Chptar 6

13 2 0
                                    

🤷 *ADDININMU*🤷

          ( *BY S REZA)*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*ADDININMU*
                   *PAGE* 👉6️⃣

............ A.J. Duk yanda yakai da son kud'i yaukan yaji ya tsorata da wannan kud'in, shi babban tashin hankalin sama shine... kar Daddy ya kama Sahra ita kuma tace shine yake turata. Haka ya shiga gida jiki babu 'kwari. Ko sallama baiyiba ya shiga gidan nasu yana tinanin mafita, Nana ce kad'ai a tsakiyar gidan tana cin abinci, hakanne yasa ta tsaya tana kallon yanayin yayan nata. "Yaya Lafiya kuwa kake?. Shikuwa A.J baima san tanayiba. Ganin bai bata amsa ta ce  "Yaya kiran sallar isha fa a keyi kuma naga kashigo gida? Cikin hanzari ya dawo daga tinanin na sa ya ce "Sorry na mantane yanzu zanje nayi. Tana kallosa ya bargidan da alama dai wani abun na damun sa.

*SALIS POV*

Kallon 'kanwar tasa ya keyi cikin soda ƙauna, tinda suke tare da ita basa ɓoyewa junann su komai domin kuwa ko saurayine yazo gurinta tofa saita sanar da shi haka shima, dukdade shi baitaɓa cewa yana sonwata yarinyar ba. Akaro na farko kenann yakejin bazai iya sanar da ita abun da ke ransaba, saninn halinta na kushe zaɓin wani.

Cikin zuciyar sa ya shiga tinann abun da yafaru yanzu minti kaɗan da suka huce. Tsaye yake a 'kofar gidan su AJ yana jiran yaga yaro ya aikeshi ya kira masa AJ, kasan cewar yakira wayar AJ ɗin bata shiga. Yana tsaye ya ga yaro yazo shiga gidan, nann take ya sanar da yaron cewar in ya shiga yace ana neman AJ.  Bayan kamar minti 2 yaron yazo ya ce wai bayanann amma ga ƙanwarsa wai zataga kowaye in yazo sai a faɗa masa. Salis ya ce "ok. Sannan ya kira yaron ya masa ihisani. Cikin gidan kuwa Innah ce ta ceda Nana taje ta dubo kowaye, domin kuwa sunsan A.J da abokai kuma duk yaran masu kuɗi.

Hakanne yasa ta saka hijab ta nufo ƙofar gidan. Leƙowa tayi ta hango baƙar mota a fake a ƙofar gidan, gakuma mutum a jingine a jikin motar, hakanne yasa ta nufi gurin sa. Tana zuwa tayi sallama haɗi da gaishisa. Salis da yake danna waya, ko kallonta baiyiba ya ce "Idan A.J yazo kice masa Salis ne yazo kuma kuce yasameni a gid... Maganar tasa ce ta maƙale a bakin sa sanadiyar tozali da fuskar Nana.

Cikin rikicea ya ce "am am am kikace baya gida ko? Nana ta ce " Eh baya gida amma yanzu zai dawo.

Ai take Salis yayi mutuwar tsaye jin wata sassaiyar muryarda tamasa magana da ita. Ya ce "To kice Salis ne yazo neman sa, Kuma kice yazo gida yanzu.

Nana ta ce "to zan fad'a masa, tana faɗa ta juya ta nufi gida cikin takunta na yan mata masu natsuwa. Salis kuwa neman fad'uwa ya keyi ganinn yanda take tafiya kamar zata karye, haka ya bar ƙofargidan cikin begen Nana.

Sauke ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga tinanin.

Laɗifa ta ce "bro lfy kuwa  tin ɗazu kazo Kanata tinani kuma kayi shiru?

Salis ya ce "sis ina maganar da hajiya Babba tamana ɗazu?

Laɗifa ta ce "Maganar aure ko maganar yaronnan abokin ka ɗan talakawannan?

Salis kuwa cikin ranshi ya ce "Allah ya sa ban faɗa mataba da wallhi bazata goyi bayana ba. Afili kuwa ya ce " maganar aure... Na yarda zanyi domin kuwa nasamu wacce na keso. Cikin mamaki Laɗifa ta ce "Yanzu-yanzu daga kaje gidansu A.J ka dawo kace min kasamu matar aure? Salis ya ce "Yes haka Allah yake abun sa. Laɗifa ta ce "Tofa!! Lallai koma wacece ta iya kamu, tabaɗa had'i da yin dariya sannan ta ce "ya sunann ta? Salis ya ce " ban saniba, bata faɗa min ba.

Laɗifa ta ce "To yanzu dai muje mu sanarwa da hajiya Babba, kaga itama saita dena maganar aurannan nata ko ya kace? Salis ya ce hakane tashi muje?. Haka suka jera suna tafiya Laɗifa na tsokanar sa, wai wata yarinyar tayi WUFF da shi a cikin lokaci kaɗan.

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang