta kashe min ɗiya!"
Kururuwar da ke fitowa ke nan daga wani gida mai ƙaramar katanga, mata sun yi dafifi cikin gidan wasu kuma basu samu wuri ba sai a bakin ƙofar shiga gidan suka tsaya suna leƙen cikin gidan, wasu kuma ta katangar suke kallon abin da ke faruwa tsakar gidan.
"Wallahi yau wannan mayyar matar sai na kasheta sai dai ni ma a kasheni."
Wata mata ta faɗa cikin kuka sai faman jijjiga wata yarinya da ba ta ma san a wacce duniyar ta ke ba.
"Kar ki yarda Maman Nusaiba dan kowa yasan mayya ce."
Wata mata da ke tsaye kusa da Maman Nusaiba ta faɗa.
"Maman Khalifa yanzu mafita ya kamata a nema dan wallahi in aka kyaleta ta kashe banza kenan."
Wadda aka kira da Maman Khalifa ta kalli Maman Nusaiba da har yanzu take ta gunjin kuka ta ce,"Wallahi Maman Nusaiba karki yarda a kashe maki ɗiya a banza ki tashi mu raka ki gidanta, Maman Asiya ai za ki rakamu koh?"
Maman Khalifa ta juya akalar maganarta wurin tambayar matar da ta yi magana ɗazun wadda suke kira Maman Khalifa.
"I ku yi sauri mu isketa gida kafin ta fita."
Maman Khalifa ta faɗa tare da isa in da Maman Nusaiba ta ke rungume da ɗiyarta, taimaka mata ta yi ta miƙe tsaye ko abaya ba ta tsaya ɗauka ba suka nufi hanyar waje, hanya mutane su kai ta darewa suna buɗa masu har sai da suka isa ƙofar gida, gaba suka yi nan fa mutane suka bisu a baya zuga guda tamkar gaba ɗaya mutanen ƙauyen ne suka taru nan, gasu nan da yawa manya da yara.
Ƙofar wani ruguzajjen gida suka ci burki, da ƙafa Maman Khalifa ta bugi ƙyauren langa-langar da ke maƙale a jikin ruɓaɓɓen bangon, harbin da Maman Khalifa ta yi ma ƙyauren yasa shi lauyewa, cikin gidan suka ɗuru sai da suka cika gidan wasu suka tsaya a waje amma suna leƙen cikin gidan.
"Ina kike baƙar munafuka wallahi yau Mai daddawa sai dai ayi gawa biyu!"
Maman Khalifa ta faɗa cikin ɗaga murya, sakin tabarya Mai daddawa da ke daka ta yi tare da nufo inda su Maman Khalifa suke, gyara tsayuwa ta yi tare da fuskantarsu sosai ta riƙe ƙugu da hannu ɗaya ta turo kallabi gaba ta ce,"Ki man bayani yanda zan fahimceki malama me kike nufi da gawa biyu za a yi?"
"Ku ji man rainin wayau kina magana kamar ba ki gane me na ke nufi ba."
Maman Khalifa ta faɗa tana kai mata bangaza ga kafaɗa.
"Wallahi yau idan har ba ki saki kurwar wannan ɗiyar ba tabbas ke ma sai kin ƙwana lahira."
Wata murya ta daki dodon kunnuwansu.
"Faɗa mata dai Ɗan Marka dole yau ta saki wannan yarinyar."
Maman Khalifa ta sake faɗi tare da anshe yarinyar da ke hannun Maman Nusaiba, gaban matar ta je ta aje yarinyar ta ce,"Ga yarinyar nan ki tabbatar da kin sakar mata kurwa."
"Wai me kike nufi bangane na sakar mata kurwa ba kina nufin ni mayya ce ko me?"
Mai daddawa ta faɗa tare da binsu da kallo.
"Abin da na ke nufi kenan dan haka ki sakar mana kurwar ɗiya..."
Tsallen da Mai daddawa ta yi ne ya hana Maman Khalifa ƙarasa maganar da ta yi niyyar faɗa, gaban Maman Khalifa Mai daddawa ta dira tare da matsowa kusa da Maman Khalifa ta cakumi wuyan rigarta ta ce,"Wallahi yau sai na maki bugun da za ki kasa fita daga gidan nan har ni za ki kira da mayya?"
Ita ma Maman Khalifa cakumar wuyan Mai daddawa ta yi ta ce,"Na ce maki mayyar ƙarya aka maki ne ko me..."
Saukar marin da Maman Khalifa ta ji akan fuskarta ne ya hana ta ƙarasa maganar da ta yi niyyar faɗi, nan fa rigima ta kaure a tsakanin Maman Khalifa da Mai daddawa, ganin Mai daddawa na niyyar cin galaba akan Maman Khalifa yasa mutanen da ke wurin rufe Mai daddawa da bugu, sai da aka mata lilis kafin su barta nan yashe.
Duk da halin da take ciki sai da suka ɗagata sama suka tsallaka ta akan yarinyar nan take yarinyar ta miƙe tamkar wadda ta tashi daga bacci, ihu aka ɗauka na murna ganin yarinyar ta tashi, babu ɓata lokaci Maman Nusaiba ta kama hannun ɗiyarta cikin jin daɗi, fita suka yi daga gidan nan fa nan fa kowa ya watse, cikin lokaci ƙanƙane magana ta watsu a cikin ƙauyen duk da rashin yawaitar gidaje amma kasancewar gidajen duk irin gidajen gandu ne yasa nan take magana ta haɗe gari, duk gidan da ka shiga magana ɗaya ake nanatawa.
Bayan sallar magrib wata mata ta sha doguwar abaya tafiya ta ke amma sai waige-waige ta ke yi kamar tana tsoron wani ya bi bayanta, wuf ta afka gidan Mai daddawa, kwance a tsakar gida ta iske Mai daddawa inda su Maman Khalifa suka yasar da ita har lokacin nan take kwance ta kasa tashi, kafaɗun Mai daddawa matar ta kama ta zaunar da ita zaune ganin ba ta iya zama yasa matar shiga ɗakinta ta ɗauko tabarma da matashin kai ta fito, shimfiɗa mata ta yi da ƙyar ta ja Mai daddawa (kasancewarta mace mai ƙiba)ta kaita kan tabarma sai uban nishi matar ke yi, wurin robobin ruwa matar ta je ta haɗa mata ruwan wanka ta zo ta kamata ta kai ta har banɗaki, fitowa ta yi ta bata waje dan ta yi wankan, abincin da ta shigo da shi ta ɗauko ta aje kan tabarmar da Mai daddawa ta tashi, babu daɗewa Mai daddawa ta fito tana dafa bango, kaya matar ta miƙa mata babu musu ta canja na jikinta, zama ta yi jikinta sai ciwo yake mata, matar ta tura mata ƙwanon abinci a gabanta, ɗagowa ta yi ta kalli matar cikin disashewar murya ta ce,"Nagode ƙwarai Tani da taimakon da ki kai man."
Murmushi Tani ta yi ta ce,"Kar ki damu Mai daddawa duk yi wa kai ne, yanzu dai ki ci abinci mu yi magana."
Matar ta faɗa tare da gyara zaman zanen da ta lulluɓa.
"Yanzu Tani ban yi tunanin a irin abin da ya faru dani yau akwai wanda zai iya taimako na ba."
Mai daddawa ta faɗa tare da share hawayen fuskarta da gefen zanenta, dafa kafaɗarta Tani ta yi ta ce,"Gaskiya Mai daddawa na yi mamaki da na ji abin da ya faru a yau wai kina maita duba da duk iyayenki haifaffun garin nan ne."
"Tsautsayi da ƙaddara yasa ni siyan maita Tani ga shi tun kafin aje ko ina na fara shan azaba."
Mai daddawa ta faɗa tana share hawayen fuskarta.
Murmushi Tani ta yi ta ce,"Yanzu wa ne mataki kika shirya ɗauka akan abin da ya faru yau sanin kanki ne yawo garin nan dai ba zai yiwu a gareki ba dan ina tsoron ma Maigari ya kore ki a garin nan dan kin san ba kirki gare shi ba."
Tani ta faɗa tana ƙara muskutawa dan ta ji daɗin zama.
"Na dai fara tunanin na kai ƙara gidan Maigari na ce sharri su kai man."
Inji Mai daddawa tana maganar tare da zubama Tani idanuwa.
"Kul karki sake ki aikata wannan ɗanyen aikin dan wancan Maigarin bai da mutunci ana iya allura ta tono galma, dan haka zo na faɗa maki matakin da zamu ɗauka wanda za ki ci-gaba da walwalarki a cikin garin nan babu wanda ya isa ya nuna ki da yatsa."
Tani ta faɗa tare da yin murmushi, ƙara matsowa kusa da Tani mai daddawa ta yi ta ce,"Da gaske kike Tani darajata za ta dawo a idon mutanen garin nan."
"Har ma fiye da ta farko Mai daddawa in dai za ki bani haɗin kai ke ba daraja ba har dukiya sai kin tara a garin nan babu wanda zai taka ki in dai za ki bani haɗin kai."
Tani ta faɗa tare da jawo ƙwanon abincin ɗazun ta tura gaban Mai daddawa.
"Faɗi duk abin da kike so zan maki in dai zan samu duk abin da kika lissafa Tani."
Mai daddawa ta faɗa tare da riƙo hannun Tani.
"Kar ki damu yanzu dai gama cin abincin na raka ki inda za a maido maki da duk abin da na lissafa maki."
Tani ta faɗa tare da zare hannunwanta daga cikin hannun Mai daddawa, miƙewa tsaye Mai daddawa ta yi duk da gajiya da ke damunta ta ce,"Tashi mu tafi ban ga ta zama ba dan ina gudun abin da zai je ya dawo cikin daren nan."
Babu musu Tani ta miƙe, katangar baya suka kama suka dire, kasancewar gidan Mai daddawa a ƙarshen gari ya ke yasa basu haɗu da kowa ba kawai sai suka nausa cikin daji.
YOU ARE READING
Hannu ɗaya
ActionHannu ɗaya littafi ne da yake ɗauke da abuuwa masu yawa, kama daga fyade siyasa,maita,maɗigo,tsubbu,jinnu ku dai karku bari a baku labari.