_*JUHAINA*_
_*Ummufatima*_
_*free pages 4*_
Wasu kalan hawaye ne suke zubowa daga idon Fulani yayin da daga gefe guda kuma take haɗa zufa wanda ita kanta bata san na mene ba, cikin second ɗaya taji gaba ɗaya jikin ta yayi wani kalan bikircewa, cikin ta ya ƙulle yayinda kanta ya ɗauki wani masifaffen ciwo, shi kuwa Abduljalal da yake kallon ƙanwar tashi kafun yakai ga buɗe bakin shi yayi magana yaga yanayin ta ya sauya cikin second guda, hakanne yasa yayi saurin zame hannun shi da ke cikin nata wanda har yanzu be dena zubar da jini ba,kafun ya kai ga yin wani abu ma, sai amai, wani kalan amai ta fara yi kamar zata fitar da duka hanjin cikin ta hakanne yasa yayi wani irin girgizata haɗe da kiran sunan ta"Zuwairaa! Ke Zuwaira!! "kiran sunan ta kawai Abdul yake haɗe da girgizata wanda hakan ya ɗagawa kowa hankali dake cikin fadar, da sauri Zulaikha ta matso itama kusa da su tana kiran sunan ta," Ranki ya daɗe me ya same ki? ". Amman ina Zuwairaa ma bata san me suke faɗi ba domin kuwa zuwa yanzun har ta fara fita daga hayyacin ta, wani irin aman jini da ga kwaro yasa har Takawa dake zaune akan kujera sai da ya miƙe yana takowa gurin.
Ita kuwa Zulaikha ƙara ruɗewa tayi tana sakin kuka sai kace wata yarinya tana diririta ƙafa haɗe da yarfa hannu tana faɗin"Wayyo Allah na na shiga uku sun kashe ta, shikenan sun kashe ta".
Shi kuwa Abdul ganin tana aman jini yasa be wani tsaya ƙara ɓata wani lokaci ba ya sungumeta sai cikin gida, hanyar sashin su ya nufa da ita hakanne yasa gaba ɗaya masarautar ta ɗauka, Gimbiya Bilkisu da Hafsa wanda suka wuce tun lokacin da sarki ya bada umarni ne suka fito daga ɓangaren su hankali su a mugun tashe jin wannan labari mara daɗi.
Shi kuwa Abdul yana shiga sashin su direct ɗakin Abdussamad ya nufa da ita, yana shiga ya kwantar da ita akan gadon dake ɗakin, da gudu ya nufi ɗakin shi ya ɗakko wata gora wanda ruwan magani ke jiƙe a ciki sake dawowa ɗakin yayi ya bata maganin ta sha wanda a lokacin ta riga da ta gama galabaita, ai kam yana bata maganin sai gashi tayi wani kalan amai, wanda n kasa gane wani iri ne, abinci ne haɗe da jini, majina babu abunda babu dai.
Ita kuwa Zulaikha da take daga waje ƙwalla take zubarwa kawai tana jika ka dawo a bakin gurin. ragowar bayin kuma suna tsaye suna kallon ta cikin tausayi don sun san ta shiga uku tunda itace me kula da ita, ita za a fara tuhuma akan komai kafun kowa.
Suna cikin wannan yanayin sai ga Gimbiya ta shigo hankalin ta a mugun tashe, ji take kamar zuciyar ta zata faɗo ƙasa saboda tsabar tsoron karta rasa Zuwairaa dumon kuwa sunyi wata irin shaƙuwa wanda bazan iya faɗa muku ba, itama Hafsat da take biye da ita hankalin ta a tashe yake amman dai babu wata damuwa ainun akan fuskar ta.
Basu damu da gaisuwar da bayin ke zambaɗa musu ba, saima wucewa da sukayi kamar bada su ake ba.
Gimbiya na shiga ɗakin tayi kan gadon tana kiran Sunan Zuwairaa.
"Auta na! Me ya faru dake? Me ya sa me ki haka iyee!" ta ƙare maganar ƙwalla na zubo mata.
Ita kuwa Zuwairaa tsabar tsananin ciwon da take ciki bata iya bawa Ammin nasu amsa ba saima lumshe idon ta da tayi.
Sanin baza ta samu amsa daga wajen ta ba yasa ta juyo ta kalli Abduljalal, cikin tashin hankli tace" Lafiyar yarinya na ƙalau da na fito daga cikin Fada me ya ƙara faruwa kuma? Ko daman an haɗa wannan gadar zaren ne don a ga bayan ku gaba ɗayan ku, iyee Abduljalal".
Ɗan shiru yayi kamar bazai yi magana ba, sai kuma yace"Ina tunanin hakan Ammi domin kuwa wannan aikin guba ne, kuma ina da tabbacin cewa a cikin abinci aka zuba mata, yanzu dai kafin wannan na bata ruwan itacuwan nan ya fitar da gubar amman ba haka yana nufin ta fita daga haɗari bane, don haka sai an samo me magani yazo ya ƙara duba ta da kyau".
YOU ARE READING
JUHAINA
Historical FictionLabari ne akan wata yarinya da ta rasa iyayen ta a sanadiyyar wata masaurata, wanda daga baya ta gano maman masoyita da tun tana ƙarama itace sanadin komai. To ku biyo ni kuji yadda zata kaya a cikin wannan labari...