Page 28

72 11 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email- Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 28'''

Runtse ido tayi tare da dafe cikinta, Khalil ta buɗe idanunta da suka fara juyewa, Khalil ita yake kallo ya ratsa yadda zaiyi.

A hankali ta furta "Jij...jini daga bakin Jannat ka kaita asibiti, sai  lokacin ya kalli Jannat yaga jinin har ya sauka a hannun rigarshi.

A hankali ya kwantar da ita anan ƙasa, yana ƙoƙarin fita, sai kuma ya tsaya gaban Farhan. Kallon cikin nata da ta dafe yayi, yaga jini har ya ɓata mata hannu, gudun data sheƙo daga part ɗin Ummu zuwa na nasu ya saka ɗinkinta ya buɗe.

Hankalinsa a tashe ya ce "Mene haka?" cikin tsananin jin azaba ta ce "Ka kira su Ummu please, zan mutu" ko hawayen ma ya tsaya saboda azabar da take ji, idanunta sun canza launi tuni.

*Hospital*

Daddy, Ummu, Khalil, Aunty Yana, Aunty Farida da Aunty Karime suna daga ƙofar emergency, duk kansu sunyi cirko-cirko.

Ko wanne hankalinsa a tashe yake. Khalil sam ya kasa zama ya kasa tsayuwa yawo kawai yake.

Doctor na fitowa gaba ɗaya suka rufe shi da tambayar jikinsu. Office ya buƙaci su bishi.

Guri suka samu suka zazzauna suna jiran jin bayanai, gyara zama yayi sannan ya ce "Ita wadda aka yiwa C.S ɗin mun samu nasarar ceto rayuwarta ta hanyar gyara aikin, ba'a ɗito da ita daga theater room ba, amma dai an gyara, sai dai zamu riƙeta a nan har ta warke gaba ɗaya.

"Jannat fa...?" Khalil ya faɗa cikin tashin hankali. Shiru Doctor yayi bai ce komai ba. "Doctor ka faɗa mana halin da take ciki" Daddy ya faɗa a raunane.

"Gaskiya bamu da tabbacin za ta tashi, domin zuciyarta ta kumbura sosai, bamu da abinda zamu iya mata, zuciyar ta kumbura kuma a tsage dama take anyi ciko to cikon ma ya fita. Kuyi haƙuri, sai yadda Allah yayi kawai"

                         *****

Gudu sosai yake akan titi, wayarsa da ta fara ringing ya ɗauka ba tare da ya duba mai kiran ba.
"Hello Fahad ya ake ciki ne?"

Daga ɗayan ɓangaren Fahad ya ce "Yanzu na bar office ɗin Sadiq, ya ce zaka iya samun visa nan da kwana biyu, amma fa gaskiya kuɗaɗen dunyi yawa Khalil"

"Fahad ko nawane na san ba zai kai million ba, zan biya, domin lafiyar Jannat tafi komai a gurina"

"To shikenan, amma kuma na mutum biyu ya ce za a iya samu"
"Mutum biyu kuma? To kayi mana ni da Jannat"
"Amma ai dole sai kazo ka kawo details ɗinta ko?"
"To zan zo, yanzu ka ganni akan hanyar zuwa gida ne, amma bari na fara zuwa ta nan."
"To sai ka zo."

*3 hours later*

Cikin yanayi na damuwa Daddy ya kalli Alhaji Auwal ya ce "Duk abinda ka yanke game da yaran nan, hakan yayi domin dukkansu ƴaƴanka ne"

"Hakane, yanzu dai zamu ɗaura aurensu a masallaci da anyi sallar la'asar, za su tafi ƙasar Las Vegas suna da ƙwararrun likitoci, mu in yaso daga baya zamuje. Manufar yin haka kuwa shine, ka ga ba yadda za ayi mu haɗa su tafi tare alhalin ba muharraminta bane, amma idan an ɗaura aure kaga ba matsala"

Daddy ya kalli Khalil daya sunkuyar da kai. "Khalil Allah yayi maka albarka, yasa wannan hidimar ta zame maka hanyar shiga aljanna" "Amin Daddy" ya furta kan shi a sunkuye.

                *****

Mutanen da suka halarci sallar la'asar a masallacin dake unguwar su Jannat, su suka shaida ɗaurin auren  Jannat da Khalil. Wanda wannan lamari ya bawa mutane da dama mamaki, sai dai a koma gefe ayi gulma.

Alhaji Sani da Rayyan suna daga cikin mutanen da suka shaida hakan, ko da suka fito a hanyarsu ta komawa gida, Alhaji Sani yana ta bawa Rayyan haƙuri kan yayi tawakkali dama Allah ya ƙaddara Jannat ba matarsa bace.

Ta ɓangaren dangin Khalil da Jannat kuw, waya Daddy da Alhaji Auwal suka riƙa yi masu. Sai dai da dama daga cikin su, sunce wannan ba ƙaramin abin kunya bane, dan da iyayensu na raye ai ba zasuyi haka ba. Wasu kuwa cewa sukayi shikenan sun jawo masu abin kunya a dangi. Dama tuni sun san haka zata faru dan haka basu wani damu ba.

Khalil kuwa gida ya koma yana ta shiri, yayinda Ummu itama ta koma tana shirya kayan Jannat duk da tana jin zafin abin, amma ta tausayawa halin da Jannat ke ciki, musamman ma da Farhan ta bata labarin irin abubuwan da tayi mata lokacin tana naƙuda, sai taji ba za ta iya barin Jannat ɗin haka ba.

Yana driving Fahad na daga gefensa. "Yanzu kawai sai dai Jannat ta tashi kace mata kai mijinta ne?" "Wannan maganar ba ita ce a gabana ba, mu fara ceto lafiyarta." murmushi Fahad yayi.

*Bayan kwana biyu*

Khalil kam ya samu ƴan rakiya zuwa asibiti, rakacakaf ɗin su sun rakashi, idan aka ɗauke Farhan dake kwance gadon asibiti. Jannat kuwa tana ƙarƙashin kulawar ma'aikata, haka jirgi ya ɗaga sannan suka juya, Daddy har da ƙwallarsa, ashe yana son Jannat haka da yawa, ko kuwa yanzu ne son ya shiga.

Ko da suka sauka kuwa kai tsaye aka zarce asibiti, bayan ya gama komai, ya samu wani babban hotel ya kama ɗaki a ciki.

                  *****

Suna zaune a falon Kawu Bashir, Hanne ba abinda dake fita daga idanunta sai hawaye. Bayan Kawu Bashir, akwai Kawu Mamman zaune a gefe, wanda ya kasance ƙani ga Kawu Bashir ɗin. Sa'ad kan shi na ƙasa, baya hawaye amma dai kuma ta ciki zuciyarsa tafasa kawai take.

Kawu Bashi yayi gyara murya ya fara da cewa. "Haƙiƙanin gaskiya ku ƴaƴanmu ne, domin mahaifinku damu uwa ɗaya uba ɗaya muke. Hakanan kafin ya rasu mun nuna muku kulawa dai-dai gwargwado, sai dai rasuwar mahaifinku mun so karɓarku, amma ganin abin ba mai yuwuwa bane, sai muka barwa Allah. Mun janye daga lamarinku kasancewar mahaifiyarku ta nuna bata son ganinku a tare damu.

Mahaifiyarku ba mutuniyar kirki bace, kuyi haƙuri ta kama na faɗa muku gaskiya ne, idan kun lura hatta danginta ma babu wanda ya taɓa zuwa gurinku, ko akwai?"

Girgiza kai Sa'ad yayi, ya ce "Ai ta faɗa mana cewa ba a ƙasarnan suke ba" "Hmmm Allah ba gaskiya ta faɗa muku ba, danginta suna can wani ƙauye, da ake ɗaukar hanya ta Zaria, sunan ƙauyen _Kiri_ ƙauye ne
lis, daga can ta gudo nan tayi barikinta mahaifinku ya rufa mata asiri ya aure ta."
  
Kawu Mamman ya ƙara da faɗin "Kakanninku mutanen kirki ne, da mukaje sunyi Allah wadai da ita, da ƙyar suka haƙura aka ɗaura auren, domin ashe bikinta za ayi shine ta gudo tayo kano."

Hanne kukanta ya fito fili, ta riƙa rera shi, suna bata haƙuri, sai da tayi kuka sosai ta share hawayenta.

"Kiyi haƙuri Hannatu, Allah ne ya ƙaddara rayuwarku a haka, kuma ma yanzu idan ta samu lafiya na san zata tuba ta daina hali irin wanda take. Babban dalilin da yasa muka juyawa mahaifiyarku baya shine mun gano cewa ita ce ta kashe ɗan uwanmu kuma mahaifinku saboda  taci gado." miƙewa tsaye Sa'ad yayi, Kawu Bashir ya zaunar dashi yana mai bashi haƙuri.

Dukkansu sunfi mintuna 15 suna kuka, ita tana na fili, yayinda Hannatu ke na zuciya. Sai da suka gama sannan suka roƙi kawunsu ya kaisu garim mahaifiyarsu suga danginsu, yace su shirya zasu tafi a ƙarshen sati.

Aikuwa haka akayi, sunje sun sada zumunci kuma dangi sunji daɗi domin ba'a sansu ba, a dafe sukayi kwana uku kasancewar ƙauyen ƙauye ne, duk da cewar a kano su talakawa ne lis, amma daƙyar suka iya rayuwar wannan ƙauyen.

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang