Page 5

1 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na biyar*

*Alƙalamin Aisha Abdullahi Fulani*

Umma tana tsugunne bakin murhu tana fiffita wuta ta ƙi kamuwa sai hayaki take, "wutar damana a kwai wahala, duk 'yan dabaru na mata amma taki kamawa, mtsw!" Hafsat ta fito  ɗaki daga ita sai rigar bacci iya cinyarta tana miƙa, ta tsaya daga kofa tana doguwar hamma, ta nufi ƙofar fita Umma ta kalle ta fuskarta a ɗaure ta ce; "ke ina za ki je haka?"

Ta juyo tana kallon Umma cikin yatsina fuska ta ce; "zan nemo ɗan aiki ne ya sayo min indomie"

"Ba na son rashin hankali Hafsat  yanzu rashin kunyar taki har ta kai haka ki fita da gajerun kaya kamar na tsallakar wuta a cikin unguwa,  ki dawo ki zauna ga dumamin tuwon jiya nan da kuka bar ni da shi zan yi"

"Ke ma dai Umma kin san faɗa kike, tuwo ko na shinkafa ne ba zan iya ci ba ballatana tuwon gero" cikin takaici ta ce; "ki gode wa Allah da a ka dafa tuwon geron a gidanku, wasu ko geron ba su da, Hafsat ki ɗauki duniya a sannu, ke ba 'yar kowa ba amma kin sa wa kanki rayuwar ƙarya" Ta yi wa Umma shiru tana turo baki, Almajiri yayi bara ta kira shi ta aiki shi, yana tafiya ta shige ɗaki, Umma ta gyaɗa kai cikin damuwa ta furta, "Allah Ya shirya".

Umma ta samu wutar ta kama ta tashi tsaye ta ɗauki bokiti da hijab ɗinta za ta je ta ɗebo ruwa, ta jiyo Habu yana masifa daga cikin ɗakinsu gabanta ya faɗi "Hh Allah waɗannan yara kowa da tashi matsalar, ko me ya faru kuma?"

Ya fito yana zage-zage "wallahi ko a fito min da kuɗina  ko na yanka rashin mutunci a gidan nan!" Umma ta kalle shi cike da damuwa ta ce; "Habu kai da waye kuma?"

Cikin rashin kunya ya ce; "Da duk ɓerayin gidan nan nake, kawai na je na yi aiki tuƙuru na samu kuɗina dan nayi lalurata kawai a zo a ɗauke min dan an mayar dani ɗan iska!"  Hafsat ta fito  ɗaki ta tsaya daga ƙofa tana faɗin "kai ma dai ka san duk gidan nan babu mai halin ɓera sai Yaya Baballe, dan haka ka je ka neme shi, ka daina cika mana gida da hayaniya".

Ya yi cikinta kamar zai dake ta "ke zan ci uw... fa zan ɓaɓɓalla ki, ni sa'anki ne da za ki fito kina ɗaga min murya!" 
"Wallahi idan har giyar da ka sha ce take nuna maka hakan to gara tun wuri ka dawo a hayacinka, dan ba zan taɓa dakuwa a wajanka ba, sai dai mu daku!" Umma ta ajiye bokiti tana zubar da hawaye ta ce; "Me kuke so ku mayar da gidan nan ne, gidan dambe? Ko dai burinku kullum ku sa min baƙinciki" ta fashe da kuka,

Hafsat ta ce; "ke fa Umma kina da matsala magana kaɗan ya isa ya sa ki kuka, salon ki janyo mu shiga bakin duniya" Baballe ya shigo yana fito da waƙi-waƙinsa, Habu ya cakume wuyan rigarsa yana faɗin "ina kuɗina?"
"Malam cakani!"
  "Anƙi ɗin, bani kuɗina!"
"Wai kuɗinka na ɗauka, ni na ma san ka a jiye kuɗi ne!"
"Ƙarya ka ke ka sani dan ga shi ka ɗauka"
"an ɗauka ɗin ba kuma zan bayar ba kayi abinda za kayi!" Suka dinga dambe suna naushin juna, suna zage-zagen juna,  Umma tana kuka tana rabasu amma sam sunƙi dainawa, ƙiris ya rage Baballe ya kai mata naushe a baki  Hafsat ta janye ta tana faɗin  "Umma ina ke ina shiga cikinsu salon su ji maki ciwo a banza, ki  ƙyalesu su daku idan sun gaji da kansu za su ba kansu haƙuri, ai bari ba shegeya bace"

Zaman dirshin tayi a ƙasa tana kuka "shikenan so kuke baƙin cikin ku ya kasheni ba ranar Allah da za ta zo ba ku da sa min baƙin ciki a zuciyata ba, Allah na tuba ka ya fe min, idan har wani laifin na aikata da a ke jarabtata da yarannan"

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now