Page 22

76 17 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email-Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

_*Masoyana musamman na WhatsApp ina jindaɗin comments ɗinku sosai da sosai, ina godiya mutuƙa🥰*_

                    '''Shafi na 22'''

Yana nan tsaye sai ga Mommy ta fito tana ƙoƙarin nufa kitchen ta hango shi. Da sauri ya ƙarasa gabanta, har ƙasa ya durƙusa ya gaisheta. "Lafiya kuwa na ganka kai ɗaya a tsaye?" "Eh nazo wajen Daddy ne, kuma baya nan" "Hakane ya fita, amma ko a kirashi a waya?" "Ba damuwa Mommy, zan dawo zuwa dare, ko in kirashi a waya" ya faɗa yana sinne kai, wai shi a dole suna magana da suruka.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Rayyan da Ahmad babu wanda ya ƙara zuwa gidan su Jannat, shi kuma Khalil bai ƙara yi mata wata magana ba, ko ya zo gidan, gaisuwa ce kawai ke haɗa shi da ita, sai tayi sauri ta gudu ɗakinta ba ta taɓa yarda ma ta zauna inda yake.

*3 Months Later*

Daga inda yake kwance ya ɗago kai ya kalli Umma, hannu ta saka ta goge hawayen idanunta "Umma wataƙila mutuwa zanyi" ya faɗa cikin jin jiki. "Waye ya faɗa maka, cuta ai ba mutuwa bace" "Umma jikina yayi zafi sosai, har baya jin magani, ina buƙatar ganin Jannat dan in roƙeta gafara, ina ji a jikina alhakin Jannat ne ke bibiyata."

Umma ta sake fashewa da kuka ta ce "Tabbas nima na fara yarda da hakan, domin kuwa ƙiri-ƙiri gidan da muke ciki wanda shine kawai nake gani a matsayin gadonku, an koremu, kayanmu na maƙota, yanzu duk ranar da aka sallameka a asibiti ban san ina zamu kwana ba, duk kuɗin da kake tari dasu ake jinyarka ga kuma abinci da muke saya" ta saka gefen zani tana goge hawaye.

Hanne ta taso daga kan tabarmar da take zaune ta kalli Umma "Umma haƙiƙa alhakin Jannat ba zai taɓa barinmu ba, muddin bamu nemi yafiyarta ba, daga wannan sai wancan, abubuwa sai faruwa suke damu. Umma ba mu riƙe matsayinmu na talakawa, kuma marayu, mun cutar da baiwar Allah da ta sadaukar da farin cikinta domin farin cikin Yaya, taya ma alhakin Jannat zai barmu, dole mu nemi yafiyarta. Ki kalli Yaya fa, duk yayi baƙi ya rame, wai a haka malaria ce ke damunsa, amma zuwanmu nan an saka masa jini sau uku a sati biyu kacal, saboda jininsa ma ƙonewa yake, ina fatan Allah ya tashi kafaɗunsa, domin neman yafiyar wadda aka zalunta."

Girgiza kai Umma tayi ta ce "Tabbas sai yau ne na tabbatar da cewa na zalunci Jannat, ni duk abinda nayi, na yi ne domin tsoron kar wani abu ya faru da ƴaƴana, kuma ina ganin kamar Jannat ta kwashi cuta, tabbas na yadda ubangiji mai hikima ne, ita ga ta ta warke garas, shi kuma ya samu ciwon da ba zai taɓa warkewa ba, ciwon rashin haihuwa" Kuka ta cigaba dayi, shi kuma Sa'ad ya runtse ido yana jin ƙunar zuci.

Hanne ta ƙara faɗin "Umma duk da haka kinyi kuskure, kiyi haƙuri zan faɗa miki gaskiya" ɗago jajayen idanunta tayi ta kalli Hanne. "Ina sauraronki, domin nayi nadama kuma ina so na gyara kuskurena.
        
Ajiyar zuciya Hanne ta sauke sannan tace "Umma tun farko da aka sanarwa da Jannat cewa Yaya na sonta, taji ba daɗi amma sai ta bashi haƙuri saboda ita bata ma san yana yi ba, kuma tana da masoyinta na gaskiya. Amma sai kika dage kikayi amfani da shaƙuwar da sukayi kika nemi rabasu, wanda kin san itace hanya kaɗai da za ki bi wajen jawo Jannat ga Yaya Sa'ad. Haka kuma ta faru, Jannat ta bijirewa iyayenta, ta zaɓi ceto rayuwar Yaya dake kwance rai hannun Allah saboda soyayya. Jannat fa korarta akayi daga gidansu, kuma mahaifinta yace bashi ba ita, sannan ya umarci danginsa duk su juya mata baya, duk fa a dalilin Yaya, amma haka ta daure ta haɗiye ta zaɓi rayuwa dashi. Kwatsam ƙaddara ta faɗa mata wanda ni a tunanina ko HIV Jannat take dashi Yaya zai haƙura ya aureta a haka, amma Yoyon fitsari da kun tabbatar da ana warkewa, amma Umma haka kika je har asibiti tana fama da ciwon abinda ya sameta kika yi mata kaca-kaca, sannan kika ce ba ita ba Yaya, wannan shine babban butulcin da kikayi. Daga ke har Yaya kunyiwa Jannat rashin halacci. Na yi iya ƙoƙarina dan ganin na fahimtar da Yaya, amma sam ya kasa fahimta, saboda shima ya so butulci, in ba dan haka ba, na san zai jajirce ya cigaba da tausasa ki har ki yarda, duk da cewar ke ɗin kaifi ɗaya ce. Umma kuskurenki a nan suna da yawa fa, matsayinki na uwa, kuma kina da ƴa mace, kamata yayi ace kin bar Jannat ta auri wanda take so, shima Yaya sai Allah ya kawo masa wata, ciwon da zaiyi ai na kwanaki ne, anan Umma sai kika bi son zuciyarki, da kin bar Jannat tayi aure da duk haka bata faru ba. Kuskure na gaba kuma, kin wulaƙanta Jannat akan abinda ta dalilin soyayyar Yaya ƙaddarar ta faɗa mata, idan da tana gidan mijinta taya wani zai mata fyaɗe? Idan da tana gidan iyayenta taya wannan mummunar ƙaddarar za ta sameta? Duk son zuciyarki ne, kece sanadi Umma. Jannat ɗiyar hamshaƙin mai kuɗi, mu kuma talakawa ne lis, babu cass ba ass, amma a haka ta shigo rayuwarmu, bata ƙyamace mu ba, ta riƙa ɗawainiya damu da zuciya ɗaya, da Jannat ta ga dama da wallahi za ta iya sakawa a ɗauremu kan wannan butulci tunda suna da arziƙi. Sai dai kuma na san ba za ta taɓa yi ba, tunda ita mace ce mai kawaici. Zai yi wuya Jannat ta yafe mana." ta ƙarashe maganar tana goge siraran hawaye da suka sauka a kuncinta.

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now