_*JUHAINA*_
_*Ummufatima*_
_*free pages 6*_
Babu wani ɓata lokaci Sulaiman yasa aka fitar da gawakin don a binne su.
Ita kuwa Zulaikha sata yayi a gaba zuwa ɓangaren dawakai inda yasa aka kira mai wasu wainda suke kula da cikin gida don su ɗaure Zulaikha a jikin wani itace. Tunda suka iso wajen take kuka tana ranstuwar bata da hannu ko ɗaya a cikin abunda ya faru, amman ina Sulaiman yaƙi sauraron ta duk kuwa da yana jin tausayin ta kuma sam jikin shi bai bashi tana da hannu a cikin abunda ya faru ba, domun kuwa da tana da hannu da duk tare za su haɗu su kashe kansu saboda kar su faɗi wani abun, amman ba yadda zaiyi haka nan zai cika umarnin Galadima.
Kawar da kanshi kawai yayi ya basu umarnin ɗaure ta, tana ihu tana tuma a ƙasa haka suka kama ta suka ɗaure ta a jikin itaciyar, nan dakarin ya zo ya fara zuba mata bulalar yana faɗin"Ki faɗi gaskiyar lamari ko ki mutu da duka".
Ita kuwa Zulaikha tunda ya zuba mata ɗaya ta saki wani ihu saboda tsabar azaba, tunda take a rayuwar ta bata taɓa jin abu makamancin haka ba, ko da take yarinya ta san sun sha wahala amman duk wahalar da tasha bata kai zafin wannan bulalar ba.
Bulalar da ya zuba mata ta biyar ce yasa tace"Wallahi wallahi, bani bace, don Allah ka yarda dani, Allah kuwa ban san komai ba, hasali ma ba ni da buri illa na in kula da Fulani, don Allah ku mun rai, ku barni in cika buri na kafun na mutu na roƙe ku".
Sulaiman kuwa lumshe idanun shi yayi yana jin tausayin ta yana ratsa mai zuciya shi yanzun ya zaiyi? ya zama dole ya cika umarnin nan da aka bashi idan ba haka ba shi zai shiga matsala,haka ya cigaba da jin yadda take kuka amman ba shi da yadda zai yi. Jin anyi mata bulala ta 15 amman bata bada alamar bayani ba, gashi kuma ta fara laushi don kukan ma baya fita da kyau, hakanne yasa ya yanke shawarar tsayar da dakarin da yake dukun ta.
Yana gab da buɗe bakin shi tace"Wallahi indai zaku barni kuma don ku yarda dani na ɗau alƙawarin nemo wanda ya aikata wannan abun indai har yana cikin masarautar nan".
Habawa jin tayi wannan furucin Sulaiman ko second guda be ƙara ba kuma ba tare da bawa bayin da suke wajen umarnin kunce ta ba ya ƙarasa da gudu ya kwance ta a jikin itaciyar, ai kuwa yana kwance ta ta zube a ƙasa sharab.
Cikin sauri ya ce" ku ɗauke ta ku kaita ɓangaren bayi, a kira likitan cikin gida ya duba ta.
Yadda ya basu umarni ko minti ɗaya basu ƙara ba su kayi kama kama don kaita ɓangaren bayin.
Shi kuwa Sulaiman cikin sauri harda gudu2 ya iso ɓangaren Abduljalal inda ya tafi ya barshi a nan yazo ya same shi, da sallama ya shiga cikin wajen yana shiga ya zube a ƙasa yace"Nazo maka da labari me daɗi raka ya daɗe.
Abdul ne ya ƙure Sulaiman da ido yana jiran ƙarin baya ni yace"Inajin ka, tayi bayani ko? "ya ƙarashe maganar cikin ƙaguwa da jin abunda ya faru".
Sulaiman ne ya ɗan ƙara sunkuyar da kanshi ƙasa sannan yace"A'a ranka ya daɗe sai dai tayi furuci wanda yake gab da kaimu ga nasara".
Ɗan yatsena fuska Abdul yayi yana ɗaga girarshi guda ɗaga haɗe da sake gyara zaman shi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya koma bayan kujrar da yake zaune ya ɗan kwanta sannan yace"Wani irin Furuci kenan Sulaiman ".
Cikin ƙara rusunar da kanshi ƙasa yace" Eh to, ta ɗauki alƙwarin nemo wanda ya aikata wannan lefin indai yana cikin wannan masarautar, jin ta faɗi haka yasa na sa aka sassauta mata hukuncin ta sannan nace a kira likitan cikin gida ya bata magani".
Ɗan ƙurawa Sulaiman ido yayi yana mamakin abunda ya gama faɗa yanzu, idan banda abun Sulaiman suma kansu suna tunanin nemo mafita sun kasa samu cikin sauƙi ballantana kuma wata Baiwa, Baiwar ma kuma da basu gama yarda da ita ba.
YOU ARE READING
JUHAINA
Historical FictionLabari ne akan wata yarinya da ta rasa iyayen ta a sanadiyyar wata masaurata, wanda daga baya ta gano maman masoyita da tun tana ƙarama itace sanadin komai. To ku biyo ni kuji yadda zata kaya a cikin wannan labari...