Page 29

69 13 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email- Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

_Shafin nan gaba ɗaya tukwuici ne ga *Mdme Alhadji MARIE* da *Aisha A Ibrahim* yadda suka damu da nayi typing hakan yayi min daɗi nagode da kulawarku🥰_

NOT EDITED⚠️
'''Shafi na 29'''

*2 weeks later*
Suna zaune su uku a falon Daddy. Ummu, Farhan sai shi Daddy. Babu wanda ke cewa komai, sai da Daddy ya nisa sannan ya fara magana "Abubuwa da yawa sun faru a cikin gidan nan, wasu masu daɗi ne, wasu kuma akasin haka"

Shiru babu wanda ya iya magana, ita Farhan ma kanta na ƙasa taƙi ɗagowa. Daddy ya cigaba da cewa "Ada muna rayuwane mu shidda ahalin wannan gida, a yanzu mun dawo mu uku domin rayuwar Jannat babu wanda ya san zata tashi ko bazata tashi ba." sai a lokacin Ummu tace "Insha Allahu Jannat za ta tashi" "Haka muke fata, Allah yasa" duk suka amsa da "Amin"

"Mun rayu a gidan nan cikin aminci da ƙaunar juna, sai dai kuma, abu ɗaya ne ya saka komai ya wargaje, shine ɗa namiji. Ina so kowa a cikinku ya ɗauki ƙaddara, duk abinda kuka ga ya faru to Allah ya ƙaddara hakan. Farhan" ya kira sunanta. A hankali ta ɗago ta kalleshi ba tare da ta amsa ba. "Ki ɗauki tawakkali kinji, Allah ya ƙaddara haka zata faru, rubutaccen al'amari ne"

A hankali ta ce "Daddy ni dama tuni na haƙura da komai, Allah ya zaɓa min wanda yafi alkhairi, ya kuma bata lafiya" "Amin ya Allsh, Allah yayi miki albarka" "Amin Daddy"

Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Ummu tace "Ya batun zuwan namu India?" "Na saka a nemo mana visa" "Amma sai ta warke zamu dawo ko?" "A'a zamuje muyi dubiya mu dawo domin shi kanshi Khalil ɗin ba shine mai jinya ba kawai yana zaune ne amma asibitin su suke komai" "Allah ya bata lafiya" Farhan ta faɗa sannan ta ƙara da cewa "Daddy baka bamu labarin rasuwar Mommy ba, tunda tare kuke gaba ɗaya a mota.

Ummu ce ta fashe da kuka sosai, ganin haka ne ya saka Daddy ya cewa Farhan ta tashi ta tafi daga baya zasuyi maganar.

Jiki a sanyaye, zuciya cike da mamaki haka Farhan ta tashi tayi side ɗinta tana ta mamaki.

LAS VEGAS

Cikin iko da yardar Allah Jannat na ta samun sauƙi yayinda Khalil ko yaushe yake yini a asibitin, idan ta kama ma har kwana, duk da dai ba ganinta yake ba wani lokacin.

Su Daddy sun kawo masu ziyara bayan sunyi wata guda acan, kwanan su Daddy biyar suka juya Nigeria. Sunji daɗi sosai ganin Jannat ɗin tana samun sauƙi da kuma irin ƙoƙari da Khalil yake a kanta.

NIGERIA

Ta ɓangaren Ahmad kuwa ya shiga cikin gagarin rayuwa, abinci ma da ƙyar yake samu, ga dangi suna nuna halin ko in kula a kansa.

Umma kuwa hauka take tuburan, abin har ya kai an saka mata sarƙa an ɗaɗɗaureta. Sa'ad d Hanne sukan kai mata ziyara, kuma su biyu suke rayuwarsu a gidan, sai dai yanzu dangi sun dawo suna ta masu alheri, basu rasa komai ba. Hanne kuwa har sun mayarda ita day, tana zuwa ta dawo.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau daɗi gobe akasin haka.

*2 Months Later*
NIGERIA

A hankali suka karasa sauka daga jirgi, Jannat tafiya take kamar bata son taka ƙasa. Satin ta biyu da samun sauƙi sannan suka dawo Nigeria amma har wannan loƙacin bata saki ranta ba.

Farhan ce ta fara hangota ta ruga tare da rungumeta. "Alhamdulillah, ƴar uwata ta samu lafiya" su Daddy da Umma suka ƙaraso inda take ta sauke kanta ƙasa sai hawaye.

Daddy bai damu da cewa a airport ne ya rungume ƴarsa tare da saka hannu yana goge mata hawaye. "Ki daina kuka ƴata kinga abinda muke ta fata kenan, kuma alhamdulillah gashi kin dawo gida lafiya.

Khalil ma sannu da zuwa saka masa sannan suka ɗunguma zuwa gida yayinda shi kuma Khalil, Abokinsa Fahad ne yazo ɗaukarsa.

Yana cikin driver ya ɗan kalleshi ya ce "Naga ka rame, ga yanayinka har yanzu kana da damuwa" "To ba dole na rame ba tunda ba daɗi ne ya kaini can ba." "Amma ya jikin nata?" "To da sauƙi zance tunda an samu an mata ciko a zuciyarta, amma fa Jannat ko magana da kyar take tun lokacin da ta dawo cikin hayyacinta shikenan ta zama salihar ƙarfi da yaji, duk da dama ita ɗin ba macece mai son hayaniya ba." "A hankali zata warware insha Allah, rasuwar mahaifiyarta ce na san har yanzu take dukanta, kamata yayi ma su kaita gidanka saboda kai zaka iya shawo kanta ta kwantar da hankalinta" "To ya na iya, ni ai ban isa nace a wuce da ita gidana." "Hakane amma gaskiya naga itama ta ƙara ramewa sosai" "To kai kuwa ciwon zuciya wasa ne" "Allah dai ya bata lafiya." "Amin ya rabbi." har gida ya kaishi. Mommy da Daddy kuwa sunyi murnar ganinsa.

A take kuma Daddyn Khalil ya ɗauki Hajiya Sa'adatu suka wuce gidansu Jannat domin su dubata, shi kuma Khalil mota kawai ya ɗauka ya nufi gidanshi domin yayi wanka ya huta.

Ta ɓangaren Jannat kuwa suna zuwa gida aka ce ta shiga tayi wanka, tayi kuwa bi umarnim nasu tana fitowa taga an fito mata da kaya kan gado. Jikin mirrow ta tsaya amma sam bata kalli kanta ba bare taga rsmar da tayi. Lotion ta shafa sannan ta juya ta ɗauki kayan ta zira a jikinta, ita sam bata sansu ba, amma dai kayan taji daɗin su, gown ce mara nauyi, ta ɗora ɗankwali sannan ta zauna jikin gado.

Duniyar tunani ta nufa, idanunta gaba ɗaya sun ciko da ƙwalla, aka turo ƙofa aka shigo, da sauri ta lumshe ido tana mayar da hawayen.

Farhan ce da Ummu. Farhan tana riƙe da Baby girl ɗinta. Ƴar wata 3. Kayan jikinta irin na Jannat, ashe ita tazo ta ajje mata sukayi anko. Ummu ta zauna kusa da Jannat yayinda Farhan take a tsaye.

"Jannat dan Allah kiyi haƙuri ki bar tunani kinga da ƙyar aka ceto rayuwarki" "Ban so hakan ba naso ace na mutu" ta faɗa tana kallon ƙasa ko kaɗan taƙi haɗa ido dasu. Ummu ta cigaba da cewa "Mutuwa tana kan kowa, domin babu wanda zai tsallake lokacinsa, Jannat ki daina wannan furuci kada ki zamto ɗaya daga cikin wanda zasu faɗi jarabawar da Allah yayi musu" sai a lokacin hawayen suka zubo, ta saka hannu ta goge.

Farhan fashewa tayi da kuka sannan ta fita daga ɗakin da sauri. Ummu ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Kin ga ƴar uwarki ma kukan take, da ace kin saki ranki itama haka, dan Allah Jannat kiyi tawakkali." Na rasa jinina, bayan rasa Safina da nayi sai gashi a ɗsn ƙaramin lokaci, itama Mommy na rasata, na rasa gata na a rayuwa"
"Nayi miki alƙawarin zan maye miki gurbin da kika rasa na mahaifiya" Umma ta faɗa tare da fashewa da kuka. A lokacin aka ƙara turo ƙofa aka shigo.

"Subhanallah haba Hajiya Bilkisu yanzu dake da ita sai ku zauna kuyi ta kuka, naga alama so kuke ku ƙara mata wani ciwon ko" Daddy ya faɗa lokacin daya shigo tare da su Alhaji Auwal.

Ummu dai bata ce komai ba ta tashi ta fita. Hajiya Sa'adatu ta zauna kusa da Jannat ɗin. A sanyaye Jannat ta gaishesu. Daddy da Alhaji Auwal suna zaune kan sofa.

Nasiha sosai suka haɗu suka yi mata. Sun ɗan daɗe sosai sannan suka tashi suka fita. Mutane kuwa dangi sai zuwa ake ana dubata.

Suna fita Alhaji Auwal ya bawa Daddy shawarar akai Jannat ɗakin mijinta domin ya san Khalil ba zai zauna suyi ta kuka tare ba dole zai rarrasheta.

Daddy kuwa ya ce ba matsala insha Allah ko zuwa gobe ne sai a kaita idan yaso ƴan dubiya sai suje can kawai.

*Ƙaranci comments ɗinku shi yaja komai, duk da cewar ina busy amma da ina samun haɗin kanku sosai da ko babu readmore zan daure in ƙarasa maku pages biyu da suka rage. To ku sambaɗo comments in sambaɗa maku zazzafan last page*

*Masu Comments ina godiya sosai, Sanaz ta dawo.*

Kuyi Following ɗina a Wattpad @SaNaz_deeyah
Kuyi Subscribe na youtube channel ɗinmu
SANAZ NOVELS TV

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Where stories live. Discover now