*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________**Shafi na shida*
'''Wannan shafin sadaukarwa ne ga masu yi mana sharhi, musamman Munaya, Maimunatu Omar, Asil, Ummu Araby, Amin Bash, Sadeeya da sauran su'''
'''Masu sharhi da guda-guda za ku ji sunayenku saman feji. Fatan alkairi ga kowa da kowa our fans, muna alfahari da ku irin sosai ɗin nan.'''*Alƙalamin Muntasir Shehu ✍️*
Da safe misalin ƙarfe takwas Hajiya Amina ta kammala shirinta tsaf na fita aiki, yadda ta tsara kwalliya sai a yi zaton taron fid da gwanar kyau ta duniya za ta je. Babu wanda zai kalle ta a karon farko ya amince ita ce ta fitar da su Shaheed daga jikinta, kullum ƙuruciya ce ke bayyana a jikinta.
Tana riƙe da makullin motarta a hannu ta nufi ɗakin Shaheed don duba shi kamar yadda ta saba.
Yana kwance ringingine a bisa luntsumemen kyakkyawan gadonsa, kafceciyar wayarsa tana hannunsa yana ta shafa ta yana zuba uban murmushi.
Da a ce wani zai yi katarin leƙa wayar don ya dubo abin da ke ƙawata zuciyar tashi yake wannan murmushi to da ya yi mummunan gani, domin kuwa irin shafukan yanar gizon nan ne da suke ɗora hotunan baɗala da na tsiraici shi yake kalla hankalinsa kwance.
Jin shigowar mutum ya sanya shi azamar juyawa ya kifa a gaggauce tare da tura wayar ƙarƙashin filo. Hajiya Amina na tsaye tana kallon yadda ya bi ya rikice, alamun rashin gaskiya ƙarara a tattare da shi.
'Tabbas wani abu yake aikatawa na rashin gaskiya.' Wani sashe na zuciyarta ya ba ta tabbaci, amma sai ta ƙi yarda hakan ya tasirantu a cikinta, cikin rashin ɗaukar hakan da muhimmanci ta ƙarasa gare shi tare da dafa ƙafaɗunsa.
"My dear lafiya kuwa?"
"Ƙalau Momi, me kika gani?"
"Na ga kamar kana aikata wani abu ne da ba ka so a gani."
Da murmushin yaƙe a fuskarsa ya yunƙura ya tashi zaune, "Momi kenan, babu wani abu da nake aikatawa... chat kawai nake yi da mates ɗina na school."
Ta ɗan yi shiru, duk da a ranta ba gamsu ba, amma ba ta jin za ta tsananta takura masa sai ta san abin da yake ɓoyewa, don haka ta saki zancen ta kama wani.
"Ƙarfe takwas yanzu har ta gota, na san kuma ba lallai ne ma in ka yi brush ba balle a kai ga maganar break fast."
Ya yi shiru cikin kai tunaninsa wani sashe daban.
Ta sake dafa shi, "Ka dinga ƙoƙartawa kana cin abinci a kan lokaci Son idan ba so kake ulcer ta yi maka mugun kamu ba, ni yau da wuri nake son fita ka ga kuwa babu lokacin da zan tsaya serving ɗinka, don haka ka tabbata ka tashi yanzu ka kimtsa ka je ka yi break."
"To mom." Cikin alamun nuna gajiyawa ya furta. Daga haka kuma bai ƙara ko motsi ba bare ta saka ran zai tashi, shi kuma jiran ta yake ta fice ya samu ya ɗauke wayarsa yana tsoron kar ya tafi ya bar wayar ta kunna ta ga abin da yake kalla.
Ta miƙe tsaye, ba ta tafi ba ta ɗan tsaya jim tana ƙara nazarin sa yayinda shi kuma yake jin kamar ya angiza ta ta bar ɗakin. Ta kaɗa kai ta fice.
A falo Shahuda ce ta harɗe kafafu a saman doguwar kujera tana aikin da ya zame mata al'ada wato chatting, a haka Hajiya Amina ta fito ta same ta.
YOU ARE READING
Hannu ɗaya
ActionHannu ɗaya littafi ne da yake ɗauke da abuuwa masu yawa, kama daga fyade siyasa,maita,maɗigo,tsubbu,jinnu ku dai karku bari a baku labari.