_*JUHAINA*_
_*historical theme*_
_*ummufatima*_
_*free pages*_
_*2*_
Ai bata bari jakadiya ta ƙara faɗan kalma koda guda bace tayi sauri tabi ta gefanta ta wuce, har ɗan sauri sauri take.
Shashin nasu ta shiga daga bakin ƙofa naga wani saurayi wanda a ƙalla zai yi shekara 16 a duniya ya taho da sauri ya rungume ta yace "Ammi Alhamdulillahi yayan mu ya tashi".
Ɗan murmushi tayi ta shafa kan shi sannan tace "Labari ya isar mun shiyasa nazo ma don na ganshi, yanzu dai hankalin ka ya kwanta ko ABDUSSAMAD daman na faɗa maka ba abunda zai samu ɗan uwanka da yardar Allah zai farka"
Murmushi yayi sai kuma ya kama hannun ta yace"Muje, kinji daɗin da naji kuwa Ammi, Allah sarki umma tana ta cewa ya tashi ya tashi, gashi yau dai ya farka amman bata raye".
Kallon shi tayi da kyau sai kuma ta ɗauke kai, saboda tausayin yaron da taji, koma dai menene ta aikata tasan saboda ƴaƴanta ne kuma Takawa shi yaja komai, ita kuwa koma menene indai akan Abdula'ziz da Abduljalal ne to zata iya yin komai ma, amman ta ɗaukarwa uwar su alƙawarin kula da su batare da nuna banbanci ba kuma in Allah ya yarda zata cika alƙawarin da ta ɗauka.
Tana cikin wannan tunanin suka ƙaraso cikin sashin nasu inda ɗakunan su suke, ɗakuna ne guda biyu a jere na farkon suka buɗe suka shiga, bayin da suke ciki ne suna ta mai fifita sukayi saurin zubewa suna kwasar gaisuwa ganin gimbiya ta shigo.
Ɗaga musu hannu kawai tayi haɗe da nuna musu ƙofa.
Sanin abunda take nufi ne yasa sukayi saurin ajiye mufitan da ke hannun su suka fita sim sim ba tare da ko ƙara kallon inda take ba, saboda kaf bayin gidan babu wanda baya shakkar ta.
A hankali ta zauna a bakin gadon tana riƙo hannun shi sai kuma ta ɗau mafici ɗaya ta cigaba da mai fifita.
Jin kamar ɗumin hannun Ammin shi cikin hannun shi yasa yayi saurin juyowa yana fuskantar ta.
Masha Allahu nace dumin kyakkyawa ne sosai sannan kuma kana ganin shi kasan itace ta haife shi yanayin fatar su da kuma idon shi, hancin ne dai ya banbanta ba irin nata ba wanda ne tunin irin na takawa ne, shima fatar shi ba mai duhu bace kuma ba me haske bace, fuskarshi tayi wasai irin na marasa lafiyar nan.
Ɗan murmushi yayi yana ƙara damƙe hannun ta a cikin nasa, yadda yake kallonta itama haka take kallon shi.
"Ammi na". Ya kira sunan ta.
"Na'am shalele na".
Ƙara matsota yayi sai kuma yace "Naga kamar kin ƙara tsufa kwana na nawa ne a kwance?"
Kanshi ta ɗan duka sannan tace "Ohhh mutum yanzu ya gama tsallake suraɗin mutuwa amman har yanzu hali yana nan,Allah ya maka albarka daman nasan zaka samu lafiya nasan ba yanzu zaka mutu ba".
Murmushi ya ƙara yi sai ya juya ya kalli Abdussamad, duk da yana da wasa amman be cika son yawan magana ba.
Taɓe baki yayi sai kuma yace "Kai baka faɗawa Umma na tashi bane? Ban ganta ba nasan ma da ta sani sai ta riga Ammi zuwa ta ganni".
Ɗakin ne ya ɗau shiru kamar ruwa ya cinye su.
Sake maimata abunda ya faɗa yayi idon shi na kan Abdussamad ɗin.
Ƙwallace ta cikawa Abdul ido, ganin hakan yasa Abduljalal ƙoƙarin tashi don yasan ɗan uwanshi ba komai ne yake sashi kuka ba, hasali ma duk cikin su shine baida saurin kuka.
Ganin yana ƙoƙarin tashi yasa gimbiya tayi saurin temaka mai don tasan ko ta hana shi ma bazai hanu ba.
Kallon Ammin tasu yayi sannan ya ƙara dawo da kallon shi kan Abdul yace"Me ya samu Umma iyeee Abdussamad!? "
YOU ARE READING
JUHAINA
Historical FictionLabari ne akan wata yarinya da ta rasa iyayen ta a sanadiyyar wata masaurata, wanda daga baya ta gano maman masoyita da tun tana ƙarama itace sanadin komai. To ku biyo ni kuji yadda zata kaya a cikin wannan labari...