Shafi na 21

89 9 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email-Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 21'''

Shi ma miƙewa yayi yana kallonta "Na san dole za ki ji wani iri ace na saki ƙanwarki kuma ina shirin aurenki, Jannat tun lokacin da muna soyayya dake na ɗauki alƙawarin ba zan taɓa bari ki wulaƙanta ba, kuma har lokacin da kika gujeni ban janye daga wannan alƙawarin ba"

Hawaye sharkaf a fuskarta take kallonshi. Ya cigaba da faɗin "Na san wannan furucin zai tada rigima sosai a family ɗinmu, amma haka ba zai saka in janye daga ƙudirina ba, zan maye maki gurbin farin cikin da kika rasa ko da zan rasa nawa farin cikin"

Bakin ta na rawa ta ce "Kenan dama saboda ka aureni ne ya saka ka saki Farhan? Kaci amana" "Jannat kada ki yanke hukunci kan abinda baki sani ba, da ace zan saki Farhan dan na aureki da tuntuni nayi haka, to amma na san a musulunci ma haramun ne, na saki ƙanwa saboda ina son Yayarta ina..." "To meyasa ka saki Farhan, meyasa?" "Saboda ta zagi mahaifiyata, Allah zai zame min shaida, sam ban saki Farhan dan na aure ki ba" "Yaya Khalil kai kasan wannan abin sam ba mai yuwuwa bane, ni kawai ka zaɓa min wanda zan aura idan ba haka zan fitar da kaina, amma ni bazan iya aurenka ba." tana gama faɗa ta juya da sauri ta yi ciki tana hawaye.

Tana tura ƙofar ɗakinsu taga Farhan a tsaye ta juya baya. Juyowa Farhan tayi idanunta sharkaf da hawaye ta ce "Kin ci amanar ƴan uwantaka, duk abinda Yaya Khalil ya faɗa miki ba wanda ban ji ba" "Amma dai ina fatan kin ji nima amsar dana bashi" "Amsar ai bata nufin kinji haushin sa akan sakina da yayi" matsowa tayi za ta dafa Farhan ɗin, da sauri taja da baya "Kada ƙazamin hannunki yayi gigin taɓani, nayi dana sanin kasancewarki ƴar uwata" sai kuma ta share hawaye tana faɗin "Ta wani ɓangaren kuma ina godiya ga Allah daya sa ba ciki ɗaya muka fito ba."

Runtse ido Jannat tayi ta zauna a gefen gado, yayinda Farhan ta fita daga ɗakin tana kuka a fili. Ɗakin Ummu taje tana hawaye ta zauna kan sofa. "Me kuma ya faru?" Ummu tayi tambayar "Ummu da bakina naji Yaya Khalil yana faɗin zai auri Jannat" ta ƙara fashewa da kuka.  "Ki daina kuka kin san haka ba zai taɓa yuwuwa ba "Ummu wallahi ina son Yaya Khalil" "Dalla rufa mana baki, mutumin daya wulakantaki, ai na san mahaifinku ba zai taɓa yarda ya aura masa wata a gidan nan" "Ni Ummu kawai zan dawo ɗakin ki da zama bana jindaɗin zama kusa da Jannat ina kallonta sai in ƙarajin ƙunar zuci."

Tashi sukayi zuwa ɗakin, suna tura ƙofa Jannat ta ɗago kai tana goge hawaye. Tsaki kawai Ummu tayi, tana kallonsu suka kwashe kayan Farhan suka fita. Bata iya yin magana ba kamar yadda ba suyi mata ba.

*1 Week Later*

Suna zaune a dinning area suna lunch ba wanda ke ma wani magana, Daddy ne ya ɗago ya kallesu, ajje spoon yayi "Na lura gidan nan sam baku jituwa yanzu, Ke Farhan kin zauna kusa da Mamanki haka itama Jannat" shiru babu wanda yayi magana, Daddy ya cigaba da faɗin "Ba zan lamunci haka ba, ada ina alfahari da gidan nan amma a yanzu gaba ɗaya kun lalace, kamar kuna ganin hanjin cikinku, to ba zan taɓa lamunta ba, ina son ganin canji daga yau ɗin nan, Yadda ake zama aci abinci ada haka nake son  naga kun cigaba" cije leɓe Jannat tayi sannan ta ɗago kai "Daddy dan Allah ku yafe min, na san duk wannan abin daya faru ni ce sanadi, da ace ban bijirewa umarninka ba na san duk haka bata faru ba" Hannu ta saka tana goge hawaye. "Shi mutum matuƙar yayi kuskure kuma ya gane yayi to abinda ake so shine ya gyara, ba kuka za kiyi ba, ki yi haƙuri ki kuma gyara kuskurenki" kai kawai ta gyaɗa tana ƙara goge hawayen da bai bar zuba ba. "Rayyan zai zo da yamma, sannan Khalil ma ya ce yana son ganinki shima zai zo amma bai faɗa min lokaci ba" Da Farhan suka haɗa ido ta harareta sannan ta tashi za ta bar gurin Daddy ya dawo da ita.

Dawowa tayi ta zauna tare da dasa tagumi. "Ba wa Jannat haƙuri" "Daddy ni ban mata komai ba" "Duk abinda kike idanuna a kanki, kibata haƙuri kafin ranki ya gama ɓaci" ranta a ɓace tace "Allah ya baki haƙuri" Bata ce komai ba kawai kanta ta sauke ƙasa. "Gaskiya ba'a yiwa Farhan adalci, a barta da abinda take ji ma" "To me aka yiwa Farhan ɗin?" "Faɗa mana, sai faɗa kake mata" cewar Ummu. "Na lura gaba ɗaya kin canza, kin saka Farhan ta dawo ɗakinki sannan matsalarma daga ke ne" "Dole ka ga canji tunda har ba za ka rabu da mutumin daya jefa ƴar ka a damuwa, saki uku fa. Amma kuma sai ƙara jan shi kake a jiki, kallonku kawai nake kuma, kuma Farhan dole za ta dawo ɗakina mana saboda tana da larura  bana barta ita kaɗai ba"

"Akwai Jannat a ɗakin ai, ba ita kaɗai bace" "Jannat tana ta kanta, idan bani ba wane zai kula da ita" tashi tayi ta bar dinning area ɗin. Da ido Mommy ta bita tare da sauke ajiyar zuciya. "Yallaɓai dan Allah ka bar wannan maganar" "Taya zan bari, so kike in bar iyalina kai a rabe, ba zai yuwu ba." tashi yayi shima ya bar gurin, Farhan na ganin haka ita tayi sauri ta bar gurin.

*Yamma*

Suna zaune akan plastic chairs a cikin rumfar dake farfajiyar gidan. Bayan sun gaisa babu wanda ya sake magana sai daga baya ya ce "Ina fatan Daddy yayi miki bayani akan zuwana" "Yayi amma ina so na tambayeka" Jannat ta faɗa lokacin da ta ɗago idanu tana kallon Rayyan "Ina saurarenki" ya bata amsa. "Meyasa kace kana son aurena bayan kasan abinda ya faru dani? Tausayi ko?" "Da kuma son gaskiya" murmushi tayi ta ce "Mu dai tsaya kan tausayin, amma ban sani ba ko kana da labarin zuwan Mahaifiyarka wannan gida" "Tazo ne?" kai kawai Jannat ta gyaɗa alamar eh. "Na san zuwan Mommy gidan nan ba alkhairi bane, amma ka da wannan ya ɗaga miki hankali, domin kuwa ni ne zan zauna dake ba ita ba"

Motar Khalil da ta shigo gidan ya saka gabanta ya faɗi, ta kalli motar sannan ta dawo da kallonta ga Rayyan. "Bijirewa umarnin iyaye shine ya saka ni a wannan mawuyacin halin, ina mai baka shawara da ka haƙura da duk abinda basu so" "Amma ai mahaifina yana so, kuma ita bata da hujjar hanani aurenki" "Ita ko ke da hujja domin itace silar zuwanka duniya" a dai-dai lokacin Khalil ya ƙaraso gabansu dan haka sukayi shiru.

Yana ƙarasowa ya miƙawa Khalil hannu sukayi musabaha, Jannat kanta na ƙasa taƙi ɗagowa ta kalleshi. "Idan babu damuwa ina son magana da kai" ya faɗa yana kallon Rayyan "Ba damuwa bismillah" kallon Jannat yayi ya ce "Ki shiga ciki za muyi magana dashi" batayi musu ba ta tashi ta bar gurin.

Tana tsaye a main parlor tana ta cije leɓe tana buga hannu, Allah-Allah take ya shigo ya sanar mata abinda suka tattauna. Tana nan tana saƙe-saƙe ba kowa a parlorn sai gashi ya shigo da sallama a bikinsa. Da ƙyar ta iya amsa masa, sai daya zauna sannan ya ce "Ko ƴan gidan basu nan?" "Daddy ne kawai baya nan" "Okay."

Ganin bashi da niyyar faɗa mata abinda suka tattauna yasa ta nufi hanyar komawa "Ai ko da kinje ma baya nan, dan sai daya fita sannan na shigo." Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, ta kalleshi tace "Korar shi kayi?" "Ba korar shi nayi ba, na faɗa masa gaskiya ne dan ba zan bari kiyi aure inda za ki sha wuya ba" Da mamaki ta kalleshi "To wai wa kake son na aura ne idan kana korar min masoya?" "Ni" ya faɗa ba tare da kunya ba.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama a kujera ta dafe haɓa. "Jannat wai mene aibuna?" kallon shi tayi sannan ta ce "Da ace ba Farhan ka saka ba, baka da wani aibu a gurina, amma yanzu kasan ko sama da ƙasa za su haɗu ba zan taɓa aurenka ba" "Sama da ƙasa ba za su haɗu ba, kuma ni na san sai kin aure ni insha Allahu" "Abu ne da ba zai taɓa yuwuwa ba" "Jannat ki juyo ki kalleni ki faɗamin cewa wallahi baki jin soyayyata a zuciyarki ni kuma zan haƙura ki auri koma waye" ƙin kulashi tayi tama rasa abinda za tayi saboda takaici. "Hakan ya nuna cewa kina sona har yanzu, wani daliline ya hanaki bayyanawa, amma tunda musulunci bai haramta hakan ba, ni zan samu Daddy na sanar masa cewa ni dake mun fahimci juna" tsaye ta miƙe ta kalleshi a kiɗime.

Shima miƙewa yayi yana kallonta hankali kwance babu alamun tashin hankali ko damuwa a tattare dashi. "Meyasa wata wutar bata mutu ba kake ƙoƙarin kunna wata, kada ka manta Farhan fa har yanzu tana cikin idda" "Ai hakan ba zai hanani aurenki ba tunda aurena da ita ya ƙare" "Wai ka manta zuciyata akwai tsaga? So kake damuwa ta kasheni?" "Damuwa ba zata kasheki ba sai dai tsoro, muddin kuwa baki amince da aurena ba to na tabbatar baki sona dama tun fil azal"

Dafe goshi tayi, sai kuma ta kalleshi ta wuce cike da damuwa.

*Ina mai baku haƙurin jinkirin typing da posting*

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now