*MABARACIYAH*
_hakkin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
Free page
5••6A bakin office ɗinnasu ta ajiye mashin ɗinnata kafin ta shiga,kanta a sunkuye kana ganinta kaga gentle soul.
Office din shugabannasu ta nufah,kasancewar babu kowa a headquater sai iyah wanda aka kira su aikin yin binciken.
Ƙwanƙwasa ƙofar tayi amma kuma sai taji shuru,da alama bai iso ba kenan,ko kuma har yanzu suna wajen binciken,dan tun jiya ya ɗebi mazan suka tafi.
Ƙarar wayarta ne ya katseta da tunanin inda Dec sadeeq din yake,ɗauka tayi ta kara a kunnenta,
"Dec khamriyyah kina ina?"
"Sir ina bakin office ɗinka yanzu haka"
"Okay maza ki taho gidan Dr bukar muna can,akwai abinda nake so mu bincika,dan there is something odd about it"
"Clear sir gani nan"
Sauƙe wayar tayi tareda ɗan cija fatar bakinta,mai kuma aka samu da har Dec. Sadeeq ya ƙirata taje can,ba a nan zasu yi bunciken ba ne?
Kardai ya gano yanda aka sace Dr bukar ɗin,kai bazaiyiyu ya gane ba,kwarewarsa bata kai har haka ba tukunna,duk da yana ganin shine shugaba amma har yanzu bai kama yatsana ba,idan naga ya gano sanja takun salo zanyi.
Share tantamar dayake ranta tayi kafin ta nufi gidan Dr bukar ɗin.
Tun daga bakin gidan yan sanda sunyi dafifi a wajen,duk da kuwa gari bai gama wayewa sosai ba.
Mamaki abin ya bata ganin yan sandan ma harda masu babban matsayi,koda yake bawani abin mamaki bane kasacewarsa babban likita wanda ake ji dashi na ƙoda,da yake yawon buɗa ido akan aikinnasa a ƙasashe daban daban.
Karisawa wajen tayi ta nunawa wani a wajen ID card dinta,saida ya dan sara mata kafin yabata waje ta shige.
Cikin gidan ta shiga inda Dec sadeeq yake.
Duk wanda abin ya shafa musamman ma Ƴaƴan sa sai kuka suke suda matarsa,masu dauriyar cikinsu ne mazan sukayo jugum kaman masu kar'bar gaisuwa.
Kallo ɗaya khamriyyah tayi musu kafin ta karisa inda Dec. Sadeeq yake,
"Barka da safiya Sir"
"Sannunki da ƙokari,inasu Ahmad kuma ban ganki tareda suba,"
"shukurah tabada taakarda akan bata da lafiya"
Kukan ɗaya daga cikin yaranne yakara tsananta tacika wajen da kuka,ga mutane dayawa kama daga yan uwansa da kuma mutanensa.
Tashi khamriyyah tayi ta isa inda yarinyar take,ganin yanda yarinyar take kuka na rsshin mahaifinta ya sa wani dukan kirjin khamriyyan,saidai kuma ko kaɗan ta samu kanta da rashin nadamar abinda ta aikatawa ahalin.
Dafa kan yarinyar tayi mai shekaru goma,in tace bataji tausayin yarinyar bama tayi ƙaryah,duk da batasan wani abu ba wai shi soyayyar uba.
"Kiyi haƙuri kinji baby,dan kin rasa mahaifinki karki yarda zuciyarki ta karye,ki daure sannan ki tafiyar ta rayuwarki,ki kasance kullum cikin dauriya da kuma jarumta,babu wanda bazai iyah yin dauriya ba saidai in bai dage ba"
Ɗaga kai yarinyar tayi tareda yi mata ɗan karakin murmushi.
"Anty nima inason zama irinki,wacce take bada lokacinta wajen ƙoƙarin nemowa ahali dan uwansu idan ya bata"
"To shikenan amma kiyi tunani kafin sannan sosai kinji,dan ba komai ne kake ganinsa a ido kuma ace cikinsa haka yake ba,karkiyi abu dan kinga wani yayi,saboda mai yiyuwa dalilinsa nayin hakan daban kekuma bakida masaniya akai,menene sunanki?"
"Sunana Fadilah Bukar"
Rutse ido khamriyyah tayi lokacin da yarinyar ta ambaci sunan ta tareda karawa da sunan dr bukar ɗin,abin akwai takaici,saidai kuma haka allah yaso fitar da ita daga tsatsonsa,duk ita ɗin ta tsaneshi amma kuma uban tane ita.
Maganar Dec. Sadeeq ce ta katseta data ji yana cewa
"Dec. Khamriyyyah,inaga akwai wani abu gameda kidnapping dinnan,Hajiya Salah tace ganin shigowar wasu mutane tayi masu baƙaƙen kaya,daga nan kuma bata sake ganin komai ba sai tashi tayi da asuba taga ba mijinnata.
Sannan a katangar baya ta gidan akwai alamar shigowar mutane guda uku,sun diro cikin gidan,amma kuma babu alamar sun fita ta wajen.
Duk yanda akayi ta kofar gidan suka fita,kuma babu alamar an buge ƙofar gidan,hakan yana nuna da key ɗim ƙofar aka buɗe"
Dukkan su shuru sukayi suna kallonsa,idonsa yana kan khamriyyah dan yaji mai zatace,ɗaga girar ta tayi kafin ta ɗan waina idonta alamar tafiya tunani.
Dolene nayi wani abun kaman ko yaushe,nasan dama zai gano wanann ƙana nan evidence din,dan haka banyi mamaki ba ko kadan saidai abu ɗaya shi.......
"Dec. Khamriyyah naga kinyi shuru kaman mai tunani"
Gyaran murya tayi alamar dawo hankalinta kafin ta hango mai gadi wanda yake ɗan nesa dasu yana magana da wani ɗan sanda.
"Am baba mai gadi a yanda binciken ya tabbatar,an samu shaidun cewa masu aikin sace uban gidanka sun shigo gidanne ta katanga,duba ta yanda alamun durowarsu ta nuna,saidai kuma babu alamar sunyi amfani da hanyar har ila yau wajen fita.
To hakan yana nuna cewa ta bakin get suka bar gidan,kuma babu alamar sunyi amfani da karfi wajen bude kofar ko kuma makulli.
Kai in takaice maka bayani ma,zanen hannunka muka gani 'baro 'baro a jikin kofar.
Shin mai kake a daren jiyah da har kunnenka yakasa jiyowa ƙarar fitarsu da kuma shigowarsu,sannan ina kaje a lokacin da karfe kusan 12:00pm na dare,dan yadda abin ya nuna zanen hannuka yayi akallah awanni shida a jiki,ko kuma daukar makullin sukayi a wajenka suka bude,sanann kuma babu duka ko barazana ka dauka ka basu?idan ba haka ba shin da haɗin bakin ka a.........."
"Kiyi hakuri madam kimin rai,wlh ba haka bane yanda kike tsammani,ni ban haɗa baki da kowa ba hasalima bana wajen lokacin da suka zo ɗin.
Wata mata tazo gidanann a daidai lokacin da kuka ambata,na ganta da ciki da kuma tana cikin mawuyacin hali,shiyasa naga yakamata na taimaka mata"
Mamaki ne ya zagaye fuskar khamriyyah,wacce mata kuma yake nufi kuma da ciki sanann a duhun dare?
"Wace irin matace da tsakar dare zatazo neman taimako?"
"Nima Bansani ba madam,da farko naji tsoron taimakonta saikuma naga yanda take nishi daya bayan daya,hakanne yasa na taimaketa"
"Daga nan kuma sai ka bar kofar a bude kuma?, ko me?"
"Ahah tacemin tana bukatar ruwa,shiyasa natafi domin debo mata a fanfon baya,dan nawa ya baci,bayan na bata ne nayi kokarin ce mata ta zauna tunda tace ana biniyarta,saikuma tace wai akwai tashar mota gaba kadan zataje ta shiga"
Tun kafin khamriyyah tasake bude baki tayi masa magana Dec. Sadeeq ya matso kusada mai gadin tareda cewa,
"Shin akwai Ctv camera ne a gidannan?"
"Eh Akwai amma guda biyuce kawai,daga ta bakin get din sai kuma ta wajen motoci"
"Nuna min nagani yanzu"
Hanyar wajen dakinsa yayi su khamriyyah na biyeda shi har dakin da suke.
Dec. Sadeeq ne ya matsa gaba kadan ya kunna screen din abinda ya faru a jiya da daddaren.
Ga mamakinsa har ma dana mai gadin babu komai daya nuna cewar wata mata tashigo.
Abinda ya kara girgizasu shine yanda iya mai gadin ne a ciki,inda ya fito yana magana sannan ya matsa alamar mutum yashigo,har inda ya tafi zuwa debo ruwan,da kuma wucewar mutane da bakaken kaya.
Bayan fitarsu kuma mai gadin ya dawo dauke da kofi a hannunsa ya miƙawa wani waje,kofin ne ya tsaya a iska kafin ya karkata alamar wani mutum boyayye a wajenne yasha.
Dukkansu zaro ido sukayi kowa na kallon kowa,wanann abin akwai ayar tambaya a ciki.
Shikam mai gadi jikinsa sai karkarwa yake dan ba karamin bugarsa abin yayi ba sosai.
Magana ma kasa cigaba yayi,abinka da mai gudawa dama,tuni yayi hanyar bandaki yana duk addu'ar data zo bakinsa.
Numfasawa Dec. Sadeeq yayi kafim ya kalli khamriyyah
"Wannan abin akwai daure kai,a yanda na fahimta wamda suka daukeshi sunada alaka da matar da mai gadi yace yagani,duk da banida masaniya shin mutum ce ko aljan"
Duk maganar dayakeyi khamriyya batace komai ba,dam itama akwai abinda take sakawa a ranta daban.
Suna nan tsaye mai gadin ya fito daga bandakin yana zuzzura ido,jar yayi hanyar barin wajen ya tsaya cak jin maganar da Dec. Sadeeq yayi masa.
"Shin kozaka iyah kwatanta mana yatake,ya kuma siffarta yake"
Marairaice fuskarsa yayi kaman mai shirin rusa kuka.
"Haba haba yallabai,yanzu karasa wace mace kake so ma siffanta maka sai aljana mai tsohon ciki hakanma,kalan na siffanta ta, mai ɗakina datake kauye ta haifi mai kamarta,yaudarata ma datayi na yafe haka"
"To naji dalilinka,amma ko sunanta bata fadamaka ba"
Sauke ajiyar zuciya yayi kaman bazayyi magana ba saikuma yace,
"Cewa tacemin na kirata da MABARACIYA kawai,dan wai dama ita bara take"
Shiru Dec. Sadeeq yayi yana cizar fatar bakinsa ta kasa kaman mai tunani,can kuma sai ya zabura tareda yin magana kaman wani zai rigashi.
"Haka tace maka sunan ta MABARACIYA?,abin da mamaki,inkuwa itace to ai yakamata ace ta mutu,ko akwai wata bayan ita kai?"
"Wacce magana kake ne sir"
Dagowa yayi yana kallon khamriyyah wacce ta kureshi da ido.
"Ahah babu komai,idam mun zauna zan miki bayani,yanzu dai yakamata mu koma headquarter dan akwai abinda nazarinsu sai a can"
"Okay sir"
Murmushi yayi kafin yace,
"Aikiniki yana kyau Dec. Khamriyyah,kinda jajircewa da nuna bajinta akan aikiniki,hakanne yasa nafi jin dadin aiki dake"
"Nagode"
Shine abinda ta fada cikin karamar muryah,da alama taji dadin yabonnasa,duk da kuwa yanda zuciyarta ke kunshe da Abubuwa kala kala na abinda ya faru a gidan.
Tare suka fito daga gidan,burka mashidin nata ta dungayi amma kuma sam yaƙi tashi,kallonta dec. Sadeeq yake wanda bai shiga motarsa ba yana ganim mai take,kafsewa tayi tareda juyar da kanta tana kallon gefe.
"Meyasamu mashin din naki,uhm kuma mata da hawa mashin..."
"Ogah toh keke zan hau inba mashin ba,ina naga kudin siyan mota toh"
"Eh naji,bari mashin din bala zai tafimiki dashi zo na nasaukeki a headquarter"
Amma sir daka barshi ma zan......"
"Kinga na gama magana,ki barshi zai gyaromiki inyaso sai ya kawomiki can din"
Ajiye mashin din tayi kafin ta nufi motar tasa,daga gani kasan dam babu yanda zatayi ne kawai.
Tafiya suke a hankali babu mai cewa wani komai,wayar tace tayi kara ganin shugabansu ne yasa ta daga,a yanda take amsa wayar kasan ko a gabansa iya kaci kenan.
"Yes sir ga shi nan ma sir din yallabai"
Mikawa dec. Sadeeq wayar tayi tareda magana cikin girmamawa,
"Gashi ogah,shugaba yace ya kira wayarka bai sameka ba tun dazu"
Karba yayi ya saka a kunnensa yafara magana,can kuma ya kashe ya mika mata wayar
"Dec. Khamriyyah kiyi hakuri zan ɗan bi ta gidana na dauko wasu takaddu kinji"
Zaro ido tayi da alama maganar batayi mata ba sam.
"Amma ogah kasan fah madam bazata so hakan ba,dan duk cikin ma'aikata matannan nice bata so saboda tana tunanin sosayya mukeyi dakai"
Yar dariyah yayi kafin yace,
"Karki damu babu abinda zai faru,zaki iyah zama a mota ki jirani har na fito,hmmm Amrah akwai kishi sosai"
"To shikenan ogah babu matsala"
Karkata motar yayi zuwa gidanansa,kaman yanda ya fada a motar ya bar khamriyyah,saidai kuma yazo fita ya kula da wani ciwo a kafarta yana zubar da jini,da alama lokacin da take burka mashinne ya yanke kafarta,komawa yayi ya zauna tareda kallon wajen
"Subhanallah a Ina kika yanke kafarki haka"
"Ahh ogah a wajen mashinne dazu,ba wani abune mai girma ba inna koma gida zan gyara wajen"
"Ahah idan kika barshi zai iyah zama miki ciwo babba,shigo ciki ki gyara da first aid yanzu"
"Amma ogah....."
"Banaso idan na faɗamiki magana ko nanemi yimiki taimako ki dunga musawa fah"
"Kayi hakuri ogah"
Fitowa tayi a motar kanta a sunkuye har suka shiga cikin gidan,sallama tayi daga bayansa wanda yasa Amrah tsayawa daga rungume dec. Sadeeq din,sannan Murmushin datake ma ta tsaya dayinsa ta murtuke fuska.
"Baby mai nake gani a bayanka,mai tazoyi kuma a cikin gidana bayan kasan bana......"
"Kinga wify ba wani abu bane trust me,mashin dinta ne yasamu matsala gashi zamu je office yin wani bincike,toh abbah yace na ɗauko masa wasu takardune dasuke wajena shiyasa na zo gida yanzu,da farko nace ta jirani a mota saikuma naga kafarta da ciwo,kiyi hakuri tana gyrawa zata tafi a gidanki mai gida"
Yafada yana jan hancinta,ajiyar zuciya tasake,saidai duk da haka hankalin ta bai gama kwanciya ba sosai.
Dakinsa ya wuce domin dauko box din,yayinda khamriyyah ta zauna a ɗan bakin kujera har ya dawo,dan itama kanta yanda take daga gani kasan bata son zaman wajen.
Daya dauko akwatin niyyar tsugunnawa yayi zai sakamata,suna hada ido da Amrah ya miƙawa khamriyyah akwatin saboda ganin kallon da amrah ta bishi dashi,sake komawa dakin yayi ɗauko abinda yazo ɗauka.
Lokacin daya fito tagama gyara wajen,godiya tayimasa kafin suka fita daga gidan.
A hanyar su ta zuwa office din har sun kusa isa wayarsa tayi kara daya saka a jikin charger mota,number Ahmad ceh dan haka ya dauka da gaggawa.
"Ahmad menene ya ake ciki"
"Eh dama wani massage ne yashigo wai yana cewa mu shiryah gobe zasu dawo da dr. Bukar din"
"Da wane layi aka kira,kun samo karin bayani akan wanda ya turo sakon?"
"Ahah ogah,munbi diddigin layin amma ya nuna layin baya nan (not exist)"
"Oh shitt kucigaba da dubawa,yanzu barina sauke khamriyyah a gidansu,ta ɗan samu rauni,zan zo nasameka daga nan"
A bakin kofar gidannata ya ajiyeta yana ta sauri,itadai kallo da idone nata kawai.
Ko amsa Godiyar datake masa bai yiba yayi gaba.
Itama shiga gidan tayi tana tafiyah dakyar saboda gajiyar data diba a ranar.
Karo sukayi da wata yarinya mai kaman shekara bakwai,tana rike da kofi da cornplask a ciki.
"Anty sannu da dawowa"
"Ina diddy take da kuma fadeel saike kadai?"
"Suna baya yana taya diddy wanke wanke"
"Ke kuma kina nan kina shegen ci koh,bake yakamata ki tayata wanke wankenba?"
"Yi hakuri anty bazan sake zama ban tayata ba kinji anty"
"To naji bani waje toh,kuma kar wacce ta shigomin daki zan hutah,idan anty maryam da shigo da anty balki kice musu su jirani idan na gama hutawa zamuyi magana karki manta fah kinji"
"Bazan manta ba,zance su tasheki idan sun shigo,sun tafi siyyar kayan abinci ne dama"
"Kaiii fadeelah yaushe xakiyi hankali ne ƴar butar ƙaniyah kai"
Takalminta ta cire tana niyyar ƙwaɗamata taruga da gudu wajen diddyn,dan ta taimaketa.
Ƴar dariyah tayi da halayyar yarinyar kafin ta jijjiga kai ta wuce daƙinta.
Ƙiran magribane ya tasheta daga baccin datakeyi,hamma tayi tareda yin salati kafin ta faɗa banɗaki.
Wanka ta iyo da alwala,ta saka kananun kaya riga da wando,amma irin buje ɗinnan.
Maryam ta samu da balki da kuma twins ɗin da diddynsu suna cin abinci ,karisawa tayi itama ta zauna,kallon ta sukayi kafin suka hada ido,da alama da abinda suke saƙawa,haɗe fuska tayi tareda cewa,
" menene naga kuna kallona haka,sanjawa nayi kome?"
"Ahah babu abinda ya sanja ogah,kawai dai sir ɗinnakine ya aiko miki mashin ɗinki,yace kuma ya jikinnaki,harda magani ma ya aiko,wanann kuwa ba folawa yayi ba kuwa?"
" ahah kakar folawa kai,mai zanyi dashi toh,kun riga kunsan matsayinsa a wajena bayan shugabana ma,beside ma he is not my type,dan haka karna karajin kun hadani dashi"
Tafada tana caka cokalinnata a cikin abincin,dukkansu shuru sukayi babu mai ce wa uffan sun sha ruwan jikinsu.
Fadeelah ce ta tuntsire da dariya harda faɗawa kan ƴar dattizuwar dasuke ƙira da diddy.
Tsaida idonta tayi akan yarinyar wacce ta har yanxu taƙi barin dariyah,saima nunata datake da yatsa.
"Hhhhhh keki ga anty saikace wlh boss ɗin film ɗin Masheƙi"
Kamo hannunta tayi zata daketa,aikuwa ta rutse idonta tareda cewa
"Maaaama tahhhh"
Saurin sakinta tayi jin ta ambaci mahaifiyar tata,tana ganin tasaketa kuwa ta tashi tayi ɗaki da gudu tana dariyah.
"Ohhh allah Anty juwairiyah kin haifi ƴar da take shiga hancina da ƙudundune,allah ya shiryeta ke kuma allah ta jiƙanki"
Suma sauran mutanen wajen ɗan murmushi sukayi,dan yarinyar bataji kam sam,inka gansu kaman ba cikinsu ɗaya da fadeel ɗin ba,ya zauna yayi shuru so gentle.
Khamriyyah ce ta miƙe bayan ta cika cikinta,ɗakin ta nufah tana tafiyah tana musu magana.
"Ƴan uwa ku shiryah mu wuce fah,am bar Safiyyah da nawwarah su kaɗai a can,dan ma Deen yana can,amma duk da haka lokaci yayi.
Suma nasu ɗakin suka nufah,dayake gidan yana ɗauke da ɗakuna masu yawa,alama duk matan kowa da nata kenan.
Cikin shiri suka fito da kayansu na aiki,kowa kuma riƙe take da babban hijabi wanda zasuyi basaja dashi.
Fita sukayi tareda yiwa diddy sallama,akan sai gobe,fatan nasara tayi musu kafin sukayi waje,tafiyah fadeel yayi ya rungume khamriyyah tareda cewa ,
"Anty saikin dawo,karkiyi fushi da fadeelah ke kadai kawai takeyiwa wasa bayanni,tana sonki itama"
Haɗiye kukan daya taho mata tayi tareda cewa
"Karku damu yarana nima ina sonku sosai kunji,kaje ka kulada ita kafin na dawo kaji,ga nan diddy maza zatayi muki addu'a kafin ku kwanta."
Saida suka shigo wajen aikinnasu kafin kowa ya cire hijabinsa ya ajiye.
Ɗakin da aka kwantar da Dr. Bukar suka nufah,gefe kuma duka daƙuna ne kowanne da ɗan gado a ciki da banɗaki,saidai kofar a rufe take,wani daga cikin wanda suke ɗakunann yafara buga ƙofar yana magana.
Kallon zainab khamriyyah tayi tareda tambayar wanene a ciki.
"Uhm ɗan gidan minister ne da aka kawoshi jiyah"
"Egnr Aisha Eemran?"
"Eh itace,tun ranar yake ta......."
"Bashshi dama dole yayi saboda bai san wahala ba ko kaɗan,yayi sa'a ma da iyah ajiyeshi akayi kawai a ɗakin,hmmm naji labarin itama yanda hankalinta ya tashi ai,ƴan rainin hankali,saina kai mata kansa naga tsiyah"
Wucewa tayi ɗakin da suke aikin Dr bukar ɗin,yana kwance a jojjona masa wayoyi a jikinsa yana fitar da numfashi da kyar da kyar.
Wani file dr nawwarah ta miƙawa khamriyyan tareda cewa,
"Duk wani abu daya kamata ayi an zartar shugaba,buƙata shine a bashi ruwan zuwa anjima idan ya farka,daga nan kuma aiki ya kammala"
"Sai ki dunga ƙirana da shugabarki duk kuwa da yanda kika girmeni a matsayi da kuma shekaru"
"Hmmm dan bakisan yanda kike a zuciyarmu bane shiyasa kika faɗi haka,ke tamkar zinariyah ce da muka tsinceta a lokacin da muke tsaka da neman ko kwandala ce wacce zamuci abinci.
Kin bamu ƙwarin gwiwa da kuma muradin yin abinda ko namiji bai isa bamuba,keɗin tamkar ɗayace da dubu,dan haka bake kika samemu ba mune muka sameki"
Ɗan murmushin gefen baki tayi tareda cewa
"Ki daina irin wanann zancen nawwarah,kin fikowa sanin na tsani abinda za'ayi ko a fadamin dazai jawo min karayar zuciya,yanzu dai aiki yayi kyau ina miki jinjina,barina je na ɗan ji da wancan ɗan gidan minister,dan in ba rufe masa baki akayi ba bazayyi mana shuru ba sam,"
Fita tayi daga dakin tareda saka wata fuska ta nufi ɗakin dayake.
Can kaman wajen karfe shabiyu saƙo ya shiga mata kan cewar dr. Bukar ya tashi daga aikin da'akayi masa na cire ƙoda.
Ɗakin ta nufah inda ta ganshi a zaune,kwana ɗaya har ya rame yayi baki,daga ɗan kansa akayi da pillow sai nishi yake bakinsa ta bushe.
A gabansa ta tsayah tareda kama kunkumi tana dariyah,shima kuma sarai daga gani ya ganeta,buɗe baki yayi a hankali da kyar tareda cewa
"Mmmmai ya ......fffaru dani a a anan wajen?"
"Aiki mukayi maka yallabai,gani mukayi baka dace ace kamar ka kana amfani da ƙoda ba,ta roba zata fi maka kyau shiyasa muka ciresu muka saka maka na roba,to yanzu sai kayi mana godiya"
"Ammmm..."
Shuru yayi yama kasa cewa komai,babu abinda yake sai zubar da hawaye,dan a yanda yake bashida karfin halin aikata komai,hannun ya kai dayake rawa ya ɗora akan babban bandejin dayake kan ruwan cikinsa,tabbas ba mafarki yake ba hakane,sun cire masa ƙoda,dan ga alama nan ta nuna har a bakinsa najin kishirwa dayakeyi.
"Oh sorry ba manta bari a kawomaka ruwa kasha,karka margaya tun yanzu"
Ruwa ta tsiyanyo a kofi daga cikin butar faro,da kaman baxai karba ba,amma ganin ruwan mai kyaune kuma yana buƙata yasa ya buɗe bakinsa ta zuba masa.
Kwat kwat yafara shan ruwan da kansa ya kawar da kai.
Dr nawwarah ce tashigo ɗakin tareda cewa
"Shugaba yasha ruwan ?"
"Ehhh yasha fiyeda yanda nake tsammani ma kuwa,aiki yayi yanda muke so,yanzu kafin ya fara birkicewa ya kamata mu jefarshi su tsinceshi"
Zaro ido yayi jin abinda suke faɗa,musamman da idonsa ya sauƙa kan fuskar dr nawwarah,wacce take masa kallom tsana.
"Dr. To yanzu ya gaka yanda abun ya juyah,kasan ruwan da muka baka kuwa,ruwane mai dauke da sinadari mai karfi wanda temporary kidney baxata iyah excretion ɗin sa ba,mai kake tunani zai faru to a matsayinka na likitan ƙodar,nasan basai na fadamaka ba kasan result ɗin dazai haifar?
Kafin nan ka more guntun lokacinka wajen tunanin,takaici,razana ,zullumi dadai sauran abubuwan dazasu kara worse ɗin ciwon,kan ka farga babu damar komawa da baya,saidai ka tunkari mutuwarka"
Tunkafin ta gama maganar ma jikinsa yafara tsanani,kana ganinsa kasan ba karamin mawuyacin hali ya shiga ba sosai.
Khamriyyah ce ta kalli su maryam wanda har sun shirya dama fita dashi.
"Vl3(maryam) deen ya ɗaukeku a motah,ku kaishi gefen gidan Dec. Sadeeq ku ajiyeshi"
"Shikenan V- lady,amma kince zaki tafi gidan,mai zai hana mu fita tare?"
"Mashin ɗina aikin mai yake,beside ma banda ra'ayin zuwa,kudai kuyi yanda nace"
Fita sukayi tareda nufar gidan dec. Sadeeq ɗin bayan sun saka shi a cikin boot,zuwa sannan har ya suma bai san inda kansa yakeba.
A gefen wata katanga da take nesa kaɗan da gidannsa suka ajiye gawar.
Har sun taka motar sun fara tafiyah,saikuma suka ga wata mata tazo kan gawar,da kaya a jikinta jajaye,babu abinda suke ganin a jikinta idonta kawai,ganin sun haskata yasa ta fasa yin komai a wajen ta zura da gudu bayan wasu gidaje wanda aka farasu ba'a gamaba.
Maryam ce ta fita da gudu tabi bayan ta yayinda shima deen yabi bayan ta da sauri.
Sun zuwa bayan wajen babu ita babu alamarta gashi kuma ba wani wajen da mutum zai buya a gurin.
"Deen inaga fah aljana ce,dan baka ga kayan jikinta bama,ni wani iri nakeji ma"
"Kefah kin faye tsoro,babu abinda xai faru,mutum ce daga gani kaman kowa,ina ruwan aljani da wani dr. Bukar toh,kawai dai inaga bacewa tayi"
Saurin komawa mota sukai tareda barin wajen,gudun karsu dade a kamasu a wajen.
Akwance yake Amrah tayi pillow da kirjinsa sai bacci sukeyi,dan jiya da daddare ma amai ta dungayi dakyar suka samu ya tsayah,shiyasa sunayin sallah suka koma bacci.
Ƙarar wayarsa ce ta tasheshi daga baccin dayakeyi,itama kuma amrah ta motsa daga kwancen datake.
Dayake tafi kusa da wayar ita tamiƙo masa wayar cikin magagin bacci,sunan data ganine yasa ta jan tsukah mai karfi.
"Kekuma keda wa haka kike jan tsaki?"
Ƙarbar wayar yayi,ganin sunan khamriyyah yasashi yin ƴar ƙaramar dariyah,yana shafah kanta wanda ta mayar ta sake kwanciyah tana tura baki.
"Hell............what?,a gefen gidana kuma meyasa? Ganinna fitowa yanzu nan,ku tabbatar kun kula sosai"
Saurin zame jikinsa yayi tareda jura rigarsa yafita da sauri.
A bakin ƙofar gidannasa yasamu dandanzon ƴan sanda,sai ƙokarin ture mutane suke.
Khamriyyah ce ta nufoshi da wata takarda a hannunta.
"Barka da safiya ogah,ga can gawar yanzu muka samu bayani daga wani ɗan anguwar daya ganta,babu wanda yaje wajen isowarmu kennan"
Ta gefenta ya wuce ba tareda yabawa abinda take faɗa muhimmanci sosai ba,burinsa ya isa ga gawar kawai.
Tsugunnawa yayi a gaban wajen yana kare mata kallo,wata ƴar takarda ya ciro a gefen gawar fara,daukowa yayi tareda buɗewa.
Rubitune irin na almajirai na warash,saidai kuma bana larabci bane,in ba wanda yayi zurfi a karstun nasu ba ba zai iyah karantawa ba bare rubutawa,dan dasu ake amfani ake ƙiran aljanu da kuma siddabaru.
Duddubawa yake saidai ya gagara karantawa sam.
Khamriyyah ce ta iso wajen tana kallon takardar a hannunsa,mikamata yayi tareda cewa
"Duba ko zaki iya ganewa?"
"Ahah yallabai,(ɗaga muryah tayi tareda nunawa mutanen wajen),akwai wanda zai iyah karanta mana wannan yaren kuwa"
Shuru akayi sai daga baya wani almajiri ƙolo ya fito tareda ƙarbar takarda,a dole an ƙirashi wajen bincike.
Duddu bawa yake alamar mai son gano wani abun,koda ba duka bane daga tasa fahimtar.
Ɗagowa yayi tareda nunawa dec. Sadeeq wani waje a jikin takardar ta ƙasa.
"Eh to nima ban iyah rubutawa ba amma kuma nakan gane harafi kaɗan kaɗan ba masu wuyah ba...........nan dai ta wajen ƙarshen MABARACIYAH aka rubuta dan na san na kalmar mabarata,nan mabaraciyane a rubuce.
Amma nasan malamina zai iyah karanta muku wasiƙar."Mabaraciyah kuma?"
Sadi-sakhna.........
YOU ARE READING
MABARACIYAH
ActionDuniyah juyi juyi abubuwa da dama sukan faru amma haka zasu zasu wuce kaman ba'ayi ba. Idan anyi maka abu sai a ce kayi haƙuri watarana zai wuce meyasa?. Ban yadda da wannan maganarba,madadin na barshi ya wuce saidai na ajiye domin neman fansa. wan...