Chptar 8

4 1 0
                                    

🤷 *ADDININMU* 🤷

       ( *BY S REZA ✍️)*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*ADDININMU*
                   *PAGE* 👉7️⃣

............... Kallon jakar kuɗin yakeyi yana aiyana abun da zai faru in ya mallake su. Cikin ransa yace "Anya kuwa in nabar wannan garaɓasar ban cutuba!?. Zuwa wani lokaci ya ɗago ya kalli Hajiya Babba sannan ya ce "Yanzu dan Allah hajiya meyasa kikeso ki aureni?. Hajiya Babba tayi dariya sannan ta ce "Banice zan aurekaba kaine zaka aureni...Kuma ba wai in ka aureni shikenan bazaka sakeyin wani auran bane, a'a zaka auri wacce kakeso, amma kafin nan zan baka labarin abin da yasa zanyi aure.

Cikin gamsuwa da abunda ya ce Nana ta ce "Ok tom barka da zuwa. Salis ya gyara tsayuwar sa sannamallak "Barkade...da fatan dai ba dole namikiba? Nana ta ce "kusan dai hakan...yanzu dai kafaɗi abunda ya kawoka tunda kace gurina kazo, kafin innah ta fito nemana?.  Cikin dariya Salis ya ce "Afito nemanki fa kikace kamar wata ƙaramar yarinya?.

"Eh dama ai ƙaramar yarinyar ce baka gani bane?. "Dan Allah karki ƙara kiran kanki da ƙaramar yarinya, kallekifa kin isa aure amma kice wai yarin ya ceke?. "Cikin jin kunya Nana ta rufe fuskarta haɗi da cewa... Please dan Allah zan tafi gida.? Salis yace "Muga wayar ki?. Ya mata wannan tambayar ne ganin wayar a hannuta. Ita kuwa Nana tinda a ka bata wannan wayar haryanzu bata barta ta hutaba.

Hajiya Babba ta ce "Nakasance tin ina yarinya Allah ya ɗoramin wani irin ciwo, wanda tin kafin na kai mizanin  aure a kamin. Na kasance  daga cikin mata harijai wato masu mutuƙar sha'awa. Hakanne yasa iyayena sukayi saurin aurarr dani, aurena uku (3) zan faɗa maka abun da yake rabani da mazajena. Har Allah yayi na auri mahaifin su Laɗifa, shima ɗin dan Allah yayishi jarimin gaske ne, shiyasa zamanmu yakai har lokacin da Allah ya amshi abinda.

Lokaci ɗaya AJ ya zaro ido waje jin abunda Hajiya ke faɗi. Ya ce "Hajiya menene harija? Hajiya tayi murmushi tana jin wani matsananci sha'awar yaron na ƙara taso mata a duk lokacin da yayi magana.

Zaro ido waje Nana tayi ta ce "Mezakayi da wayana? Salis ya ce "kinga rufe bakin kar..."ai kafin ya ƙarasa ta rufe fuskarta tsabar kunya. Haka ta ciro wayar ta bashi, domin kuwa babu fuskar masa musu, domin kuwa ya mata kwarjini sosai. Bayan ta bashi sannan ta zuba masa ido domin ganin mai zaiyi da ita. Hoton ta da AJ ne a gaban wayar. ganinn yanda sukayi kyau ne yasa ya ce "Kunyi kyau sosai kamar ba keba ya ci gaba da cewa "Badan AJ ya girmekiba da sai ace ko ɗin ƴan biyu ne. Dariya tayi tana jin daɗin yanda ya yabesu.

Number sa ya saka mata sannan ya ƙwada kira ko tanada kuɗi, aikuwa sai gashi ta shiga, yayi seveng number sa da (my sweetheart) sannan ya nuna mata. Haɗi da cewa wannan number nane zamu dinga gaisawa.

Hajiya Babba ta ce "Karka damu duk zan sanar dakai. Taci gaba da bashi labari. Yanzu haka shekarar Alhaji huɗu da rasuwa, kuma tun baya ya rasu yarana suka hanani yin wani auran, kuma sunsan da cewar addinmu bai hanaba amma duk wanda yazo sai sun korheshi. Jiyama sun koriwani, shine yasa nayi amfani da kai domin cimma wani burina, inaso ka yarda babu abun da zai faru, domin kuwa ADDINIMU bai haramta ba.

Zamuyi aure na shekara ɗaya, Sannan zan baka miliyoyin hamsin da gida harda mota... sannan babu abun da zai shiga tsakanina da kai har muyi wannan shekara ɗaya ɗin, abin da nakeso shine Karka sanarwa da kowa, harda kakarku domin kuwa nasamo labarin ka gaba ɗaya, iyayenku sun rasu, daga kai sai ƙanwarka sai kakarku, to banaso susan da labarin, da so  samunema wata ƙasar samu tafi mufara yin wats ɗaya kafin mudawo, kokuma kawai zan cewa su Salis na ɗaukeka a matsayin yaron gidana, zaka dinga zuwar min aike da cefane. Kaga kassmu damar shiga ɗakina duk lokacin da na kiraka koda kuwa kana inane?.

Nana bata tsaya karanta abun da yayi seveng number ba, domin ita duk a tinanin ta kawai yasa number ne bai ajiye taba. Hakan  ne yasa ta karɓa tana cewa "Tom zan shiga gida? "To sai kinga kirana. Batace komaiba ta shige gida, shikuma ya tsaya yana Kallon ta har ta shiga gidan. Sannan shima yayi murmushi ya huce gida. Yana hanya yana tinanin hirarr da sukayi.

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMWhere stories live. Discover now