_*JUHAINA*_
_*Ummufatima*_
_*freepages 8*_
Haka kawai yasa shi rungume mace mtssss, macen ma Baiwa, Baiwar ma ƙaramar Baiwa, cikin jin haushi da ɗan kunya kunya ya tashi yana karkaɗe jikin shi, sannan ya juyo yana wani haɗe rai irin ba wasan nan, sauran mutane biyun da suka taho tare da su ne suka buɗe fuskar su suna ɗan sakin murmushi kafun suka zube a ƙasa kamar yadda Abdussamad ya rusuna, wani kalan murmushi AS(Abdussamad) yayi sannan ya tashi ya rungume AJ(Abduljalal) tsam tsam a jikin shi, yace"Haba yayan mu, haba yayan mu, fushi baya maka kyau".
Ko kula shi beyi ba ya ƙwace jikin shi ya wani gyara zamn rigar shi sannan yace "Sulaiman muje". Sulaiman kuwa kallon AS yayi ya ɗanyi murnushi sannan yabi bayan AJ suka wuce. AS kuwa kallon bashir da Ibrahim yayi yace"Mubi bayan shi kasan halin mutumin naku ya shaƙa wlh ".
Bashir ne yace" Ai saida nace maka kar muyi mai irin wannan wasan amman kaƙi ji"
Ibrahim kuwa tashi yayi ya karkaɗe jikin shi yace "Kai dalla rabu da shi daman ya fiya baƙar zuciya shi besan wasa ba, kuzo mubi bayan shi duk tsiya be isa ya kore mu ba".
Dariya dukkan su suka kwashe da shi, ita kuwa Zulaikha tana rakuɓe kamar wata munafuka har yanzun gabanta be dena dukan tara tara ba.
Ibrahim ne ya kalli inda take yace"Ke! Ke! ".
Dukkan su a tare suka juyo suka kalle ta, ita kuwa har ynzun ta kasa ɗago kanta ballantana ta kalle su.
Juyawa AS yayi" yace kunga tafiya ta, idan ta gama dawowa dai dai tasan hanyar zuwa gida ai ko".
Dukkan su ɗaga kafaɗa sukayi suka tafi suka barta a gurin.
Koda suka bi bayan AJ basu tarar da shi a hanya ba don yyi musu nisa sosai, suna isa ɓangaren nasu basu tsaya ɓata lokaci ba, suka shiga cikin ɗakin shi, inda suka hango shi a jikin taga ya naɗe hannu a ƙirji kamar irin jiran su yake yi ɗin nan.
Koda suka shigo juyowa yayi ya kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ya juya ya cigaba da kallon waje.
AS ne ya taho da Sauri yace "Haba yayan mu wlh kawai mun taho zamu shigo muka ga fitar ka shine nace mu dan wasa jini mana mun daɗe bamu motsa jiki ba, Allah ya huci ranka ya daɗe,Kuma naji yadda aka kawo maka hari nace bari na ɗan ƙara tsokanar ka".
Bashir ne yace"AS dan Allah share shi ba gashi mun wasa jini ba, kuma mun ƙara kawo maka hanyar ankarewa".
Kamar ko Jira yake ya juyo a fusace yace"Amman kunsan yadda kuka dizga ni a wajen wannan Baiwar shine abunda yafi ƙona mun rai, akan wani dalili zaku farmake ta?".
Ibrahim ne ya kwashe da dariya yace" Au ai munyi tunanin budurwar kace shiyasa muka gwada muga ko ka damu da ita".
Wani irin kallo ya watsa mai haɗe da cewa"Budurwa ta!? Buduwarta fa kace Ibrahim tabb". Ya juya yana taɓa haɓar shi haɗe da jinjina kai alamar abun mamaki.
Dariya Ibrahim yayi sannan yace"Aa bawai budurwar ka nake nufi ba, ina nufin muna so mu gwada muga zaka iya kare Bayin ka, sai kuma muka ga ashe zaka iya kana da zuciya mai kyau".Tsabar baƙin ciki ma kasa magana yayi sai juya musu baya da yayi yace"Madalla, ai yayi muku kyau, tunda kun ganni zaku iya tafiya yanzu ko, sannan kuma AS kace da Sulaiman ya faɗa ma Baiwar nan tazo ta taya Fulani haɗa kayan ta, ta koma ɓarayin Gimbiya, don ba me kwanar mun a ɗaki a cikin ku wallahi ".
Dukkan su dariya sukayi sannan suka fita daga cikin ɗakin, yadda ya faɗa musu haka suka sanar da Sulaiman su kuma suka nufi ɗakin AS da Fulani take ciki, yana shiga ya hango ta a gado tana kwance alamun bacci take yi, ga bayi guda biyu a gefan ta suna mata fifita a hankli, ganin shigowarsu yasa duk suka zube a ƙasa suna gaishe su.
YOU ARE READING
JUHAINA
Historical FictionLabari ne akan wata yarinya da ta rasa iyayen ta a sanadiyyar wata masaurata, wanda daga baya ta gano maman masoyita da tun tana ƙarama itace sanadin komai. To ku biyo ni kuji yadda zata kaya a cikin wannan labari...