Page 7

2 0 0
                                    

*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)

*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Shafi na bakwai*

*Alƙalamin Zahra'u Abdul*
      Momyn Ahlan

Kwance take shame-shame duk jikinta yayi laushi duk wata gaba ta jikinta ciwo take mata, saboda yadda kartin maza bakwai suka taru su ka yi mata rubdugu wajen karbe budurcinta ba tare da tausayawa ba, ko tunanin ita budurwace sam wannan bai damesu ba kaca-kaca sukai mata, numfashinta kansa da kyar take fusgoshi, hawaye ya kafe a idonta sai kukan zuci. Ba wanda take tausayawa sai mahaifinta da mahaifiyarta wanda ta san tai bakwana dasu a halin yanzu domin basu da hanyar da zasu samu kudin da zasu kawo kudin fansarta, abincin da za suci gagararsu yake bare aje ga batun naira dubu dari biyar, gashi sun gama da ita sun gama kassara rayuwarta domin tasan rayuwarta ta gama lalacewa.

       Oga Gagare ne zaune yana nishadi da jin dadi domin rabonsa da samun mace zakwai irin wannan yarinyar har ya manta, duk wayanda ake kawowa duk yawanci dama sun san maza amma wannan ta musammance, babban yaronsa ne ya karaso hannunsa dauke da jakar kudin ya ajiye a gaban ogan nasu,
  "Oga iyayen yarinyar nan sun fa kawo kudin nace su jira za a mayar musu da ita kawai." Wani kallo Oga yabi Nanaso dashi ya sheke da dariya "hhhhhh Nanaso kenan ai wannan yarinyar tazo kenan domin kuwa tayi mun yadda raina yake so nida sauran yara, ta kashe mana kishin da muka dade muna jinsa dan haka wannan yarinyar wallahi ba za a maidata ba."
      "Hhhhhh sai Oga rabbu ya dafama Oga kai komai ba komai ba aljanna ta mai raboce hhhhhhh" Nanaso jikinsa yai sanyi kalau durkushewa yai akan gwiywarsa kawai zuciyarsa cike da tsananin rudani da tashin hankali, kallon Oga yake hankalinsa a matukar tashe da kyar ya iya bude baki yace "Oga baka kyauta ba wallahi tallahi, ba kai mana adalci ba, ba miyi haka da kai ba kasani, mun matsawa iyayen yarinyar nan sun kawo mana kudin nan amma ku lalatawa yarsu rayuwa wannan bai kamata ba." "Kai shashasha! kai zaka nunan abunda ya dace nayi ko yaya? To kul! karka kuskura karka fara wallahi muddin baka cire kanka daga wannan sabgarba zan batar da kai, bari kaji na gaya maka daga yau wannan yarinyar ta zama abun hutawarmu anan wajen, idan kana bukata kaima kaje kawai kayi." "Cau-cau Oga kai komai ba komai ba" gaba daya yaran suka hada baki suka fada.
   Mikewa yai cike da sanyin jikin ya nufi tantin nasu runtse idonsa yai saboda ganin irin rashin imanin da aka gwadawa wannan yarinyar, duk da dama babu imani a ransu amma shi sam a tsarinsa babu maganar fyade ya tsani fyade baya so, karasawa yai cikin halin tausayawa ya duka a gabanta zaninta dake yashe ya dauka ya rufa mata, ya fita domin baima san me zai mata ba bai san kalar taimakon da zai mata ba, yana fita daga tantin daidai lokacin da aka kawo wasu mutane mota guda mazansu da matansu, ciki ko harda matan manya da 'yammata hakan yai masa dadi dan ko ba komai zasu taimaka mata.
     Gurfanar dasu aka a gaban Oga wata dariya Oga yake yana karawa, "himma dai yarana! lallai yau aiki yai kyau dawa tayi nama haka nakeso ai daga gareku hhhhhhhh! Kuce yau akwai kwasar dabgen mata hhhhhh!" Gaba dayansu mazansu da matansu jikinsu karkarwa yake duk sun firgice domin kowannensu ratayake sa bindiga samfurin ak 47 da pistol a hannayen wasu, wani mutum Oga yasa aka fito dashi a gabansu daga cikin jama'ar dake wajen wanda ya dade a wajen, har yanzu yan uwansa basu kawo kudi ba dariya Oga yake yana binsu da kallo, duk jikinsu yai sanyi banda bari ba abunda jikinsu keyi.

     Zulaihat na kwance najin kukan mutane wani hawaye ke kara kwaranyo mata domin duk yayin da iska ta ratsata ji take tamkar ana watsa mata barkono a gabanta, kallon mutanen da aka kamo Oga yai cikin tsawa yace "kuu! Kunga wannan watansa daya da sati biyu a hannunmu yan uwansa basa kaunarsa sun gaji dashi dama, dan haka zan baku misali dashi yanzun nan duk wanda yan uwansa basu kawo kudi na rantse da sarkin dake busan numfashi sai dai uwarsa ta haifi wani bashi ba." Gaba daya jikin kowa bari yake har da Zulaihat dake kwance gaba daya jikinta rawa yake, wani tsoro ke shigarta domin tasan da cewa itama kasheta zasi duk da tafi bukatar mutuwar a yanzu amma tai matukar firgita, karar harbin bindigar da taji ya sata zabura ta fita waje da gudu duk wannan radadin ta dena jinsa, daidai kokon kansa ya saita ya harbeshi ya fadi matacce, wanda duk wayanda ke wajen sun saka ihu da kuka wasu sun rungume junansu.
     Tsawa ya daka musu wadda tasa suka dawo hankalinsu dukkansu ba wanda ma hankalinsa ya kai kan wata Zulaihat data fito tsirara haihuwar uwarta, duk wata azaba da take ji ta kau saboda tashin hankali ihun da ta saka shi ya maida hankalin kowa kanta, sunkuyar da kai aka fara tuni matan suka kuma rikicewa suna kuka saboda tsananin tashin hankali ganin halin da Zulaihat ke ciki, banda jini ba abunda ke sintiri a kafarta, wata mata ce tai karfin halin mikewa tai kanta ta lullubeta da mayafinta. "Keeee!" Wata uwar tsawa ya daka musu "uban waye ya baki izinin mikewa a yanzu? Ke kuma har kin warke kenan kin fito kice akwai na dare? ko da yake ga sababbi sunzo kuka suka kuma rushewa dashi matar ce ta rungume Zulaihat duk da gargadin da yai mata ta gwammaci ya kasheta da ganin wannan wulakancin.
     Kallonsu yai suna duke suna kuka "keeee ki bar wahalar da kanki da kuka domin kowa zai iya barin nan amma banda ke domin mun karbi kudi a hannun mahaifinki gasu nan, ya daga jakar ya nuna mata amma ba zamu taba sakin ki ba kisa a ranki kinzo kenan domin kin zama matata daga yau kisa wannan a ranki, kuma duk mai bukatarki a yarana zai yi yadda yaso dake dan haka kidena kuka kin zama yar cikinmu zama yanzu kika fara hhhhhhhh!" Saukar maganganunsa takeji tamkar saukar aradu kenan iyayenta sun kawo kudin a ina suka samu kenan? Jiri ne ya kwasheta idonta ya dinga gani dishi dishi luuu ta zube dif numfashinta ya dena aiki.

Hannu ɗayaWhere stories live. Discover now