Bismillahir Rahmanir rahim.
Allah yasa yadda nafara lafiya yasa nagama lafiya, ya kuma sa karshen masoyan nan aure ne dan hasken kabarin Annabi.
22/09/2019
Kwance take tana chat a instagram sai kuma ta koma ganin pictures din mutane anan tayi karo da wani kyakkyawan saurayi sanye da wani milk colour captan murmushi ta sakar wa hoton sai kuma ta duba kanwar ta dake gefen ta, tace"Ilham kinga wani cute guy kuma wai yau birthday sa dariya sukayi sai kuma ta shiga comment section ta rubuta Happy birthday. Cikin ikon Allah yayi reply da thank u sis i really appreciate.Page dinsa ta shiga ta duba sauran pics din dake page din da duba hoton daya tace"Ilham ina ga wan nan ce budurwar sa sai kuma tayi murmushi ta fita daga page din iya abunda yafaru kenan a wan nan rana sai kuma ta manta dashi domin bata jima dayin breakup ba san nan tasamu tayi move on ba tare da wani tashin hankali ba domin koda yaushe tana rokan Allah kada ya jarrabata da soyayya to tsawan wan nan lokacin dai Allah ya kare ta daga duk wata damuwa da ta shafi soyayyah.
Daga yadda soyayyah tafara cin riba akanta.
18/11/2019
Tana chat da wata k'awar ta sai sukayi musu akan auren Mut'ah hakan yasa taje wani group din fiqhu dan yin tambaya sai kuma taji kunya, tunanin ta masa message private ne yazo aiko tayi saurin yin hakan cikin ikon Allah kuwa yayi reply san nan yace ta tuna masa anjima dan yanzu yana busy.
Tambayar sa tayi kamar yaushe zata tuna masa yace dare around 8 to 9 sukayi sallama akan sai zuwa daren.
8:30pm. Nayi ta sake sallama ta tuna masa ya kuma bata amsa san nan tace yayi hakuri saboda bazata iya tambaya a group ba yace ba komai zata iya tambayar sa koda nan gaba a private.
Bayan kwana biyu ta sake masa tambaya akan period wato jinin al'ada nan ma ya amsa daga nan suka fara hira kalmar da tafara kawo hirar itace Thank you Mr Malam.
Abun ya bashi dariya hakan yasa yace sai ta fada ta hausa daga haka conversation yafara chat sukayi sosai daga dare ya shiga sukayi ban kwana sai da safe.
After two days hirar su ta tsanan ta har tafi na da dan raba dare sukayi suna hira daga nan suka zama friends akayi excahnging suna kowa yayi saving number kowa.
Sunkai sati suna abota kowa yasan labarin dan uwansa tabashi labarin saurayinta shima ya bata na budurwar sa sai dai kuma dukan su biyu kowa yayi break-up cikin hikimar Allah
Nidai a ganina had'in ubangiji zaiyi wuyar rusa wa kuma believe dina ne Ummi and Jai will surely get married one day.
Ranar 23/11/2019
Ranar da dare Ummi and Jai suka fara soyayyah wanda hakan yasa ko bacci basu iya ba ranar dukan su biyu suna san kasan cewa da junan su.
Tun ranar da sukayi nuna wa juna suna son kasance wa tare dukan su biyun suke ba wa juna kula wa more especially jai.
Jai yana san ummi tamkar rayuwar sa ya dau duk wani son duniya ya daura mata, da duk mata zasu samu namiji kamar jai nidai ina ga da sun dace.
Jai da ummi suna wani irin rayuwa ne da ba abunda suke iya boye wa juna hatta assignment na islamiya tare sukeyi.
The most funny fact in their relationship is yadda ummi take damun sa daga zarar jai ya kwanta bacci zata tashe shi ga shagwabar tsiya kamar wata small baby shi kuwa hakan baya damun sa ko kadan sai ma irin yadda yake sake ta rairayar ta in har ba bacci take ba to fa shima bai isa ya kwanta ba babu ruwanta da dare ko rana ko da yaushe in dai idon ta biyu kawai shima ya zama haka, duk da cewa ba'a country daya suke ba baruwan ta har wani voice massage ya mata ranar birthday ta wanda a chan gaba zan sako muku shi.
Soyayyah da tausayin juna sai ummi da jai,
Hummm mu hadu a wani page dan jin yadda labarin zai sanja salo wan nan de kadan ne daga cikin yadda soyayyar su tafara
YOU ARE READING
So Sanadin Labarina
RomanceSo sanadin labarina, labarine akan mutane biyu da suke soyayya amma babancin su ba lallle yabarsu su rayu tare ba and issa true life story. amma addua ta Allah ya basu ikon rayuwa tare.