*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*2*
"Maijidda na kasa gane wajen".
Fillo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin.Maijidda dake tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar dake hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa.
"wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me kikai ne a wurin nan?".
Fillo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun dake wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen.
Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka ɗauko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk sanda ta tuno, abu ne da bai shafeta ba amma ta kasa mantawa da shi acikin ranta.Ita dai tasan ta kuɗuri aniyar tarwatsa alƙadarin waɗanda sukai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani ayanzu shine waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi acikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa acikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba?, me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me yayiwa masu son kassara rayuwarsa?.
Bata da dukkan amsar waɗannan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce ba. Komai yana nan daki-daki acikin kanta, fuskokin mutanen da sukai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu dakayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar sune.
MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake ajikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta saina sunansa da jan penti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tai arangama da layar, kuma haka taita ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa.
Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen sukai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan dake rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya.
Abu guda kawai tasan da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke acikin wannan babban gidan da baya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami.
kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir.
A lokacin bata san taya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasa bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku suna kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya.