_*JUHAINA*_
_*Ummufatima*_
_*free pages 7*_
Zulaikha ta ɗan yi tafiya a ƙalla na minti talatin kafun ta isa inda zata je, sai da ta jiƙe sharkaf sannan ta iso bakin wani gida ai kam bata tsaya ɓata lokaci ba ta shige cikin gidan da gudu tana kiran sunan "Inna! Inna! Kina ina ki fito ki temake ni na jiƙe sharkaf, yau ruwan garin nan gaba ɗaya a kai na ya ƙare".
Matar da take zaune tayi tagumi daga gani tunani take, jin muryar Zulaikha yasa ta zabura da sauri kamar daman ita take jira, cikin farin ciki da jin daɗi ta yo ƙofar ɗakin tana faɗin"Muryar wa nake ji a gidan nan ko sallama babu? "
Zulaikha na gab da ƙarasowa bakin ɗakin matar ta fito daga cikin ɗakin, ganin matar yasa Zulaikha tayi wani tsalle ta rungume ta" Oyoyo Inna na, nayi kewar ki kwana biyu wallahi".
Ita kuwa Inna jin sanyi yasa tace"Ka ga ja'irar yarinya, so kike nima sai kin jiƙa mun jiki kamar yadda kika jiƙe"ta ƙarashe maganar suna shiga cikin ɗakin a tare, suna shiga Zulaikha tace "kai inna sanyi ki bani wani kayan in canza".
Inna ce ta ɓalla mata harara irin na wasan nan, sannan tace "Lallai ma yarinyar nan kayana tsaranki ne da zaki ce in dakko miki ki saka?"
Cikin zumɓura baki da shagwaɓa tace"Ni gaskiya inna idan baki son gani na ne ki faɗa mun kawai in tafi, a bani kaya in canza shine ake mun wani yanga".
Inna ce ta buɗe baki tana kallon ta sannan tace"Au iyeee, lallai ma yarinyar nan wuyanki ya isa yanka, toh sai ki biyo ni ko, idan kuma a nan zaki canza kayan toh sai in sani".
Dan kallon innan tayi sannan ta tashi ta bita, tana shiga dakin ta tarar da inna har ta buɗe Cabot ɗin kayan ta, ta ɗakko mata zani da tshirt sai irin kallabin tsoffin nan.
Cikin jin daɗi Zulaikha tace"Yauwa ko kefa Inna, ki bari in canza kaya sai ayi duk gaishe gaishe".
Murmushi kawai inna tayi tana kallon ta, ita kuwa Zulaikha ta manta ma da akwai wani ciwo da tabo a jikin ta ta fara cire rigar ta.
Inna kuwa idon ta ƙur a akan Zulaikha, ganin tabbo da ƴan ciwuka a bayan ta, cikin sauri ta ƙaraso kusa da Zulaikha bata wani ɓata lokaci ba takai hannu jikin ta tana shafa wajen, ita kuwa Zulaikha da sauri ta juyo tana kallon inna don batayi tunanin tana kallon ta har haka ba ballantana takai da ganin tabbon dake bayan ta.
Da sauri ta matsa baya tana ƙarasa saka rigar ta haɗe da wayancewa tace"Inna ina wuni, na same ku lafiya? ".
Inna kuwa bata ce mata komai ba ta kamo hannun ta zuwa bakin gado zaunar da ita tayi sannan itama ta zauna tana riƙo hannun ta, damuwa fal akan fuskar ta.
Cikin tsantsar so da ƙauna haɗe da tausayin yarinyar tace" JUHAINA, kalle ni nan, ki gaya mun me ya faru dake kwana biyu bakya zuwa sannan kuma wainnan tabbon da ciwuka na jikin ki daga ina? Meye labarin su".
Cikin son kauda maganar Juhaina tace "Innnna, bafa wani abu bane, lefi akayi acikin gida shine aka haɗa bayi duka aka zane su, shine fa kawai innna babu wani abun damuwa".
Kallon rashin yarda da ita inna ta watsa mata sannan tace"Yaushe muka fara irin wannan wasan dake Juhaina? yaushe kika fara ɓoye mun lamuranki? Kada ki manta fa ni ƙanwar mahaifin ki ce, kuma tare muke son samun nasara, to akan me zakizo kina mun ɓoye ɓoye, idan har kin san baza ki iya ba to kiyi haƙuri ki barwa Allah komai kawai".
Inna kuwa cikin fushi ta tashi da niyyar barin ɗakin, cikin sauri da sanyin jiki Juhaina ta riƙo hannun ta, sannan tace"Inna don Allah kiyi haƙuri wallahi zan faɗa miki abunda ya faru, bana so ki shiga damuwa ne shiyasa tun farko ban gaya miki ba".
YOU ARE READING
JUHAINA
Historical FictionLabari ne akan wata yarinya da ta rasa iyayen ta a sanadiyyar wata masaurata, wanda daga baya ta gano maman masoyita da tun tana ƙarama itace sanadin komai. To ku biyo ni kuji yadda zata kaya a cikin wannan labari...