🤷♂️ *ADDININMU* 🤷♂️
( *By S REZA* ✍️)☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO* ...🌟
_I'M BACK 🥰 SO MUCH LOVE MY FAN'S 🙏_
*ADDININMU* .
*PAGE* 👉4️⃣______________Muryoyin al'umma ne kawai ketashi agurin ana bin wa'kar kamar sune suka rerata, ita kuwa Zainab sai kallon gurinda Abdalh yake takeyi tana son ganin wani irin yanayi zai shiga. Abdullha kuwa yana ji tasaki wannan wa'kar ya kalli abokin nasa cikin tsananin b'acin rai ya ce "Nagode da abun da kamin sannan kuma in harkana so na cigaba da zama anann to sai an kori wannan mawa'kiyar. Angon ya kalli Abdalh sannan ya ce "Haba Shek abdullha kasanfa banine na gaiyatotaba uwar amaryar ce, kuma tana gurinnan kaga kuwa banida ikon korarr ta.
Abdullha najin haka ya mi'ke tsaye ya bar gurin cikin tsananin jin haushin abokin nasa. Tin da yake ba'a ta'ba cimasa fuska irin wannan ba, wato saboda ta ganshi agurin shena tasa a ka sake Mata wannan wa'kar ko!!? Haka Abdalh ya dawo gida cikin tsananin jin haushi, dama mukullen mutar na hannun sa, sai kawai ya tafi yabar su. Duk abun dake faruwa a kan idon Zainab, dama tasan bazai zaunaba hakanne yasa tayi amfaninn da wannan damar ta kore shi. Bayan ta gama rera 'kasidar ne kuma ta koma wa'a zi a kan zaman aure tsakanin ango da amarya. Tana musu tini da irin zan auran Nana fad'ima Yar ma'aikin Allah .s a w. Yanda tayi ha'kuri agidan mijin ta, sannan tamusu tinida da, rayuwar manzan Allah da yayi da iyalan sa, haka dai Zainab ta dinga kawo musu abubuwa da manzan Allah yayiwa matansa.
Daga 'karshe ta rufe da salatul fati. Abokin ango da ango sai mamaki sukeyi ganinn yanda ta dinga fad'ar irin abubuwan da ma'aurata ya dace da suyi domin koyi da sunnonin Annabi Muhammad sallalahu a w s azaman aure. Haka mutane suka dinga mata ihisani harda ango da kansa saida ya mata, haka uwar amarya ta rasa inda zata sakata tsabar murna.
*A.J POV*
Da sallama ya shigo gidan baki har kunne, ba kowa a tsakar gidan hakanne yasa ya sake doka wata sallamar, dai-dai lokacin Nana ta fito daga wanka, ta amsa sannan ta tsaya da bokiti a hannu tana kallon ledodin da suke hannun sa, cikin mama ta ce "Yaya wannan kumafa daga Ina? "Kafin ya bata amsa Innah ta fito daga cikin d'aki tana cewa "lafiya kuw... "Lafiya lau Innah kawai taga abun da bata saba gani bane shine ta tsaya sai tayi surutun nata da tasaba.
D'akin Innah ya huce yabarsu tsaye suna kallon sa. Ya ce "Innah wallhi mugodewa Allah domin ni mai sa'a ne! Ya shiga fito da abubuwan da ya siyo , dai-dai lokacin Nana ta iso gurin bayan ta d'aura hijjabi a kan tahul d'in da tafito dashi daga wanka. Ganinn doguwar riga Amaya ne yasa ta d'auka tana cewa yayana amma wannan tawace ko?
A.J ya ce "Ai Nana daga yanzu mun fi 'karfin irin kayan da muke sawa a baya duk kyatar dasu zakiyi kifarasa na zamani. Cikin tsananin mamaki Innah ta ce "Yanzu Abdul jabaru bazakamin bayaninn yanda kasamu kud'ad'an nannba, har sai na tambayeka? Cikin farin ciki A.J ya ce "Innah amma ai tinkafin na tafi na miki bayani ko? Kuma kinsande A.J baya sata, saboda haka kawai kimanta da komai Allah ne ya dubemu.
Haka dai Innah tayi shiru domin kuwa tasan tinda yace to hakane, nann fa Innah ta shiga cin kaza ba kwa-kwatawa, haka suka kasance cikin farin ciki wannan ranar. Bayan komai ya kammala ne ya d'auki wayarsa yaga kiran Zarah, saida yaja tsaki sannan ya kirata yana cewa, yarinya yanzu kuma ai nahuce ajinki, nasan yanzuma zakicemin ba'a samu bane, kuma ke ya dama.
*LA'DIFA. SALIS. POV*
Da gudu ta fito daga cikin palorn gidan nasu tana mai kirin sunann mai gadin nasu tamkar ita ta rad'a masa. IRO!... IRO!... IRO!... Wanda shikuwa iro tin kiran farko ya taso daga sallamar sallha da yayi ya fito da gudu yana cewa "hajiya karama Dan Allah kiyi haguri wallhi yanzu na idar da sall... Cikin tsananin b'acin rai ta ce "Wai Kai wani irin wawane Kai baka da hankali ne? Shin saunawa zan cemaka karka sake barin wani ba'ko in dai magidanci ne ya shigo cikin gidannan? Cikin sabawa da irin abun da Lad'ifa ta kema dukda kuwa yakai ya haufeta, bata duba wannan domin kuwa wani lokaci ma harda mari ta had'a masa. Ya ce "Allah ya huci zuciyar ki wallhi saideko ina sallha ne ya hajiya Babba ta shigar dashi amma Dan Allah a gafarceni bazan sakeba in Sha Allah.
ESTÁS LEYENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AcciónThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3