Page 26

72 10 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email- Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 26'''

Itama Jannat murmushi take kafin ta ce "Yanzu kafin ya dawo mu kuma mun tafi, na san zai kiraki, karki yarda ki nuna masa tsoro ko mene zai faɗa to kina da abinda za ki kare kanki, number matarsa da address ɗinsa yana hannunmu, kin ga kuwa a tafin hannunmu yake." "Hakane kam, yanzu na samu lafiya, Jannat ba zan taɓa manta wannan alkhairin ba." "Ka da ki damu, nima ai kin min abinda na kasa mantawa ne."

Har asibiti ta kaita lokacin tara har ta wuce. Itama kai tsaye gida ta wuce tana ta addu'ar Allah yasa kar ayi mata faɗa.

*11:30pm*

Har tayi wanka ta saka kayan bacci ta kwanta wayarta ta fara ringing. A hankali ta buɗe ido ta miƙa hannu ta ɗauko wayar dake kan bedside drawer. Bata ma tsaya duba suna ba kawai ta kara a kunne. "Hello" "Ba dai har kinyi bacci ba" jin muryar Yaya Khalil ne ya saka tayi zumbur ta tashi zaune, ji tayi gaba ɗaya baccin ma ya bar idanunta.

"Kina ji na ko bacci kike?" "A'a idona biyu" ta faɗa tana murtsike idanunta da ɗayan hannun. "Ya kike, fatan dai baki cikin damuwa?" "Hmmm" shine kawai abinda ta iya faɗa. "Jannat ni na yanke shawarar zama dake ko ta wane irin hali ne, ni kawai a yanzu ina ji a jikina cewa dake kaɗai zan iya rayuwa"  ji tayi gabanta ya faɗi ta daure dai ta ce "Yaya Khalil ba zan ɓoye maka ba, har yanzu ina sonka amma aure tsakanina da kai abu ne mai matuƙar wuya, dalilai biyu ne za su hana aurenmu" shiru tayi har sai da ya ce "Ina saurarenki?."

Gyara zama tayi ta jingina bayanta da fuskar gado, sannan ta cigaba da faɗin "A halin yanzu ni ba budurwa bace, sannan ina da ciwon zuciya wanda tsagewa ce ma, a ko wane lokaci zan iya mutuwa, abu na biyu kuma Farhan, gaskiya bana jin zan iya auren tsohon mijin ƙanwata, kayi haƙuri ka samu wata ka aura, ni na san za ka samu wadda ta fini, kuma nima ka tayani da addu'a Allah ya bani miji nagari." shiru ne ya biyo baya har sai da ta ƙara duba wayar taga dai bai kashe ba.

Sun fi mintuna biyar kafin ya ce "Shikenan insha Allahu na haƙura dake, zan nemi wata, kema ina miki fatan samun miji nagari, sai da safe." kasa cewa komai tayi har ya katse, sannan ta fashe da kuka a fili.

Kuka sosai tasha har taji wani abu ya tokare a maƙogoronta. Yayinda taji zuciyarta na zafi, da sauri ta miƙe ta nufi ɗakin Mommy a daddafe ta ƙarasa.

"Lafiya Jannat? Mene ke damunki?" Mommy ta faɗa sannan ta tashi ta ruƙo Jannat. Anan ta fara kakarin jini, baƙi ƙirin, hankalin Mommy ba ƙaramin tashi yayi ba ta kira Daddy a waya ta sanar masa. Kai tsaye aka ɗauki Jannat zuwa asibiti lokacin har ta fita a hayyacinta.

Suna zuwa aka shigar da ita emergency dan a bata taimakon gaggawa, yayinda Mommy da Daddy suke tsaye a bakin ƙofa hankali a tashe.

*Washe Gari*

Tun bayan da Daddy yayi sallar asuba ya kira Ummu ya sanar da ita cewa sun kawo Jannat asibiti bata da lafiya, dan har lokacin ma ba a bari sun ganta ba, dan haka a haɗo kayan break a kawo masu, shima yanzu zai shigo gidan yayi wanka sannan ya koma. Da "To" kawai ta bishi, abinda ya bashi mamaki ko dubiya batayi ba.

Wurin ƙarfe bakwai da rabi aka kawo kayan, ɗaya daga cikin ƴan aikin gidan ce, da kuma driver, ba Ummu, ba Farhan, har a lokacin dai ba a bari sun ga Jannat ba.

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now