*HANNU ƊAYA*
(Ba ya ɗaukar jinka)*Rubutun Haɗakar Marubutan Kainuwa*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________**Shafi na goma sha ɗaya*
*Alƙalamin Real Nana Aisha*
Wani ihu Kabiru ya saki bayan ya gama kirga kuɗin da Shuhuda ta ba shi a lokacin da ya dawo ɗakinsa daga wajen Talatu. Daɗi ya lulluɓe shi tamkar ya taka rawa sakamakon ganin da ya yi kuɗin suna da ɗan yawa, don za su kai kimanin nera dubu talatin. Bai samu damar kirga su ba tun a hanya sanadiyyar nutsuwar da ta gagare shi, yana fafukar neman yadda zai kawo wa Talatu magani, har cikin ya fita ba tare da 'yan gari sun kula da halin da take ciki ba musamman ma iyayensa da ya san kashinsa sai ya bushe a wajen su.
Sai bayan ya kai mata maganin ne hankalinsa ya dawo jikinsa, ya yi amfanin da fitilar salularsa raka-ni-masai wajen kirga kuɗin da tun ba shi su suke cikin aljihunsa.Ya kwashe lokaci mai tsayi yana saƙe-saƙe makomar kuɗin da kuma abin da zai yi da su ma'ana dai kasuwanci zai fara yi da su, inda daga ƙarshe ya yanke shawarar shiga gari ya saro lemo da rake don ana samun cinikin su sosai a ƙauye. Da haka ya kudiri aniyar safiya tana wayewa zai bar ƙauye zuwa cikin gari don da ma babban burinsa ya fara sana'a, musamman yadda ya ga birni mutane da yawa suna sana'a, ga kuma masu kuɗi da ya sha tozali da su a hanya cikin tanfatsa-tanfatsan motoci. Dalilin da ya sa tunaninsa ya tsaya a kan sana'a, don shi a ganinsa duk wani maikudi da ita ya fara har ya zama babban maikuɗi. Don haka shi ɗin ma tun da ya samu jari ya zama dole ya gwada sa'arsa don zai dace, da ma ya gaji da zuwa gona.
Sai juya kuɗin yake cikin farinciki yana faɗin,
"Allah Ya yi wa hajiya mai mota albarka, gaskiya tana da kirki. Daga ɗan buge ni da mota ko ciwo ban ji ba sai ba ni waɗannan damin kuɗi?"
Ya tsahirta haɗe da yin tagumi hannu bibbiyu kafin ya washe haƙoranshi ya ci gaba da cewa,"Yo ni gobe in na koma birni ma da zan samu mai sake yi min irin na yau ai da more, sai jarin nawa ya ƙara gwaɓi."
Ya faɗa yana sakin ihu tamkar zautacce. Daga nan ya ci gaba da zancen zucinshi, kuma in ta ciyo shi ya shiga magana a fili har zuwa lokacin da ya ji motsin Iro a ɗakin nasu sai a sannan ya yi saurin ɓoye kuɗin haɗe da yin baccin karya, har baccin gasken ya kwashe shi ba tare da ya ankara ba.Washegari ko da ya tashi bai ga Iro a ɗakinsu ba, a tunaninsa Iro ya tafi masallaci ne bai tashe shi ba don haka ba tare da tunanin komai a ransa ba ya yi alwala haɗe da zuwa masallaci, bayan ya dawo ya fara shirin tafiya birni, ba tare da kowa ya sani ba ya bi ta bayan gida haɗe da nufa kai tsaye tashar mota, bai jima sosai ba a tashar motarsu ta ɗaga sai cikin garin gari.
A cikin motar babu abin da yake yi sai tunanin ya kusa zama maikudi, saboda wannan sana'ar da zai fara. Har tunanin ga shi nan cikin mota yana tuƙawa, sai washe haƙora yake yi kamar sabon mahaukaci, ya sanya wa Talatu albarka ya fi cike da kwando a cewarshi silarta ne ya samu kudin da bai taɓa samu ba tun da yake. Don haka ya yi murna Sosai da zuwanshi birni don ga shi dai ya samu damin kuɗin da zai zama maikuɗin gaske silar su.
Mota tana sauke su kai tsaye a-daidaita-sahu ya hau ya nufi kasuwa*********
Buguzum-buguzum take tafiya kamar za ta tashi sama, ta ci ɗagama da mayafinta kamar mai shirin yin dambe, sai masifa take yi ita kaɗai kamar mahaukaciya. Fuskar nan tata ɗauke da fushi mai tsanani, kananun idanuwanta cike da kwamtso ba kyan gani, kafufuwanta fari kal kamar jaka, kasancewar tashinta daga bacci ke nan daga fuskar har ƙafafuwan nata babu wanda ya ga ruwa cikin su. Tana farkawa daga bacci ta fito tana ɗaure kugu babu salla ballatana salati. Cikin masifa ta shigo gidan baba Tukur tana faɗin,
YOU ARE READING
Hannu ɗaya
ActionHannu ɗaya littafi ne da yake ɗauke da abuuwa masu yawa, kama daga fyade siyasa,maita,maɗigo,tsubbu,jinnu ku dai karku bari a baku labari.