Page3

2 1 0
                                    

_*JUHAINA*_

_*historical theme*_

_*Ummufatima*_

_*free pages*_

_*3*_

Wani ɓangare ne me faɗin gaske, kana ganin gurin kasan anyi shekara da shekaru ba ayi amfani da shi ba. wata ƙatuwar bishiya ce a tsakiyar gurin, sai daga gefe kuma wasu ƴan shukoki ne da basu da yawa, kana ganin gurin dai kasan a shekarun baya an shuka furanni a wajen.

Wani dogon matashi na hango daga can gefe ya tsaya yana ta kallon farfajiyar gurin kamar kar ya dena kallo, daga bayan shi kuma wani bawa ne wanda nake tsammanin shi yake mai jagora. Sai da na matsa kusa sosai, sai naga ma ashe  Jalaludin ne yake tsaye a gurin, sai dai fa yanzun ya ƙara kyau sosai sannan kuma jikin shi ya murje ƙirjinshi yayi faɗi sosai kana ganin shi dai kasan matashi ne me jini a jika.

Bawan dake bayanshi ne ya ɗan matso kusa da shi sai alokacin ma naga ashe Sulaiman ne,shima ya girma sosai ya ƙara kyau kamar ba shi ba.

Ɗan kallon Abduljalal yayi yana rusunar da kai sannan yace"Ranka ya daɗe lokaci fa ya tafi da yawa ya kamata ace mu koma cikin Fada kasan yau akwai taro".

Ɗan lumshe idon shi yayi sai kuma ya buɗe yana ƙara kallon gurin kafin yace"Muje".

Juyowa yayi yana tafiyar ƙasaita kana ganin shi kasan ɗan sarki ne kuma jikan sarki, yasha rawani abun shi ga kayan jikin shi sunyi mai kyau sosai, hannun shi yana baya yana tafiya ɗaiɗai kamar bazai taka ƙasa ba.

Abunda yake cin shi a cikin rai ne ya kasa ɓoye shi sai da ya furtawa Sulaiman"Yanzu shikenan na rasa Ukteyy bazan ƙara ganin ta ba Sulaiman?".ya jefo mai tambayar a bazata yana cigaba da tafiya abunshi.

Sulaiman ne ya ɗago kai ya kalle  shi yana cigaba da bun bayan shi sannan  yace"Ranka ya daɗe ya kamata ace zuwa yanzun ka manta da ita, ka ga dai har yanzu ba ita ba alamun ta kuma  itama an tabbatar da cewa ta mutu tunda aka tsinci kallabinta a kusa da wannan tsaunin hakan ya tabbatar da faɗawa sukayi cikin wannan rafin ita da ragowar ahalin ta".

Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke ba tare da Sulaiman ɗin ya gani ba, shi kanshi yana jin babu ita a duniyar nan amman har yanzun zuciyar shi ta kasa yarda da hakan gani yake kamar wata rana idan yaje wajen zai ganta.

"Kasan me Sulaiman?"
Y faɗa cikin sanyin murya.

"Aa sai ka faɗa ranka ya daɗe".

Idon shi ne yayi ja, yana ƙara tuna irin kisan da akayiwa Waziri sannan yace"Har yanzun ina dana sanin rashin sanar mata da koni waye, duk kuwa da bata da wayo sosai a lokacin, amman nasan da zata riƙe hakan".

Sulaiman ne ya ɗan girgiza kai yana kallon uban gidan nashi wanda kullum tausayi yake bashi sannan  yace"Tun a lokacin na faɗa maka ka sanar da ita ko kai waye amman kace mun ba yanzun ba sai ta ƙara hankali".

Shiru yayi ba tare da ya ƙara cewa Sulaiman komai ba har suka ƙaraso cikin gida, sashin shi suka wuce direct yana zuwa Sulaiman ya temaka mai ya shiriya shi cikin wasu kaya masu kyaun gaske yasha rawanin shi fuskakar nan tashi tayi kyau tayi sayau kamar wanda bashi da wata matsala.

Suna fitowa daga cikin ɓangaren nashi bayin da suke jiran su maza da mata a ƙalla sun kai su 8 suka fara take mai baya, tafiya yake kamar be son ya taka ƙasa, duk inda suka wuce sai an ɗago kai an kalle shi ko wace baiwa kuwa da irin abunda take saƙawa a ranta akan shi saboda bayin da suke son shi a cikin masarautar Allah yayi yawa da su.

Taron nasu iya na dangin sarki ne don haka kowa ya hallar shi kaɗai ake jira kawai, gashi taron akanshi ne.

Yana dosowa cikin fada aka fara gaishe shi ana mai kirari nan aka fara sanar da shigowar shi zuwa cikin fadar sarkin.

JUHAINAWhere stories live. Discover now