*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email- Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 30'''
Not Edited
🔚*Washe Gari*
Tun ƙarfe goma na safe aka kai Jannat gidan Khalil. Sam batayi kukan rabuwa da gida ba domin kuwa bata da wanda za tayi kukan rashinsa a cikinsu.
Farhan dai bata je ba, sai dai 'ƴan uwa ana ta zuwa. Aunty Mammy kuwa ita ta zauna ta shirya mata komai. Sai bayan sallar Isha'i sannan suka tafi.
Tana zaune shiru ita kaɗai a gidan, sai after 10 sannan Khalil da Fahad suka shigo gidan, Fahad na riƙe da leda a hannunsa na kajin amarci.
Tana jin shigowarsu kuwa taja gyalenta ta rufe fuska, idanunta cije da hawaye. A kusa da ita Khalil ya zauna, yayinda Fahad ya zauna a gefen Khalil.
"To Alhamdulillah yau dai buri ya cika, masoya suna zaune a inuwa ɗaya. Ni dai nasihar da zan muku itace ku sani cewa rayuwar da ake a waje ba ita ake a cikin gida ba, zaman haƙuri ake, kai Khalil kaine babba duk abinda tayi ba dai-dai ba kaine za ka tsawatar mata, ka nuna mata kuskurenta ta hanyar nasiha. Ke kuma Jannat, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki saka a ranki zakiyi bautar ubangiji ne, domin ko da soyayya dole wata rana sai kun samu saɓani, Allah ya dawwamar da farin ciki tsakaninku ya kuma baku zuri'a ɗayyiba." Khalil ya amsa da "Amin" Yayinda ita kuma Jannat tayi shiru."
Miƙewa tsaye yayi, tare cewa "To zan wuce, Allah ya baku zaman lafiya" Khalil zai miƙe tsaye sannan ya ce "Muje na taka maka" "A'a ka barshi ka da a barta ita kaɗai" "Karka damu, bakin mota zan raka ka" "Okay." zan kalli Jannat ya ce "To Jannat, sai na ƙara leƙowa." zai wuce shi kuma Khalil ya bi shi a baya.
Yana dawowa anan inda ya barta ya tarar da ita, still mayafinta a rufe da fuskarta. Kusa da ita zai zauna sannan ya ce "Matata ki buɗe min fuskar ta ki, yanzu dai daga ni sai ke a gidan" ƙin buɗewa tayi har sai da ya saka hannu ya buɗe mata fuskar. Mayar da fƴskarshi yayi kalar tausayi tare da cewa "Hawaye...! Ya nake ganin hawaye a idanunki Jannat, wannan fa ranar farin ciki ce, bai kamata ba" rinannun idanuwanta ta ɗago ta kalleshi dasu "Yaya Khalil, ina jin nauyin abinda nayi, na auri mijin ƙanwata, na tabbatar Farhan yau ba zata iya bacci ba." dafe goshi yayi sannan ya kalleta. "Komai da kike gani a rayuwa to ki sani rubutaccen al'amari ne, dan haka kiyi haƙuri ki rungumi ƙaɗdara, Jannat wallahi ina ji a jikina ba zan iya rayuwa ba tare dake ba, shiyasa na kasa jure halin da kike ciki, gani nake idan bani ba babu wanda zai iya miki kyakykyawan ruƙo" zsi kai gwiwonsa ƙasa yana kallonta da rinannun idanunsa. "Na san bakya sona, amma hakan ba zai hanani baki kyakykyawar kulawa ba, dan Allah ki aminta dank, zan kuma baki dama, ba zan taɓa miki dole ba. Dan haka mu'amular aure ba za ta taɓa shiga tsakaninmu har sai da amincewarki" zai miƙe tsaye, ita kuma sam taƙi ta ƙara haɗa ido dashi. "Jannat zan tafi na kwanta, ka da ki manta kuyi nafila ko da raka'a viyu ne kafin ka kwanta, ga abinci nan ki ci."
Juyawa yayi ya fara tafiya, da sauri ta tashi tare da shan gabanshi. Kallon-kallo suka tsaya kafin ta sake fashewa da kuka. "Ina sonka Yaya Khalil" shine kawai abinda bakinta ya iya furtawa shima cikin kuka. Rungumota yayi jikinsa, ji tayi gaba ɗaya tsigar jikinta ta tahi, taji wani abu ya tsireta tun daga babban yatsa har zuwa ƙwaƙwalwa.
Wanka ya saka tayi tsre da alwallah, shima yayi hakan, sannan sukayi nafila, sai daya shafa goshinta yayi mata addu'o'i sosai, sannan ya jawo ledar kaza da kayan maƙulashe, sai shine ya riƙa bata tana noƙewa a haka har ta ƙoshi, sannan suka hau gado, ita ta fara kwanciya ta juya masa baya, shi a lokacin ma bai kwanta ba.
03:00am
Juyi tayi ta buɗe ido, ganin baya kwance ya saka ta tashi zaune, tsaye ta ganshi ya jingina bayanshi da bango kai a sama alamar yana tunani, murtsuke idanunta tayi sannan ta masa magana taji bai amsa ba. Sauka tayi daga gadon ta ƙara gabanshi tana kallonshi "Yaya Khalil..." nan ma shiru ba amsa.
Hannu ta kai ta dafa kafaɗarsa, a ɗan tsorace ya juyo yana kallonta. "Tunanin me kake haka?" ta ƙarasa faɗa tana kallon agogo kafin ta mayar da kallonta gareshi. "Me ya tasheki? Bana so kiyi ciwon kai please ki koma ki kwanta." Hannu ta saka ta rufe bakinta dan kar kukan ta ya fito fili. "Me kuma ya faru? Ko mafarki kikayi?" kallonshi kawai take yana ƙara bata tausayi, hannunsa ta fara riƙewa sannan ta rungumeshi.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sake faɗin "Meya faru dake Jannat" "Ina sonka, ni matarka ce, bazan taɓa tauye maka duk wani haƙƙinka da yake kaina"
Rungumeta ya ƙarayi cikin jindaɗi kalamanta, ɗaukarta yayi ya kwantar da ita a kan gado sannan ya kwanta tare da kashe fitila.
****
"Daddy please" Farhan ta faɗa, tana zaune a kan carpet, idanunta na kallon ƙasa. Ajiyar zuciya Dady ya sauke sannan ya ce "Farhan na san dama dole za kiji wani iri, amma ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara, kuma ni nafiso ki zauna anan ki ƙarasa karatunki saboda ki samu miji kiyi aure" hawaye ta goge sannan ta miƙe ta bar falon.
Ummu ce tayi ta tausar zuciyarta har ta samu ta warware.
Ta ɓangaren Khalil da Jannat soyayya soyayya suke sha kamar babu abinda ya taɓa shiga tsakaninsu. Yayinda Farhan ta manta komai har takan je gidan ta yini, wani lokacin ma ta kai ƴar ta baro ta.
A haka dai suka fara soyayya da wani Muktar wanda shima matarsa ta rasu ta bar masa ƴa ɗaya, ba'a wani ɗauki lokaci ba aka fara shirye-shiryen biki.
Ta ɓangaren Sa'ad kuwa daga shi sai Hanne suke rayuwa a gidan, domin Umma kam hauka tuburan ba alamar samun sauƙi kusa. Sai dai a yanzu dangi na matuƙar ƙaunarsu suna kuma kula dasu yadda ya kamata.
Ahmad kuwa rayuwa ta masa zafi, ya nemi komai ya rasa, abinci ma da ƙyar yake samu, dan ma Salim bai yada shi ba. Haka yayi ta istigfari yana neman gafara wajen Allah.
Bayan Shekara biyu
Jannat ta haifo ƴarta mace aka mayar da sunan Mommy, lokacin kuwa Little Safina ta dawo hannunta saboda Farhan tayi aure.
Daga ita har Farhan rayuwar farin ciki suka cigaba dayi gwanin sha'awa.
*Alhamdullillah, anan gaɓar na kawo ƙarshen wannan littafi mai suna a ƙasa*
Note: Kasancewar labarin ya ɗan jima ba'ayi posting ba, kasancewar abubuwan sun ɗan min yawa, wannan dalili ne ya saka na ƙarƙare labarin domin duk ya fita a kanku
_Ina tafe da wani zazzafan littafi ma suna *SARƘAƘIYA* ko daga jin sunan kusan akwai ƙalubale a cikinsa, kuma yaci sunan nashi, ku dai ku kasance dani, ta hanyar yin following ɗina a Wattpad@SaNaz_deeyah da kuma youtube *@SANAZ NOVELS TV* Littafin Sarƙaƙiya littafine da zaku riƙa samun update kullum da yardar Allah ba wata gargarda, ku dai ku kasance dani, zaizo maku nan bada jimawa ba._
A ƙarshe ina mai tura ɗumbin saƙon yabo da kuma godiya ga Karamci Writers da kuma ɗumbin masoyana masu bibiyar littattafaina a koda yaushe, ina ƙaunarku🥰🥰

YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...