Page 4

0 1 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na huɗu*

*Alƙalamin Rasheedat Usman*
           Ummu Nasma

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Me ya samu baban Zaliha, Allah dai ya sa ba mutuwa ya yi ba?"
  Ta yi Maganar a gigice idanunta na ƙoƙarin zubar da hawaye, ɗaya daga cikin mutumin da suka ɗauko sa ne ya ce,
    "Wallahi a nan kwanar gidan naku muka hango sa haka kawai ya yanki jiki ya faɗi, ki ɗan bamu ruwa mu yayyafa masa mu gani ko Allah Zai sa ya farfaɗo."
  Da sauri Inna ta juya ta je ta ɗebo ruwa a buta ta miƙa musu, amsa suka yi suka yayyafa masa wani irin ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa yana wani irin numfashi mai wahalar fita.
    "Alhamdulillah! dan Allah ku kama min shi mu shiga dashi cikin gida."
   Babu wata jayayya suka kamasa, har uwar ɗaka suka kaisa, tare da masa Allah yabasa sauƙi, Sosai Inna tayi godiya bayan sun tafi ne ta dubi Khadija da Mansur dake tsaye akan Baban nasu tace.
    "Maza kije ki haɗa muku garin, A'isha naga yunwa takeji."
  Da to ta amsa tare da barin wajen ta nufi madafin, cewa Mansur tayi.
    "Kai kuma kaje ka cire uniform ɗinka."
  Kansa ya girgiza tare da fita.
    "Baban Zaliha sannu, ba dai abinda yake damunka yanzu ko.?"
   Kansa ya ɗaga mata cikin sanyin murya da damuwa yace.
   "Maman zaliha kema kinsan bana cikin kwanciyar hankali kam, ji nake tamkar rayuwata tazo ƙarshe damuwa tana neman kasheni, damuwar halin da Zaliha take ciki shine kullum yake tsinka min zuciyata, mtsss! Ban sani ba ta mutu ko tana raye wannan shi yake ɗaga min hankali Maman Zaliha, ga damuwar babu da yunwar dake damun yaran nan ji nake na gaza kare iyalina bana son su shiga wani hali saboda gazawata, yunwa masifa ce tana sawa yaro yayi sata ko ya shiga wani mungun hali bana son hakan ta faru da ƴaƴana, ni kaina yanzu haka yunwa ke damuna ga yaran nan basu ci ba kinga ai dole zan shiga cikin damuwa."
  Numfashi Maman Zaliha ta sauƙe itama tana cikin wannan tashin hankalin, sai dai ya zamo wajibi a gareta ta kwantarwa da Uban ƴaƴanta hankali domin kuwa tasan idan yana dashi babu abinda baya musu.
   "Baban Zaliha meyasa zaka saka damuwar da zata illata maka lafiyarka, Saboda wannan damuwar bazamu iya magancewa kanmu ba, Tabbas rashin sanin halin da Zaliha take ciki babbar barazana ce a garemu sai dai ya zamuyi dole zamuyi hkr mu cigaba da mata addu'a, Allah ya ƙwato mana ita cikin ƙoshin lafiya, idan har muka shiga wani mummunan hali Saboda Zaliha ko ka mutu ta sanadiyyar wannan damuwar, ya rayuwar ƴan uwanta zai kasance kaine gatan mu bama son rasaka da kai muka dogara, suma yaran hankalinsu yana tashi idan suka ganka acikin tashin hankali, dan Allah ka nutsu ka sawa zuciyarka hkr, idan kana dashi babu abinda baka bamu, bazamu ji haushinka ba Saboda mun san baka dashi, ganan sauran kwakin da ka kawo mana shi zasu ci, akwai hamsin a wajena bara naje na bawa Mansur ya karɓo maka kunu a gidan Atine."
  Tunda ta fara Maganar yake kallonta cike da so da ƙauna domin kuwa matar rufin asiri ce, bata taɓa juya masa baya ba saboda bashi dashi, idan ta lura bashi dashi takan yi da aljihun ta muddun tana dashi, kullum burinta ta rufa masa asiri, tana ɓoye damuwarta domin ganin farin cikin sa, idanunsa ya runtse tare da cewa.
   "Shikenan Maman Zaliha, Allah ya bayyana mana ita ya yaye mana wannan talaucin dake damun mu, amma damuwa kam bazan iya daina ta ba har sai ubangiji ya kawo mana ƙarshen wannan Matsalar."
  Da ameen Maman Zaliha ta amsa tare da tashi taje ta bawa, Mansur kuɗi yaje ya sayowa Babansu kunu.

************************

Tun daga waje yake jiyo sautin dake tashi na music a cikin gidan, cike da masifa ya shigo, kunnen sa ya toshe jin yanda kiɗan ke tashi tamkar zai kurmantar da kunnuwa, Ɗakin Hafsa ya leƙa tana sanye da dogon wando wanda ya matseta ta sanya best duk rabin nononta a waje, ga ƙawayenta da suka cika ɗakin suma duk babu suturar kirki a jikinsu, sai rawa suke, gefen su ga wasu masu kama da tangalu sun saka shisha a gaba sai zuƙa suke, salati Kawu Ali ya ɗauka yana tafa hannayensa, tare da dosar su ya sanya hannu ya kashe kiɗan duk da kallo suka bisa, Hafsa cike da tsanarsa cikin rashin kunya tace.
   "Meye haka Kawu Ali akan me muna tsaka da jin daɗin mu zaka zo ka kashe mana kiɗa, ba gidan ka mukaje muka kunna ba, bare ka wulaƙanta mu."
  Tayi Maganar tana riƙe kunkumi.
  "iyye! Ai babu mamaki idan ma kika zageni Hafsa tunda baki samu tarbiyya ba, ƴar mace Kuma meye bazata aikata ba, kaf unguwar nan akwai lalatattun yara irinku ne kun zama fitsararru kun zamewa jama'ar unguwa masifa, daga ƴar iska sai ɓarawo sai kuma Ɗan shaye shaye, babu mutumin kirki a cikinku, kai wallahi Ubanku Tanko yayi asarar haihuwa dama ya sani da bai auri uwarku ba bare ku jawo masa tsinuwa yana kwance cikin kabarinsa, matsiyatan yara masu tarin abun kunya ku dai kunyi asara ku da uwarku da ta ɗaure muku gindi kuke iya shege."
  Yayi Maganar yana juyawa ya nufi ƙofar ɗakin Umman nasu yana kwaɗa mata kira     
    " Zainabu! Zaibabu"
Jin muryar Kawu Ali yasa Umma fitowa da sauri domin kuwa tasan zuwansa gidan ba alkairi bane tabbas wata Maganar yaran suka jawo mata.
    "Kawu Ali sannu da zuwa Allah yasa dai lafiya.?"
   "Ina lafiya kuwa Zainabu kin haifa mana masifa da annoba, ke dai Allah ya wadaran yaranki wallahi me za'ayi da irinki mungun iri anyi asarar haihuwa, gacan wancan tambaɗaɗen ɓarawon ɗan naki Babale, yana hannun hukuma yayi sata shine zai wani ambato sunana a matsayin ƙanin ubansa a kirani station ƴaƴana basu jawo min abun kunya ba sai naki, shine yanzu na shigo na samu wannan tambaɗaɗɗiyar ƴar taki, ta tara tsinannu karuwai ƴan uwanta suna famar shashaye sun cika gida da mungun sauti ke kuma kina ɗaki zaune kin zuba musu idanu suyi abinda suka ga dama nayi magana ta zageni, kai amma Saminu ya cucemu daya auroki ya haɗamu da mungun irinki, to gacan ɗanki ya je ya suncewa Amadu glass ɗin mota ya sayar an kamasa sai kije ki san yadda zakiyi ni babu ruwana ba hanuna bazanyi belin ɓarawo ba, kuɗina bana banza bane."
  Yayi Maganar yana juyawa zai bar wajen Hafsa cike da takaici tayo kansa tare da cewa.
   "Kowa yana da abun faɗa a gindinsa, namu kawai ake gani idan munyi karuwancin ina ruwanka ko kasan cinmu da shanmu ne waye yake saya mana magani idan mun cutu, shin kun taɓa tambayar mu damuwarmu tunda Abban mu ya rasu, ka amm..."
   "Hafsaaa! Karna kuma jin maganar ki duk lalacewar sa uba yake a gareki, kimin shuru."
  Umma ta dakatar da Hafsa cikin tsawa shuru Hafsa tayi tana huci, shi kuwa cewa yayi.
   "Meyasa zaki dakatar da ita tarbiyyar ki ai take gwadawa da kin barta ta ƙarisa matsiyaciya."
  Yayi Maganar yana saka kai ya fice daga cikin gidan.
  Umma runtse idanunta tayi hawaye masu zafi suka zubo daga idanunta wannan wacce irin masifa ce, ya zatayi da rayuwa, yau ko Naira biyar ɗin da zata musu abinci bata dashi, sai kuma gashi Babale ya jawo mata Magana ina zata samu kuɗin da zatayi belinsa tasan Amadu bazai yafe ba dole sai ta biyasa abunda Babale ya satar masa.
    "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ya Allah ka fitar dani acikin wannan jarabawar da nake ciki, Allah ka jarabceni da ƴaƴa, marassa jin magana ina iya bakin ƙoƙarina akansu sai dai basa gani, Allah ka shirya min su ka kawo min mafita a cikin rayuwata."
  Tayi addu'ar cike da ƙunar rai, hijabin ta ta ɗauka ta fita da niyyar zuwa police station ɗin da aka rufe Babale.
________________________

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now