Page1

4 1 0
                                    

_*JUHAINA*_

_*historical theme*_

_*Ummufatima*_

*BISMILLAHIR RAHMAN ARRAHIM*

_*tsokaci*_

*Idan wannan labari yayi kama da na ka/ki ba da niyya bane, labarin abubuawa ne wanda suka daɗe suna damun mu ne na cikin masaurata, ba kuma nayi bane don cin fuska ko da wata manufa ba. Wasu ɓangarorin labarin ya faru a gaske.*

*_free pages 1_*

Shekara ta 1980.....

Iskace me sanyin gaske take kaɗawa yayin da shukokin da ke cikin gonakin ke ta yawo kamar za su fito daga cikin ƙasa saboda yanayin ƙarfin iskar da alama guguwar damuna ce sannan kuma abun ya haɗu harda sanyin asuba wanda gari yake dabb da wayewa.

Wani mutumi dogo me murɗaɗɗan jiki sannan kuma me ɗan hasken fata na hango ya ɓullo daga cikin wata gona a guje yana riƙe da hannun wani yaro wanda aƙalla zaiyi shekara 15zuwa16 a duniya suna sanye da wasu fararen kaya riga da wando wanda suka yi duƙun2 daga gani sun shawo tafiya koma daga ina suke kuma gudun rai suke yi, daga bayan su kuma na hango wata mata me duhun fata riƙe da hannun wata yarinya wanda baza ta wuce shekara 10 ba a duniya. daga ganin matar kyakkyawa ce sai dai yanayin da suke ciki na wahala ya ɓoye kyaun nata.

Yarinyar da ta gaji matuƙa ga ƙishin ruwa ga yunwa ce ta tsaya tare da fuzge hannunta a cikin na mamanta tace"Mama na gaji da wannan gudun da muke yi ni ruwa zan sha, wai ina zaku kaimu ne? Me yasa muke gudu?"

Duk ta jerowa mmn nasu tambaya a lokaci guda.

Mutumin da yake ɗan gaba da su ne ya juyo ya tsaya yana kallon su, sai kuma ya dawo baya da sauri ya ƙaraso wajen ya kama hannun yarinyar yace" Mama na kiyi haƙuri, kiyi hakuri kinji ko gudun rai muke yi kashe mu za su yi, ki daure kinji ko, mu dan ƙara gaba zamu samu ruwa sai ki sha ko? "

Noƙe mai kafaɗa tayi alamun ita baza ta cigaba da tafiya ba, mamance ta sunkuyo daidai saitin fuskarta tace" JUHAINA!, kiyi haƙuri mana, kin ga babanki hannun shi akwai ciwo ni kuma bazan iya ɗaukan ki ba ballantana kuma yayan k....

Bata ƙarasa faɗan abunda za ta faɗa ba suka hango hasken fitilu alama masu bin nasu suna gab da cin musu.

Ai da sauri baban ya ɗauki yarinyar ya saɓa suka cigaba da gudu yayin da mmn ta riƙe hannun namijin ta bi su a baya, suna cikin wannan gudun suka iso gabda wani tsauni a lokacin gari yayi haske sosai.

Matar ce ta kalli mutumin tace"Baban su yanzu ya zamuyi za su cimmana
fa? "

Ɗan shiru yayi yana tunani kafun yace" Mu haƙura kawai mu nemi inda zamu ɓoye yaran nan in yaso mu sai mu tsaya a kashe mu kowa ma ya huta ba shikenan ba,hankalin gimbiya bilkisu zai fi kwanciya".

Hawaye ne ya silalo daga idon matar tayi saurin goge shi tace"To shikenan baban Juhaina, haka tamu ƙadarar tazo mana".

Cikin wasu ƴan ciyayi ya shiga ya ajiye yarinyar yace mata"Juhaina ke ƙaramar yarinya ce ba abunda kika sani, duk abunda zaki gani yau kada kiyi ihu ko kuka kinji ko kiyi shiru idan ba haka ba kema kashe ki zasu yi, Allah yayi miki albarka, Allah ya raya mun ke ya albarkaci rayuwar ki".

ɗaga mai kai tayi ba tare da tace komai ba ya dawo yazo ya kama hannun namijin da niyyar ya neman masa wajen ɓuya saboda baya so ya haɗa su koda za a gano ɗaya kada a gane ɗaya.

Suna cikin haka sai ga wasu mutane su uku sun ɓullo suna sanye da jajayen kaya da ratsin shuɗi a jiki, dukkan su hannayen su riƙe da dogayen wuƙaƙe masu kama da adduna.

Salati kawai mutumin ya zabga haɗe da rungume yaron a jikin shi sannan ya janyo matar itama zuwa jikin shi.

Ɗaya daga cikin mutanen da babu alamar tausayi ko annuri a fuskar shi ne yace"kai waziri har kaine zaka gujewa umarnin gimbiya ka bamu wahala, to wallahi kaima sai mun aika ka inda muka aika gimbiya Asma'u".

JUHAINAWhere stories live. Discover now