*JUHAINA*
*page9*
*ummufatima*
AS kallon su Ibrahim ya tsaya yi ranshi a mugun bace wato sun maida shi mahaukaci besan me yaki yi ba,ko magana beyi musu ba ya tashi fuuuu ya fita daga cikin gurin be tsaya a ko INA ba sai a sashin su,ko da ya shiga cikin dakin be tsaya bata lokaci ba ya cire babbar rigar da ke jikin shi ya jefata kan gado .rike kugun shi yayi da hannu daya, dayan hannun kuma ya dago takardar yana sake karewa fuskarta kallo shi kanshi yasn Abu ne me wahalan gaske samun ta amma koma yaya ne zai gwada ya gani ,kuma idan ya same ta indai tana da asali koma wacece sai ya aure ta.haka dai ya dinga tunane2 daga baya ya Shiga bayi don ya kama ruwa.
JUHAINA kuwa da ta bar wajen AJ bata tsaya ko ina ba sai a sashin Fulani ,tana shiga ta hango su a wata barandar shan iska yayinda kanta ke kan cinyar Gimbiya babu ko dankwali a kanta saida JUHAINA ta matsa gab da su sannan ta gane ashe tsifa suke yi ,ko da ta is a bata wani tsaya bata lokaci ba ta rusuna kasa cikin sanyi murya tace"barka da rana ranki ya Dade".cikin sakin fuska gimbiya tace barka dai".kafun takai ga gaisar d Fulani tace"Uhmm sai yanzu ake ganin ku ko Zulaikha?"ta karashe maganar tana sakin murmushi.JUHAINA itama murmushin tayi mata sannan tace"Tuba nake ranki ya Dade naje sashin galadima ne".
Kada kai Fulani tayi tana gyara kanta akan cinyar gimbiya tace"keda yaya ko,ai kina cikin wani hali tunda kika mai wannan alkawarin".murmishi kawai juhaina tayi ta mike ta zagaya ta bayan su ta dau mifici tana musu fifita a hankali.suna cikin haka sai ga Hafsa ta shigo cikin barayin, ko da ta shigo idonta akan juhaina ya sauka hakan ne yasa ta balla mata harara tana Kara watsa mata wani kallon banzan.ita kuwa juhaina ta rasa me tayi mata duk inda suka hadu kallon banza da harara shi ke shiga tsakanin ta da hafsan.cikin zuciyarta tace"ke kika sani ina da abun yi bani da lokacin ki".hafsa kuwa cikin girmamawa ta gaisha da gimbiya tana sunnar da kai kasa daga gani akwai abunda tazo nema.Cikin wasa da dariya Fulani tace"matar yayan mu Muke gani a wannan lokacin."ta karashe mganr tana tashi zaune hade da gyara zaman gashin ta.
Hafsa kuwa dariya tayi tace"ohh kedai Allah ya shiryeki abun wasa baya miki wahala".
Fulani gyara zaman ta tayi tace"to ba gashi na saka ki dariya ba".dukkan su murmushi suka yi hafsa tace"ranki ya dade daman nazo muyi magana ne".ta karashe maganar tana sunkuyar da kanta kasa.
Gimbiya kuwa gyara zaman ta tayi tace"inajin ki hafsa me ya faru?".
Hafsa kuwa cikin yatsina fuska da daure fuska ta kalli juhaina tace"ke! zaki iya tafiya ki bamu guri kamar yadda kika gani muna bukatar sirri".
Juhaina kuwa gyada kai tayi cikin nutsuwa ta ajiye mufucin zata fita.Fulani ma saurin mikewa tayi ta dauki dankwalin ta ta daura tace"Zulaikha tsaya ki bani alkyabbata mu shiga ciki tare don nima nasan hardani a Koran nan".
Zulaikha kuwa ba ta bata lokaci ba ta temaka mata ta saka sannan suka wuce cikin.ita kuwa hafsa dama har cikin ranta bata so tayi maganar Fulani na wajen.
Ganin sun shige ciki hakan yasa gimbiya tace"Ina sauraren ki".
Sun kuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsun ta sannan tace"daman.. daman akan maganar baikon mu ne da galadima".
Wani murmushin manya gimbiya tace"oh ni bilkisu naga takai na,yarnan kiyi hakuri kinji ni shiru ko,dama so nayi sai Sakina ta dawo sai a shirya komai a tsanake to Amman tunda kinzo da maganar in sha Allah a satin nan za ayi baikon, ki kwantar da hankalin ki".
Murmushi hafsa tayi ta gyadama gimbiya kai tana jin kunya sosai.
Juhaina da Fulani koda suka shiga ciki waje suka nema suka zauna inda juhaina t a cigaba da yiwa Fulani tsifa suna ta hirar su gwanin ban sha'awa.
YOU ARE READING
JUHAINA
Historical FictionLabari ne akan wata yarinya da ta rasa iyayen ta a sanadiyyar wata masaurata, wanda daga baya ta gano maman masoyita da tun tana ƙarama itace sanadin komai. To ku biyo ni kuji yadda zata kaya a cikin wannan labari...